Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/053/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 25 ga watan Mayun 2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin namu.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Mu kwana lafiya.

  2. Rasha ta gargaɗi ƴan ƙasashen waje da ke Ukraine su fice daga Kyiv

    Rasha ta gargaɗi ƴan ƙasashen waje da ke Ukraine, ciki har da jami'an diflomasiyya, su fice daga Kyiv, inda ta ce tana shirin kai wasu hare-hare kan babban birnin ƙasar.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce dakarun Rasha za su kai hari ne kan kamfanonin samar da kayayyakin tsaro na Ukraine, waɗanda ke tsarawa da samar da jirage marasa matuƙa.

    Sanarwar ta ce Rasha ta shirya kai harin ne a matsayin martani, kan abin da ta bayyana a matsayin hari da gangan da Ukraine ta kai, kan wata makaranta da ginin ɗalibai, a wani yanki na gabashin Ukraine da Rasha ta mamaye.

    Rundunar sojin Ukraine ta musanta kai hari kan fararen hula da gangan.

  3. Sojojin Najeriya sun yi gargaɗin samun hare-haren ƙunar-baƙin-wake a lokacin bukukuwan salla

    Babban hafsan sojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rundunar sojin Najeriya ta gargaɗi mazauna yankin Arewa maso Gabashin ƙasar kan yiwuwar hare-haren ƙunar baƙin wake da na bama-bamai da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP za su iya kaiwa yayin bukukuwan Babbar Sallah.

    A cikin wata sanarwa da shalkwatar rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce sahihan bayanan sirri sun nuna akwai yiwuwar mayaƙan ƙungiyoyin biyu za su yi amfani da lokacin bukukuwan Babbar Sallah wajen kai hare-hare kan fararen hula, musamman a wuraren da jama’a ke taruwa don gudanar da shagulgula.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, rundunar ta tura dakarunta zuwa muhimman wurare masu hadari a dukkanin sassan yankin, yayin da aka sanya na’urorin tattara bayanan sirri domin bibiyar duk wata barazana da kuma tallafa wa ayyukan tsaro da ake gudanarwa.

    Haka kuma sanarwar ta ce an ƙara yawan sintiri, tare da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da sauran hukumomi da kuma jami’an tsaro na JTF da ƙungiyoyin sa-kai, domin hana duk wata ɓaraka ta tsaro a lokacin bukukuwan Babbar Sallah.

    Haka kuma rundunar ta shawarci mazauna yankin su kasance cikin shiri tare da kauce wa zirga-zirgar da ba ta zama dole ba, musamman da daddare da kuma wuraren da babu jami’an tsaro.

    Sanarwar ta kuma buƙaci jama’a su gudanar da sallar Idi da sauran bukukuwa a kusa da gidajensu, su guji manyan taruka, sannan su gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani mutum ko motsi da ba su gamsu da shi ba, ko kuma wani abu da aka yasar babu mai kula da shi.

    Rundunar sojin ta kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa dakarunta na cikin shirin ko-ta-kwana, tare da cikakken shiri domin hana mayaƙan samun damar kai hare-hare a duk lokacin bukukuwan Sallah.

    Rundunar ta ce ta jibge dakarunta tare da kayan sa ido domin daƙile duk wata barazana.

  4. WHO ta ce cutar Ebola na ci gaba da barazana a DR Congo

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesu, ya ce yaɗuwar cutar Ebola a ciki da wajen Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo, na nema ta fi karfin ƙoƙarin da hukumomi ke yi wajen daƙile cutar.

    Ya ce jinkirin da ake samu wajen gano masu ɗauke da cutar, ya sa masu yaƙi da ita na fuskantar cikas a ƙoƙarinsu na shawo kanta.

    WHO ta ce zuwa yanzu mutum 220 ne ake zargin sun mutu sakamakon cutar ta Ebola.

    Ƙungiyar agaji ta RedCross na gudanar da jana'iza cikin taka tsan-tsan ƙarƙashin kariyar jami'an tsaro domin a guje wa yaɗuwar cutar.

    Hukumomi a Uganda sun tabbatar da ƙarin mutum biyu da suka kamu da cutar Ebola.

