KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 27 ga watan Mayun 2026

  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Haruna Ibrahim Kakangi

  1. 'Rasha ta rasa sojoji kusan rabin miliyan a yaƙin Ukraine'

    Vladimir Putin

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar leƙen asiri mafi girma a Birtaniya ta ce ƙasar Rasha ta yi asarar sojoji kusan rabin miliyan tun bayan yaƙin da ta ƙaddamar a Ukraine cikin shekarar 2022.

    Shugabar hukumar tattara bayanan sirrin intanet da tsaro ta Birtaniya (GCHQ), Anne Keast-Buttler ce ta bayyana haka a jawabin da ta gabatar.

    Ta yi gargadin cewa Rasha na aiki "ba-dare-ba-rana" wajen kai harin intanet kan muhimman ɓangarori da kuma kan dimokuraɗiyyar Birtaniya da ƙasashen yankin Turai.

    Ta ce hukumar GCHQ na aiki tuƙuru wajen daƙile hare-haren da Rasha ke kaiwa ta intanet wanda ta bayyana a matsayin "yunƙurin zagon ƙasa da kisa na ba-gaira babu dalili".

    Haka nan Ms Keast-Butler ta bayyana cewa a halin yanzu Rasha na da matuƙar ƙwarewa a fannin tattara bayanan sirri ta kowane fanni, kamar ta intanet da harkar soji, tare da cewa dama ƙalilan ne kawai ta rage wa Birtaniya da ƙawayenta wajen shawo kan hakan.

  2. 'Iran ta karɓi sabon daftarin yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi'

    Mojtaba Khamenei

    Asalin hoton, Tasnim

    Bayanan hoto, Mojtaba Khamenei

    Kafar talabijin ta ƙasar Iran ta ce gwamnatin ƙasar ta karɓi daftarin farko-farko na yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi tsakanin ƙasashen biyu.

    Kafar yaɗa labaran ta gwamnati ta ce yarjejeniyar ta ƙunshi cewa Iran za ta buɗe mashigar Hormuz ga jiragen ruwa domin su ci gaba da sufuri kamar yadda yake kafin fara yaƙi, a cikin wata ɗaya.

    A ɓangaren Amurka kuma, za ta janye duk wasu dakarunta daga kusa da Iran tare da daina toshewar da ta yi wa tashoshin jiragen ruwa na Iran.

    Haka nan yarjejeniyar ta ƙunshi cewa Iran da Oman za su zamo ƙasashen da za su riƙa lura da sufurin jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz.

    Fadar shugaban Amurka ta bayyana yarjejeniyar da kafar talabijin ɗin ta fitar a matsayin "zallar tatsuniya".

    Daftarin ya samo asali ne daga tattaunawar da Pakistan ke yi domin shiga tsakanin ƙasashen biyu.

  3. Ya kamata duk wanda ya yi layya ya raba nama - Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Asalin hoton, Gwamnatin Jihar Sokoto

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya buƙaci al'ummar jihar da suka samu damar yin layya su raba nama ga mutanen da ba su samu damar yin layyar ba kamar yadda Musulunci ya tanada.

    Gwamnan ya yi wannan bayani ne a saƙonsa na ranar Idi a yau Laraba.

    Ya ce yin hakan zai kawo "sauƙi ga mutane masu rauni baya ga samun lada daga Allah."

    Ya ƙara da cewa Musulunci ya riga ya yi bayani kan yadda ake raba naman layya, saboda haka ya kamata al'umma su bi ƙa'idar.

    A cewar sa gwamnatin jihar na kashe maƙudan kuɗaɗe a kowace shekara wajen tallafa wa malaman addini da mabuƙata da ƴan gudun hijira waɗanda rashin tsaro ya tarwatsa da kuma marasa ƙarfi.

    Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin da rikicin ƴan bindiga ya tarwatsa mutane da dama, wadanda suka bar muhallansu.

    A yau Laraba ne Musulmai a Najeriya da ma wasu ƙasashen duniya suka yi bikin sallar Idin layya, inda Musulunci ya buƙaci masu hali su yi yanka domin yin koyi da annabi Ibrahim.

    Hotunan yadda aka yi sallar Idi a Sokoto:

    xxx

    Asalin hoton, Gwamnatin jihar Sokoto

    xxx

    Asalin hoton, Gwamnatin jihar Sokoto

    xxx

    Asalin hoton, Gwamnatin jihar Sokoto

  4. Farashin mai ya yi ƙasa bayan rahoton ci gaba a yarjejeniyar yaƙin Iran

    Farashin mai ya yi ƙasa sakamakon rahotannin ci gaba da aka samu a tattaunawar cimma yarjejeniyar dakatar da yaƙi tsakanin Amurka da Iran.

