Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 27 ga watan Mayun 2026
Taƙaitattu
- Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
- Majalisar Iran ta fara zamanta na farko tun bayan fara yaƙi
- Yau ake fara aikin Hajjin shekarar 2026
- Farashin mai ya faɗi saboda fatan cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka
- An kashe sojan Isra'ila a Kudancin Lebanon
- Yadda ake tababa kan zaɓen fitar da gwani na Tinubu
- Kasashe 7 da suka fi ƙanƙanta a duniya
- Wane ne Sadiqu, jakadan Shekau da ake zargi da sace ɗalibai a Oyo?
- Iran ta tabbatar da kisan Ali Khamenei a hare-haren Amurka da Isra'ila
- Yadda Amurka da Isra'ila suka kwashe watanni suna kitsa kashe Ayatollah Khamenei
- Matakan da ake bi wajen zaɓen sabon Jagoran Addinin Iran
- Me ƙasashen Afirka suka ce kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila?
- Me ya sa Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran hari, kuma yaushe yaƙin zai ƙare?
Rahoto kai-tsaye
Nabeela Mukhtar Uba da Haruna Ibrahim Kakangi
Narendra Modi ya nemi Indiyawa su kare kansu daga matsanancin zafi
Firaiministan Indiya Narendra Modi ya yi kira ga al'ummar ƙasar da su ɗauki matakai domin kare kansu daga matsanancin zafin da ake fama da shi a sassan ƙasar, lamarin da ke janyo afkuwar wutar daji.
Birane 40 da suka fi fama da zafi a duniya suna Indiya - inda yanayin ke kai wa fiye da maki 43 a ma'aunin salshiyos.
An shawarci mutane da ke zaune a Delhi, babban birnin ƙasar da su zauna a gidajensu.
An kuma rufe makarantu saboda tsananin yanayin na zafi.
Can kuma a Himalayas, sojojin Indiya suna ta ƙoƙarin kashe gagarumar gobarar daji.
Falasɗinawa sun yi idi a tsakiyar ɓuraguzon yaƙi
Me ya sa mutane ke rububin taɓa dutsen Hajaral-Aswad?
A duk lokacin da Musulmai ke ibadar ɗawafi a ɗakin Ka'aba, akan gan su suna ta tururuwa a wuri guda a ƙoƙarin taɓa wani baƙin dutse da ke jikin ɗakin Ka'abar.
Dawafi na nufin zagaye Ka'aba har sau bakwai, kuma a wannan lokaci ne yawancin zukatan masu ɗawafin ke karkata zuwa kusurwar da ke ɗauke da baƙin dutsen na Hajar al-Aswad.
A nan ne ake ganin tururuwar mutane, wasu na ture wasu cikin turmutsisti duk a yunƙurin taɓa ko sumbatar dutsen, duk da cunkoson jama'a da ke kewaye da shi.
Wannan yanayi kan haifar da tambayoyi ga masu kallo.
Shin wajibi ne musulmi ya taɓa wannan dutse a lokacin ibadar, ko kuwa akwai wata ma'ana ta daban da ke bayan wannan aiki?
Domin samun ƙarin haske kan wannan batu, BBC ta tuntuɓi wani malami a Abuja, Ustadh Aminu Zubairu, wanda ya bayyana cewa mutane suna rububin taɓa Hajar al-Aswad ne saboda matsayinsa a tarihin Musulunci da kuma abin da ake dangantawa da shi na falala da lada.
A cewar malamin ya zo a cikin hadisi, Annabi Muhammad (SAW) ya taɓa wannan dutse, kuma Musulmai suna bin wannan misali ne domin neman lada da ɗaukaka da falala da ake kyautata zaton yana da shi da kuma daga asalin inda ya Dusten ya taho.
Ga cikakken bayanin a nan.
Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Boko Haram a dajin Sambisa
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta zafafa hare-hare ta sama da take kai wa kan mayaƙan Boko Haram a jihar Borno inda a baya-bayan nan ta kai hare-hare kan cibiyoyin masu tayar da ƙayar baya a dajin Sambisa lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu.
Samamen wanda aka kai shi ƙarƙashin rundunar Hadin Kai, ya shafi wuraren da ƴan ta'adda ke ɓoyewa da kuma inda suke ajiye makamansu a Biramiri da ke jihar.
Kakanin rudunar sojin saman ta Najeriya, Ehimen Ejodame ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar.
Sanarwar ta ce sojoji sun kai hare-haren ne ranar 26 ga watan Mayu bayan samun wasu sahihan bayanan sirri kan maɓoyar mayaƙan.
Manufofin gwamnati sun fara daidaita tattalin arzikin Najeriya - Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ƴan ƙasar tabbaci cewa sannu a hankali lamura suna yin sauƙi ta fuskar tattalin arziki.
Ya bayyana haka ne a saƙonsa na barka da sallah da ya yi wa al'ummar ƙasar.
A cewar shi, manufofin gwamnatinsa sun fara daidaita tattalin arziki tare da jawo hankalin masu zuba jari.
Shugaban ya kuma bai wa al'umomin da matsalar ta'addanci ta yi wa katutu cewa gwamnatinsa ba ta yada su ba.
Ya yi alƙawari gwamnatinsa za ta murƙushe duk masu yi wa ƙasar barazana.
