Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Sadiqu, jakadan Shekau da ake zargi da sace ɗalibai a Oyo?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta ce ƙungiyar Boko Haram ce ta kai hari a makarantar da aka kashe malami tare da sace ɗalibai da wasu malamansu cikin makon jiya a jihar Oyo, da ke kudu maso yammacin ƙasar.
An sace gomman ƙananan yara a harin da ba a saba gani ba a jihohin kudancin Najeriya. Tuni dangin malamin da aka kashe Mista Adesiyan Adebgoye suka yi masa jana'iza.
Cikin wata sanarwa da kakakin sojin Najeriyar Manjo Janar Michael Onoja ya fitar, ya ce sace-sacen da aka yi a baya-bayan nan, ayyukan ta'addanci ne da mayaƙan ƙungiyar suka ƙaddamar bayan da matsin lambar farmakin soji ya tilasta musu tserewa daga wasu sassan ƙasar.
Masana tsaro na ganin cewa sabon bayanan da sojoji suka fitar, na nuna ƙarin damuwa cewa mayaƙan da farmakin sojoji ya fatattaka a arewa maso gabashin Najeriya, na iya fantsama zuwa wasu sassan ƙasar.
Barista Audu Bulama Bukarti, mai sharhi ne kan tsaro a nahiyar Afrika, ya yi wa BBC ƙarin bayani kan mutumin da ake kyautata zaton shi ne zai iya ƙaddamar da irin wannan hari.
Wane ne Sadiqu?
Barista Bukarti ya ce tun da har rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa Boko Haram ce ta kai harin, to babu wanda ake hasashen zai kai harin da ya wuce wani jakadan tsohon shugaban ƙungiyar da aka kashe Abubakar Shekau.
Ya ce mutumin da ake kira da Sadiqu, ɗaya ne daga cikin mutane bakwai da Shekau ya tura daga yankin arewa maso gabas zuwa arewa ta tsakiya a shekarar 2014 domin su nemi haɗin kan ƴan ƙungiyar Darul Islam, waɗanda aka taɓa fatattaka daga Mokwa a jihar Neja a shekara ta 2009.
Asalinshi mutumin jihar Borno ne, inda yake jagorantar tsagin ƙungiyar ta Boko Haram da ke wannan yanki.
Ya ce mafi yawan ƴan ƙungiyar Darul Islam ba su shiga ƙungiyar ta Sadiqu ba, "amma wasu sun shiga", inda ya rika kai kawo har sai da ya samu ya kafa sansanin ƙungiyar Boko Haram a jihar Neja.
Barista Bukarti ya ƙara da cewa Sadiqu ya samu damar kafa sansaninsa ne a dajin Alawa, inda daga baya ya koma dajin Kainji da ke da hanya har zuwa gandun dajin tsohuwar jihar Oyo.
"To ka ga daga nan Kainji, Sadiqu [da mayaƙansa] za su iya shiga har zuwa jihar Oyo su aikata wannan aika-aika," in ji shi.
Bukarti ya ƙara da cewa Sadiqu ne ya kai harin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a 2022, da ma wasu hare-haren da aka ƙaddamar, inda ya ke tura yaransa zuwa jihohi daban-daban domin kafa sansani.
Abin da gwamnatin Najeriya ta ce
Tuni shugaban ƙasar Bola Tinubu ya umurci jami'an tsaro su gaggauta kuɓutar da ɗalibai da malaman, inda ya yi Allah wadai da harin, kamar yadda kakakinsa Bayo Onanuga ya bayyana a cikin wata sanarwa.
Shi ma gwamnan jihar ta Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa malamai bakwai da dalibai ciki har da yara ƙanana masu shekaru biyu zuwa uku aka sace.
Yanzu haka ɗaliban sun shafe sama da mako guda a hannun masu garkuwar.
Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 8:00 zuwa 9:00 na safiya a makarantar Community High School da ke Ahoro-Esinele inda aka tafi da shugabar makarantar Rachael Alamu.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ayanlade Olayinka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.
"Rahoton da muka samu ya nuna cewa ƴan bindigar sun tsere da shugaban makarantar a cikin motarta zuwa wani daji da ke iyaka da yankin," in ji shi.
Wasu rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne a makarantu uku da ke garuruwan Esinele, Yamota da Alawusa a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo, kuma aƙalla mutum 46 ke hannunsu.
Yadda lamarin ya faru
A ranar Juma'a 15 ga watan Mayu, 2025 ƴan bindigar suka kai hari makarantar yara ta Baptist da ke Yawota da Community Grammar da ke Esiele sai kuma firamaren gwamnati ta LA Ogbomoso, duk a ƙaramar hukumar Oriire.
Kwamishinan ƴansandan jihar ta Oyo ya tabbatar da kisan mutane biyu da ƴan bindigar suka yi a harin, sannan ya ce akwai malamai da ɗalibai kimanin 45 da aka yi garkuwa da su.
Hukumar kula da harkokin ƙananan makarantu sun bayar da umarnin rufe makarantun da ke kusa da garuruwan da aka sace nasu ɗaliban, har sai abin da hali ya yi.
Hukumar ta ce an yi hakan ne a matsayin wani mataki na wucin-gadi, domin gudun a sake sace wasu, domin tabbatar da kwanciyar hankali.
A sanarwar da suka fitar, sun bayyana lamarin a matsayin mai tayar da hankali ga jihar ta Oyo, inda suka bayyana cewa sun damu matuƙa tare da tausayawa ga iyayen yaran da al'ummomin gaba ɗaya.
Amma kuma daga bisani hukumomin jihar sun bayar da umarnin a ci gaba da karatu a makarantun ranar Litinin, bayan da aka kai ƙarin jami'an tsaro yankin.
Harin na zuwa ƙasa da sa'oi 24 da mahara suka kai makamancinsa a ƙaramar hukumar Askira-Uba da ke jihar Borno, inda suka sace yara sama da 40.
Lamarin hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don neman kuɗin fansa sun fi ƙamari ne a yankin arewacin Najeriya, inda ba kasafai aka saba ganin hakan ba a kudancin ƙasar, wadda ke fama da matsaloli na tsaro.
A baya-bayan nan ita ma dai jihar ta Oyo na fuskantar matsalar tsaron daga gungun masu aikata laifi.