    Gidan Talabijin na ƙasar ya ce Iran ta samu daftarin yarjejeniyar fahimtar.

    A ƙarƙashin tsarin, Iran za ta dawo da zirga-zirgar jirage a Mashigar Hormuz yayin da ita kuma Amurka za ta janye sojojinta.

    An samar da daftarin sakamakon tattauna inda Pakistan ta zama mai shiga tsakani tsakanin Tehran da Washington.

  5. Saƙon Barka da Sallah a harsunan Afirka

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon
  6. Yaƙi a Congo na tarnaƙi ga ayyukan daƙile Ebola - WHO

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Yaƙin da ake yaƙi a Jamhuriyar Dimokraiyyar Congo na tarnaƙi ga ƙoƙarin da ake na yaƙi da ɓarkewar cutar Ebola, kamar yadda shugaban Hukumar Lafiya WHO ya yi gargaɗi.

    Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce gabashin ƙasar shi ne cibiyar cutar Ebola da yaƙi inda kuma ɓarkewar cutar a Lardin Ituri ke neman gagarar ƙoƙarin ma'aikatan lafiya.

    Cikin wata sanarwa a shafin X, Tedros ya ce WHO ba za ta keɓe marasa lafiya a yanayin da ake ciki na yaƙi ba.

    A wannan makon ne ake sa ran Ghebreyesus zai isa Congo domin jan ragamar ƙoƙarin da ake na daƙile bazuwar cutar.

    An samu mutum 220 da ake zargi sun mutu sakamakon cutar tun bayan da aka ayyana ɓarkewar cutar a ƙasar.

  7. Hotunan Shugaba Tinubu yayin idi a Legas

    ..

    Asalin hoton, @drobafemihamzat/X

    Bayanan hoto, Shugaba Bola Tinubu ya bi sahun sauran al'ummar Musulmi don idin babbar sallah a jihar Legas
    ..

    Asalin hoton, @drobafemihamzat/X

    Bayanan hoto, Daga cikin jami'an da ke tare da shugaban ƙasar akwai ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila da mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.
    ...

    Asalin hoton, @drobafemihamzat/X

    Bayanan hoto, Sauran sun haɗa da mataimakin gwamnan jihar Legas Obafemi Hamzat da tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola
    ..

    Asalin hoton, @drobafemihamzat/X

  8. Narendra Modi ya nemi Indiyawa su kare kansu daga matsanancin zafi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Indiya Narendra Modi ya yi kira ga al'ummar ƙasar da su ɗauki matakai domin kare kansu daga matsanancin zafin da ake fama da shi a sassan ƙasar, lamarin da ke janyo afkuwar wutar daji.

    Birane 40 da suka fi fama da zafi a duniya suna Indiya - inda yanayin ke kai wa fiye da maki 43 a ma'aunin salshiyos.

    An shawarci mutane da ke zaune a Delhi, babban birnin ƙasar da su zauna a gidajensu.

    An kuma rufe makarantu saboda tsananin yanayin na zafi.

    Can kuma a Himalayas, sojojin Indiya suna ta ƙoƙarin kashe gagarumar gobarar daji.

  9. Falasɗinawa sun yi idi a tsakiyar ɓuraguzon yaƙi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Falasɗinawa sun taru a wata hanya da yaƙi ya yi wa kaca-kaca domin yin idi.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Sun yi idin ne a Khan Yunis da ke Kudancin Gaza.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Tun bayan cimma yarjejeniya, an ga tsagaitawar yaƙi tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas sai dai ɓangarorin biyu na zargin junansu da saɓa ƙa'idojin yarjejeniyar.
    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Bayan idar da idi ne kuma wasu Falasɗinawa suka ziyarci kaburburan makusantansu da suka mutu.
  10. Me ya sa mutane ke rububin taɓa dutsen Hajaral-Aswad?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A duk lokacin da Musulmai ke ibadar ɗawafi a ɗakin Ka'aba, akan gan su suna ta tururuwa a wuri guda a ƙoƙarin taɓa wani baƙin dutse da ke jikin ɗakin Ka'abar.

    Dawafi na nufin zagaye Ka'aba har sau bakwai, kuma a wannan lokaci ne yawancin zukatan masu ɗawafin ke karkata zuwa kusurwar da ke ɗauke da baƙin dutsen na Hajar al-Aswad.

    A nan ne ake ganin tururuwar mutane, wasu na ture wasu cikin turmutsisti duk a yunƙurin taɓa ko sumbatar dutsen, duk da cunkoson jama'a da ke kewaye da shi.

    Wannan yanayi kan haifar da tambayoyi ga masu kallo.