A saƙon, Tinubu ya ce sadaukarwar da ƴan Najeriya suka yi cikin shekaru uku da suka gabata sun fara kawo nasrarori, inda kuma ya ce a yanzu ƙasar tana samun masu son zuba jari da zai iya samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Yadda aka yi idi a masallacin Annabi da ke Madina
An kwashe rukunin farko na ƴan Ghana daga Afirka ta Kudu
Wani jirgi ɗauke da ƴan Ghana kusan 300 ya bar Afirka ta Kudu.
Suna cikin ƴan Ghana kusan 800 da suka nuna sha'awar komawa gida saboda tsanantar zanga-zangar ƙyamar baƙin haure a birane da dama na ƙasar.
Jakadan Ghana a Afirka ta Kudu ya shaida wa BBC cewa gwamnatinsu tana da nauyi na kare lafiyar al'ummarta.
Ƙasashe na taƙaita tafiye-tafiye kan ɓarkewar Ebola
Ƙasashe da dama na sanar da taƙaita tafiye-tafiye saboda fargabar da suke da ita akan yadda da cutar Ebola ke yaɗuwa.
Canada ta haramtawa 'yan Uganda da Sudan ta Kudu shiga ƙasar har zuwa nan da watanni uku.
Sauran yankunan da cutar ta fara ɓulla kuma 'yan ƙasar idan sun shiga Canadan sai sun keɓe kansu na tsawon makonni uku.
Ita ma Bahamas ta fitar da makamanciyar sanarwar Canadan.
Thailand kuma ta sanya dokar keɓe duk waɗanda suka shiga ƙasar daga yankin tsakiyar Afirka.
A makon da ya gabata ne Amurka ta haramtawa 'yan ƙasarta zuwa ƙasashen da cutar ta Ebola ta ɓulla yayin da 'yan ƙasashen kuma suma aka haramta musu tafiya zuwa Amurkan.
Rahotanni sun ce an keɓe wata mata daga Uganda da ta shiga Indiya a Bengaluru inda kuma aka same ta da cutar bayan gwajin da aka yi mata sakamakon rashin lafiyar da ta soma.
Yadda aka yi sallar Idi a Abuja da Kano
Al'ummar Musulmi sun halarci sallar idi a masallatai da dama da ke faɗin duniya.
A Abuja, babban birnin Najeriya, wakilin BBC ya shaida yadda aka yi sallar idi a Masallacin idi na Unguwar Katampe inda manya maza da mata har ma da ƙananan yara suka halarta.
Kazalika a jihar Kano, gwamna Abba Kabir da mataimakinsa, Murtala Sule Garo sun yi idi a masallacin Ƙofar Mata inda Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar.
Gwamnan ya halarci sallar tare da wasu muƙarraban gwamnatinsa.
Ghana ta fara shirin kwashe ƴan ƙasarta kusan 800 daga Afirka ta Kudu
Jami'ai daga Ghana za su kwashe kusan 'yan ƙasar 800 zuwa gida daga Afirka ta Kudu.
Hakan ya biyo bayan zanga zangar nuna ƙyama ga baƙin hauren da ake a wasu sassan biranen Afirka ta Kudu fiye da wata guda ke nan.
Wakiliyar BBC ta ce ta ga yadda gwamman mutane ke fita daga motocin bas inda suka isa filin jirgin saman Tambo suna hawa jirgin zuwa Accra.
Jakadan Ghana a Afirka ta Kudu ya ce gwamnatinsu na son tabbatar da cewa 'yan Ƙasarsu sun kuƁuta daga hare-haren da ake kai wa baƘin hauren.
Ghana ta ce tana tabbatar da tsare lafiyar 'yan Ƙasarta.
Waɗanda suke zanga zangar sun ce yawancin mutanen da ke shiga cikin Ƙasar ta Afirka ta Kudu ba bisa Ƙa'ida ba na mamaye musu guraben aiki a ma'aikatun gwamnati.
Isra'ila ta yi iƙirarin kashe sabon kwamandan Hamas
Isra'ila ta ce ta kashe wani Shugaban ɓangaren mayaƙan Hamas, Mohammed Odeh a wani hari da ta kai Gaza ranar Talata - kwanaki bayan mutuwar magabacinsa a wani hari makamancin wannan.
Aƙalla Falasɗinawa uku aka kashe sannan gommai sun ji rauni a gagarumin harin na ranar Talata wanda ya faɗa kan wani gida a ɗaya daga cikin manyan kasuwannin birnin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Sojojin Isra'ila sun ce an kai hari kan gine-ginen da ke zama maɓoyar Odeh bayan da aka bibiye shi tsawon watanni.
Zuwa yanzu Hamas ba ta ce komai ba kan lamarin.
Shi ne hari mafi muni da Isra'ila ta kai kan Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da Hamas wadda ta fara aiki a Oktoba.
Musulmi na bikin babbar sallah a faɗin duniya
Al'ummar Musulmai a faɗin duniya na bikin idin Babbar Sallah, bayan hawan Arafah jiya Talata a Ƙasa Mai Tsarki.
Ranar na cikin manyan ranakun bikin Musulunci biyu a shekara.
Biki ne da akan yanka rago ko sa inda wasu ke bayar da naman sadaka ga mabuƙata.
Musulmi na yin amfani da muhimmin lokacin wajen sada zumunci a tsakanin ƴan'uwa da abokan arziki.
A bana ranar ta zo daidai da ranar yara ta duniya da ake yi duk 27 ga watan Mayu.
Kazalika, sallar ta zo yayin da ake ci gaba da yin yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.
Barka da Sallah
Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na marhaba da ɗumbin masu bibiyar mu a wannan rana da Musulmi a faɗin duniya ke bikin sallah babba.
Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.
Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.
Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo har ma ku tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.