Shugaban Majalisar Shari'ar Musulunci Nafiu Baba-Ahmed ya rasu
Allah ya yi wa Shugaban Majalisar Ƙoli kan Harkokin Shari’ar Musulunci a Najeriya, Mallam Nafiu
Baba-Ahmed rasuwa.
Mallam Nafiu Baba-Ahmed ya rasu ne
yau Talata bayan doguwar jinya.
Za a yi jana’izarsa anjima da
ƙarfe 1 na rana a masallacin ƙasa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Marigayin ya shafe shekaru 26 na rayuwarsa wajen hidimtawa Musulunci tare
da fafutukar tabbatar da adalci ga kowa.
Cikin waɗanda suka miƙa saƙon ta’aziyyar rasuwarsa har da Tsohon Ministan
Sadarwa na Najeriya, Sheikh Isa Pantami.
Pantami ya bayyana alhininsa ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa
na Fesbuk.
Ana ci gaba da aikin gano sojojin da suka mutu a hatsarin jirgi
Asalin hoton, Ondo SEMA
Gwamnatin Jihar Ondo ta ƙaddamar da aikin ceto sakamakon hatsarin wani
jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya da ya faru a yankin Igbokoda na Ƙaramar
Hukumar Ilaje a jihar Ondo.
Wakilan Gwamnan Jihar Ondo, Dr Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ƙarƙashin
jagorancin Babban Mataimaki na Musamman ga gwamnan kan agajin Gaggawa da
Tabbatar da Tsaro, Hon. Wellington Oriade Adebawo, sun ziyarci wurin da jirgin
ya yi hatsari jiya Litinin, domin tantance halin da ake ciki da kuma tallafawa
ƙoƙarin gano mutanen da ke cikin jirgin.
Tawagar ta ƙunshi jami’an Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Ondo da
Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), wakilin ƙungiyar agaji ta Red Cross
ta Najeriya, da kuma wani mai bai wa gwamna shawara, Hon. Cornelius Owolewa.
Mai Bai wa Gwamnan Shawara na Musamman kan Harkokin Sadarwa, Hon. Allen
Sowore, shi ma ya haɗu da tawagar a wurin da jirgin ya yi hatsari.
Jirgin, mai lamba NAF 970, nau’in ATR-42 ne da Rundunar Sojin Saman
Najeriya ke amfani da shi. An ruwaito cewa yana ɗauke da mutum 32, waɗanda suka
haɗa da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgi bakwai, lokacin da ya yi hatsari a
yankin Igbokoda yayin da yake kan aiki daga Benin zuwa Lagos.
Gwamnatin Jihar Ondo ta nuna damuwa kan lamarin tare da jaddada aniyarta ta
ci gaba da tallafa wa aikin da ake gudanarwa.
Ta kuma yi kira ga mazauna yankin da sauran jama’a su kwantar da hankalinsu
tare da dogaro da sahihan bayanai daga hukumomi yayin da ake ci gaba da aikin
nema.
Asalin hoton, Ondo SEMA
Najeriya na makokin mutuwar sojojinta a hatsarin jirgin sama
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya ayyana zaman makoki na kwanaki
uku sakamakon hatsarin jirgin soji da ya faru a jihar Ondo inda kuma ya bayar
da umarnin gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin.
Haka kuma, Tinubu ya bayar da umarnin a yi ƙasa ƙasa da tutoci domin girmama jami’an sojin da
suka rasu a hatsarin jirgin.
A wata sanarwa da
mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, Tinubu
ya “miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai da
lamarin ya shafa, da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke,
da daukacin hafsoshi da jami’an Rundunar Sojin Saman Najeriya.”
Hatsarin jirgin
dai ya yi ajalin dukkan mutum 32 da ke ciki da suka hada da fasinjoji 25 da
ma'aikata 7.
“Wannan lokaci ne
mai matuƙar raɗaɗi ga Rundunar Sojinmu da ma ƙasa baki ɗaya. Jami’an Rundunar Sojin Samanmu suna jefa
rayukansu cikin haɗari a kowace rana domin tabbatar da tsaron Najeriya. Ba
za a taɓa mantawa da sadaukarwar da suka yi ba,” in ji Tinubu.
Assalamu Alaikum
Masu bin wannan shafin barkan mu da safiyar wannan rana ta Talata.
Nabeela Mukhtar Uba ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da makwabtanta.
Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.