    Shin wajibi ne musulmi ya taɓa wannan dutse a lokacin ibadar, ko kuwa akwai wata ma'ana ta daban da ke bayan wannan aiki?

    Domin samun ƙarin haske kan wannan batu, BBC ta tuntuɓi wani malami a Abuja, Ustadh Aminu Zubairu, wanda ya bayyana cewa mutane suna rububin taɓa Hajar al-Aswad ne saboda matsayinsa a tarihin Musulunci da kuma abin da ake dangantawa da shi na falala da lada.

    A cewar malamin ya zo a cikin hadisi, Annabi Muhammad (SAW) ya taɓa wannan dutse, kuma Musulmai suna bin wannan misali ne domin neman lada da ɗaukaka da falala da ake kyautata zaton yana da shi da kuma daga asalin inda ya Dusten ya taho.

    Ga cikakken bayanin a nan.

  11. Sojoji sun tarwatsa maɓoyar Boko Haram a dajin Sambisa

    ...

    Rundunar sojin sama ta Najeriya ta zafafa hare-hare ta sama da take kai wa kan mayaƙan Boko Haram a jihar Borno inda a baya-bayan nan ta kai hare-hare kan cibiyoyin masu tayar da ƙayar baya a dajin Sambisa lamarin da ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu.

    Samamen wanda aka kai shi ƙarƙashin rundunar Hadin Kai, ya shafi wuraren da ƴan ta'adda ke ɓoyewa da kuma inda suke ajiye makamansu a Biramiri da ke jihar.

    Kakanin rudunar sojin saman ta Najeriya, Ehimen Ejodame ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar.

    Sanarwar ta ce sojoji sun kai hare-haren ne ranar 26 ga watan Mayu bayan samun wasu sahihan bayanan sirri kan maɓoyar mayaƙan.

  12. Manufofin gwamnati sun fara daidaita tattalin arzikin Najeriya - Tinubu

    Tinubu

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ƴan ƙasar tabbaci cewa sannu a hankali lamura suna yin sauƙi ta fuskar tattalin arziki.

    Ya bayyana haka ne a saƙonsa na barka da sallah da ya yi wa al'ummar ƙasar.

    A cewar shi, manufofin gwamnatinsa sun fara daidaita tattalin arziki tare da jawo hankalin masu zuba jari.

    Shugaban ya kuma bai wa al'umomin da matsalar ta'addanci ta yi wa katutu cewa gwamnatinsa ba ta yada su ba.

    Ya yi alƙawari gwamnatinsa za ta murƙushe duk masu yi wa ƙasar barazana.

    A saƙon, Tinubu ya ce sadaukarwar da ƴan Najeriya suka yi cikin shekaru uku da suka gabata sun fara kawo nasrarori, inda kuma ya ce a yanzu ƙasar tana samun masu son zuba jari da zai iya samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

  13. Yadda aka yi idi a masallacin Annabi da ke Madina

    ..

    Asalin hoton, Inside the Haramain/FB

    ..

    Asalin hoton, Inside the Haramain/FB

    ..

    Asalin hoton, Inside the Haramain/FB

    ..

    Asalin hoton, Inside the Haramain/FB

  14. An kwashe rukunin farko na ƴan Ghana daga Afirka ta Kudu

    ..

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Wani jirgi ɗauke da ƴan Ghana kusan 300 ya bar Afirka ta Kudu.

    Suna cikin ƴan Ghana kusan 800 da suka nuna sha'awar komawa gida saboda tsanantar zanga-zangar ƙyamar baƙin haure a birane da dama na ƙasar.

    Jakadan Ghana a Afirka ta Kudu ya shaida wa BBC cewa gwamnatinsu tana da nauyi na kare lafiyar al'ummarta.

  15. Ƙasashe na taƙaita tafiye-tafiye kan ɓarkewar Ebola

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasashe da dama na sanar da taƙaita tafiye-tafiye saboda fargabar da suke da ita akan yadda da cutar Ebola ke yaɗuwa.

    Canada ta haramtawa 'yan Uganda da Sudan ta Kudu shiga ƙasar har zuwa nan da watanni uku.

    Sauran yankunan da cutar ta fara ɓulla kuma 'yan ƙasar idan sun shiga Canadan sai sun keɓe kansu na tsawon makonni uku.

    Ita ma Bahamas ta fitar da makamanciyar sanarwar Canadan.

    Thailand kuma ta sanya dokar keɓe duk waɗanda suka shiga ƙasar daga yankin tsakiyar Afirka.

    A makon da ya gabata ne Amurka ta haramtawa 'yan ƙasarta zuwa ƙasashen da cutar ta Ebola ta ɓulla yayin da 'yan ƙasashen kuma suma aka haramta musu tafiya zuwa Amurkan.