  5. Gwamnatin Katsina ta nesanta kanta daga tsohon hadimin gwamnan da aka kama kan zargin garkuwa da mutane

    Gwamnan Katsina

    Asalin hoton, Dikko Umar Radda/X

    Gwamnatin jihar Katsina da ke arewa maso gabashin Najeriya ta nesanta kanta daga wani tsohon mashawarcin gwamnan jihar da aka kama kan zargin satar mutane domin neman kuɗin fansa.

    A baya-bayan na ne ƴansandan jihar suka kama mutumin mai suna Nura Aliyu da aka fi sani da Nura Garwa kan zargin sace wani ƙaramin yaro mai shekara takwas.

    Kwamishinan al'amuran tsaron cikin gida na jihar ya shaida wa BBC cewa jami'an tsaro sun kama mutumin tare da wasu mutum bakwai da yake aiki tare da su.

    ''Shi ne ya kama yaron, kuma ya tsara duk hanyar da za a bi wajen karɓar kuɗin fansar'', in ji kwamishinan.

    Aliyu Garwa shi ne tsohon mataimaki na musamman ga gwamnan Katsina kan harkokin ci gaban al'umma, kodayake a baya-bayan nan ya ajiye aiki, inda bayanai suka nuna cewa ya tsaya takarar ɗan majalisar jiha, kodayake bai yi nasara ba.

    To amma gwamnatin Katsinan ta ce dama tun kafin faruwar lamarin ta kore shi daga aiki, bayan da ta same shi da laifukan rashin gaskiya.

  6. Gwamnatin Najeriya ta bayar da hutun Babbar Sallah

    Shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Bola Tinubu/X

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Laraba 27 ga watan Mayu da Alhamis, 28 ga watan a matsayin ranakun hutu a ƙasar domin shagulgulan Babbar Sallah.

    Cikin wata sanarwa da sakataren dindindin na ma'aikatar cikin gida na ƙasar ya fitar a madadin, ministan cikin gidan ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce gwamnati ta bayar da hutun ne domin nuna martabawa ga miliyoyin musulman ƙasar.

    Sanarwar ta ce ta bayar da hutun ne domin musulman ƙasar su samu damar yin shagulgular Babbar Sallah kamar yadda sauran Musulman duniya ke gudanarwa.

    Ministan ya kuma taya al'ummar musulman ƙasar na ciki da wajen ƙasar su yi amfani da muhimmin lokacin domin yi wa ƙasar addu'o'in samun zaman lafiya da ci gaba.

    A ranar Laraba ne msulman duniya za su gudanar da Idin Babbar Sallah bayan tsayuwar Arfa da mahajjata za su yi a Saudiyya ranar Talata.

  7. Cutar ƙyanda ta kashe yara fiye 500 a Bangladesh

    Hukumomi a Bangladesh sun ce ana zargin fiye da yara 500 sun mutu a ƙasar tun daga watan Maris, bayan da aka samu ɓarkewar cutar ƙyanda mafi muni tsawon shekaru.

    Akwai wasu aƙalla 500 da aka tabbatar sun kamu da cutar ko kuma suna nuna alamun kamuwa da ita.

    Zuwa yanzu mutum 60,000 aka tabbatar sun kamu da cutar ko ake zargin suna ɗauke da ita a ƙasar.

    Gwamnatin Bangaldesh na ci gaba da gudanar da gagarumin gangamin yin alurar riga-kafin cutar.

    Sai dai ba lallai a ga tasirin hakan ba nan da watanni masu zuwa, duk da cewa ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta ce ta soma ganin alamun raguwar cutar a yankunan da ta fi shafa.

    Ƙyanda cuta ce da ke yaɗuwa sosai, ta hanyar yin tari ko atishawa, musamman tsakanin ƙananan yara.

  8. Gwamnatin Taliban ta ƙi yin bayanin lokacin da ƴanmata za su koma makaranta

    ...

    Asalin hoton, ..

    Wani kakakin gwamnatin Taliban na Afghanistan ya ƙi amsa tambayar da BBC ta yi masa kan lokaci da za a bar ƴan mata da mata su ci gaba da zuwa makaranta a ƙasar.

    Gwamnatin Taliban dai ta haramta wa matan da suka kai shekara 12 zuwa makaranta, jim kaɗan bayan da ta ƙwace mulki shekaru biyar da suka gabata.

    Kakakin gwamnatin, Hamdullah Fitrat, ya ce gwamnatin Taliban ɗin ta dukufa wajen bai wa mata hakkin su ƙarƙashin dokokin musulunci.

    Majalisar Ɗinkin Ɗuniya ta ce idan matakin haramcin na Taliban ɗin ya zarce har 2030, za a tauye wa mata fiye da miliyan biyu damar samun ilimin gaba da firamare.

    Wata ƴar Afghanistan ta ce idan ta ga maza sa'ointa sun kammala sakandire, har za su shiga jami'a, sai ta ji wani baƙin ciki a ranta.

  9. Firaministan Pakistan ya gana da shugaban China

    Kamfanin dilllancin labarai na China, Xinhua ya bayar da rahoton cewa firaminstan Pakistan Shebaz Sharif ya gana da shugaban China Xi Jinping a lokacin wata ziyara da yake yi a Beijing.

    Ziyarar firaministan wanda ke tare da babban hafsan sojin Pakistan wani ɓangare ne na ci gaba da amfani da diplomasiyya domin kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka.

    A baya-bayan nan an bayar da rahoton ziyarar babban hafsan sojin na Pakistan, wanda shi ne babban mai shiga tsakani na ƙasar zuwa China.

    Mista Sharif ya kuma gana da Firimiyan China Li Keqiang.

  10. Iran na shirin dawo da intanet bayan dogon lokaci da katse shi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin musamman da gwamnatin Iran ta kafa domin tsara harkokin intanet ya gudanar da taronsa na hudu ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban kasa na farko, Mohammad Reza Aref.

    A taron, an amince da wasu muhimman shawarwari da suka shafi yanayin intanet a ƙasar, waɗanda za a miƙa wa ma’aikatar sadarwa domin aiwatarwa bayan shugaban kasa Masoud Pezeshkian ya bayar da amincewa ta karshe.

    Ko da yake gwamnati ba ta bayyana cikakken bayani kan matakan da aka dauka ba, kamfanin dillancin labarai na Fars ya rawaito cewa kwamitin ya amince da shirin dawo da intanet da kuri’u tara masu goyon baya hakan. Rahoton ya ce an aika da ƙudurin zuwa ofishin shugaban kasa domin tabbatarwa kafin fara aiki da shi.

    Tun bayan ɓarkewar yaƙin baya-bayan nan, mafi yawan al’ummar Iran sun rasa damar amfani da intanet sai dai wasu ƙalilan masu amfani da “Internet Pro”, katin SIM na musamman ko kuma tsarin Starlink.

    Ana kallon wannan katsewar a matsayin mafi tsawo da aka taba samu a tarihin katewar intanet a Iran.

  11. An tabbatar da ƙarin mutum biyu sun kamu da cutar Ebola a Uganda

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Uganda sun tabbatar da mutum biyu sun kamu da cutar Ebola, wanda ya sa adadin wadanda suka kamu da ita a kasar ya kai bakwai tun bayan da aka gano bullar ta kwananki 10 baya.

    Mutunen biyu duk sun kasance ma'aikatan lafiya ne da ke aiki a wani asibiti mai zaman kansa a Kampala, kuma a yanzu haka suna karɓar kulawar gaggawa.

    Jami'an kiwon lafiya na bibiyar mutanen da suka yi mu'amula da su, kuma sun buƙaci ƴan ƙasar su bayar da rahoton duk wanda suka ga yana nuna alamomin cutar.

    Shugaban Hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce zuwa yanzu mutum ɗari biyu da ashirin ne ake zargin sun mutu sakamakon cutar ta Ebola.

  12. Fafaroma Leo ya yi gargaɗi game da haɗarin amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    A cikin bayaninsa na farko kan alƙiblar cocin katolika, Fafaroma Leo ya yi gargaɗi game da haɗarin amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI, inda ya yi kiran a samar da yadda za a yi amfani da ita ta hanyar da ya kamata.