    Rahotanni sun ce an keɓe wata mata daga Uganda da ta shiga Indiya a Bengaluru inda kuma aka same ta da cutar bayan gwajin da aka yi mata sakamakon rashin lafiyar da ta soma.

  16. Yadda aka yi sallar Idi a Abuja da Kano

    ...
    Bayanan hoto, Gwamna Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Murtala Sule Garo da sauran muƙarraban gwamnati

    Al'ummar Musulmi sun halarci sallar idi a masallatai da dama da ke faɗin duniya.

    A Abuja, babban birnin Najeriya, wakilin BBC ya shaida yadda aka yi sallar idi a Masallacin idi na Unguwar Katampe inda manya maza da mata har ma da ƙananan yara suka halarta.

    Kazalika a jihar Kano, gwamna Abba Kabir da mataimakinsa, Murtala Sule Garo sun yi idi a masallacin Ƙofar Mata inda Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar.

    Gwamnan ya halarci sallar tare da wasu muƙarraban gwamnatinsa.

    ...
    Bayanan hoto, Wasu daga cikin jami'an gwamnatin Kano da suka halarci sallar idi tare da gwamna Abba Kabir Yusuf
    ....
    Bayanan hoto, Masallata a masallacin Kofar Mata da ke Kano
    ...
    Bayanan hoto, Limamin da ya jagoranci sallar idi a masallacin unguwar Katampe
    ...
    Bayanan hoto, Sauran masallata da suka yi sallar idi a masallacin unguwar Katampe
    ...
  17. Ghana ta fara shirin kwashe ƴan ƙasarta kusan 800 daga Afirka ta Kudu

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Jami'ai daga Ghana za su kwashe kusan 'yan ƙasar 800 zuwa gida daga Afirka ta Kudu.

    Hakan ya biyo bayan zanga zangar nuna ƙyama ga baƙin hauren da ake a wasu sassan biranen Afirka ta Kudu fiye da wata guda ke nan.

    Wakiliyar BBC ta ce ta ga yadda gwamman mutane ke fita daga motocin bas inda suka isa filin jirgin saman Tambo suna hawa jirgin zuwa Accra.

    Jakadan Ghana a Afirka ta Kudu ya ce gwamnatinsu na son tabbatar da cewa 'yan Ƙasarsu sun kuƁuta daga hare-haren da ake kai wa baƘin hauren.

    Ghana ta ce tana tabbatar da tsare lafiyar 'yan Ƙasarta.

    Waɗanda suke zanga zangar sun ce yawancin mutanen da ke shiga cikin Ƙasar ta Afirka ta Kudu ba bisa Ƙa'ida ba na mamaye musu guraben aiki a ma'aikatun gwamnati.

  18. Isra'ila ta yi iƙirarin kashe sabon kwamandan Hamas

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta ce ta kashe wani Shugaban ɓangaren mayaƙan Hamas, Mohammed Odeh a wani hari da ta kai Gaza ranar Talata - kwanaki bayan mutuwar magabacinsa a wani hari makamancin wannan.

    Aƙalla Falasɗinawa uku aka kashe sannan gommai sun ji rauni a gagarumin harin na ranar Talata wanda ya faɗa kan wani gida a ɗaya daga cikin manyan kasuwannin birnin Gaza, kamar yadda shaidu suka bayyana.

    Sojojin Isra'ila sun ce an kai hari kan gine-ginen da ke zama maɓoyar Odeh bayan da aka bibiye shi tsawon watanni.

    Zuwa yanzu Hamas ba ta ce komai ba kan lamarin.

    Shi ne hari mafi muni da Isra'ila ta kai kan Gaza duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da Hamas wadda ta fara aiki a Oktoba.

  19. Musulmi na bikin babbar sallah a faɗin duniya

    Al'ummar Musulmai a faɗin duniya na bikin idin Babbar Sallah, bayan hawan Arafah jiya Talata a Ƙasa Mai Tsarki.

    Ranar na cikin manyan ranakun bikin Musulunci biyu a shekara.

    Biki ne da akan yanka rago ko sa inda wasu ke bayar da naman sadaka ga mabuƙata.

    Musulmi na yin amfani da muhimmin lokacin wajen sada zumunci a tsakanin ƴan'uwa da abokan arziki.

    A bana ranar ta zo daidai da ranar yara ta duniya da ake yi duk 27 ga watan Mayu.

    Kazalika, sallar ta zo yayin da ake ci gaba da yin yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.

  20. Barka da Sallah

    Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na marhaba da ɗumbin masu bibiyar mu a wannan rana da Musulmi a faɗin duniya ke bikin sallah babba.

    Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.

    Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo har ma ku tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.