    Takardar na yi wa ƴan ɗarikar katolika karin bayani ne game da koyar war cocin kan amfani da fasahar.

    A cikin sakon, fafaroma ya nemi afuwa kan tsawon lokacin da aka kwashe kafin cocin katolika ya yi Allawadai da bautar da bayi, inda ya yi gargaɗin cewa AI na iya ƙirƙirar sabbin hanyoyin yin bauta.

    Fafaroma Leo ya kuma yi gargaɗi game da amfani da ƙirkirarriyar basira ta AI a fannin aikin soji, inda ya ce dole a raba AI da makamai.

  13. Ya kamata ƙasashen Larabawa su kyautata alaƙarsu da Isra'ila - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donlad Trump ya ce ya kamata Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa, har ma da Pakistan, su kyautata alaƙarsu da Isra'ila, a wani ɓangare na ƙokarin da ake yi na samar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya.

    Trump ɗin na so ƙasashen su sanya hannu kan yarjejeniyar Abraham, wadda ta tuni kasashen da dama suka sanya wa hannu domin kulla yarjejeniya da isra'ila, ciki har da Bahrain da Haɗaɗiyyar daular Larabawa.

    Buƙatar Trump na zuwa ne a yayin da gwamnatinsa ke kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran.

    A cikin jawabin Trump na baya bayan nan, ya ce ko dai a cimma gagarumar yarjejeniya mai ma'ana, ko kuma a bar batun gabadaya.

    Sai dai jami'an Iran sun ce har yanzu akwai abubuwan da ba a kammala ba kafin cimma yarjejeniyar.

  14. Ko a cimma yarjejeniya mai inganci da Iran ko kuma a watsar - Trump

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amruka, Donald Trump ya sake bayyana goyon bayansa ga tattaunawar da ake yi da Iran, yana mai cewa ko dai a cimma “babbar yarjejeniya mai amfani” ko kuma babu wata yarjejeniya gaba ɗaya.

    Trump ya soki ’yan siyasar Jam’iyyar Democrat da kuma wasu na Jam’iyyar Republican da ke nuna adawa da tattaunawar, inda ya kira su “wawaye” da ba su fahimtar ainihin abin da yarjejeniyar za ta iya kawowa.

    A shafinsa na Truth Social, ya bayyana su a matsayin “masu rarraba jama’a” da ke yawan suka ga abin da ya kira nasarorinsa.

    Ya kuma jaddada cewa duk wata yarjejeniya da Iran za ta kasance mai “ƙarfi da tasiri,” ko kuma babu wata yarjejeniya kwata-kwata.

    A cikin ’yan kwanakin nan, wasu ’yan majalisar dokokin Amurka daga jam’iyyun biyu sun nuna damuwa kan yiwuwar yarjejeniyar gwamnatin Trump da Iran.

  15. Gwamnan babban bankin Iran na kan hanyar zuwa Qatar kan kadarorin ƙasar da aka ƙwace

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan babban bankin Iran, Abdolnaser Hemmati na kan hanayarsa ta zuwa ƙasar Qatar domin tattaunawa da ta shafi kuɗaɗen Iran da aka ƙwace a ƙasashen waje.

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labaran ƙasar sun bayyana cewa wannan tafiya ta biyo bayan tattaunawa da wata tawagar Qatar ta yi a Tehran kan batun kuɗaɗen Iran da aka ƙwace a asusun waje.

    Daya daga cikin muhimman bukatun Iran a tattaunawarta da Amurka shi ne a saki waɗannan kuɗaɗe da aka ƙwace a ƙasashe daban-daban, ciki har da Qatar.

    A lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar, Ebrahim Raisi, an riga an tura wani ɓangare na kuɗaɗen Iran da aka ƙwace daga bankunan Koriya ta Kudu zuwa Qatar.

    An ce an saka su ƙarƙashin kulawar Amurka domin sayen muhimman kayayyaki kamar abinci da magunguna, tare da wani shiri na musayar fursunoni da Amurka.

    Sai dai bayan musayar fursunonin, ba a kammala tura kuɗaɗen zuwa Iran ba. Rahotanni sun danganta hakan da tashin hankali da ya biyo bayan yaƙin Gaza da ya fara da harin 7 ga Oktoba wanda ya dagula tsarin.

    Shugaban addini na Iran, Ali Khamenei, ya taɓa bukatar a hanzarta sakin waɗannan kuɗaɗe yayin ziyarar sarkin Qatar a Tehran a watan Fabrairu 2024.

  16. Shugaban majalisar dokokin Senegal El Malick ya yi murabus

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Majalisar Dokokin ƙasar Senegal, El Malick Ndiaye ya yi murabus daga muƙaminsa kwana biyu bayan korar firaminista Ousmane Sonko, lamarin da ya tayar da zargin cewa ana shirin ba Sonko damar komawa cikin majalisa da kuma neman sabon muƙami.

    A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Ndiaye ya ce matakin nasa ya samo asali ne daga “zurfin tunani” da kuma “la’akarin kishin ƙasa,” yana mai cewa akwai lokuta da muradin ƙasa ke bukatar fifikon gaskiya kan komai.

    Bayan murabus ɗinsa, an kira zaman majalisar dokoki da za a yi a ranar Talata domin shirya mayar da Sonko kujerarsa ta majalisa tare da zaɓen sabon Shugaban Majalisar.

    Sonko, wanda shi ne shugaban jam’iyyar PASTEF, ya riga ya lashe kujera a zaɓen 2024 amma ya ajiye ta lokacin da ya zama Firaminista.

    Ƙasar Senegal na fuskantar sabon yanayin siyasa, inda ake ganin dangantaka tsakanin Shugaba Bassirou Diomaye Faye da Sonko na iya kawo canji ga ikon gwamnati, musamman ganin jam’iyyar PASTEF na da rinjaye a majalisa, abin da ke ƙara haifar da rashin tabbas kan yadda sabuwar gwamnati za ta gudanar da mulki.

  17. 'Sama da mutum 125,000 sun kamu da matsalolin fata a Gaza'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar agajin ’yan gudun hijira ta Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNRWA ta ce ta gano fiye da mutum 125,000 da ke fama da cututtukan fata da suka samo asali daga cizon ɓeraye da ƙwari a yankin da ke fama da rikici a zirin Gaza

    Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na X, inda ta ce tawagogin lafiyarta na ci gaba da feshin magungunan kashe ƙwari tare da tsabtace wuraren da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu ke zaune.

    UNRWA ta ce ƙarancin man fetur da magungunan feshi da tantuna da magunguna na ƙara tauye ƙoƙarin shawo kan matsalar.

    Ta kuma jaddada cewa yankin na buƙatar samun damar kai kayan lafiya da magunguna ba tare da takura ba domin rage yaɗuwar cututtuka.

    A halin yanzu, dubban Falasɗinawa da suka rasa gidajensu na ci gaba da rayuwa cikin tantuna, yayin da ake fargabar cewa rashin tsafta da cunkoso na ƙara haifar da yaɗuwar cututtuka.

  18. FRSC ta buƙaci matafiya su kauce wa hanyar Abuja-Kaduna saboda cunkoso

    ...

    Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya Federal Road Safety Corps ta shawarci direbobin da ke tafiya ta hanyar Abuja zuwa Kaduna da su yi amfani da wasu hanyoyi domin kauce wa cunkoson da ke addabar babban titin a wannan lokaci na bukukuwan Babbar Sallah.

    Hukumar ta ce ana samun taruwar ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon yawan masu tafiya Sallah da kuma ayyukan gyaran hanya da ke gudana a wasu sassa na titin. Wannan hali ya sa motsin ababen hawa ya ragu musamman a yankin Katari zuwa Jere.

    A dalilin haka ne FRSC ta shawarci matafiya su yi amfani da wasu hanyoyi, kamar hanyar Kaduna–Kachia–Maraban Kubacha–Jere–Bwari–Dutse Abuja zuwa Abuja ko Kaduna saboda ƙaurace wa cunkoso.

    Ta ce waɗannan hanyoyi za su taimaka wajen guje wa cunkoso da rage shi da kuma inganta tafiyar ababen hawa a lokacin bukukuwa.

    Hukumar ta kuma bukaci direbobi su ci gaba da bin dokokin hanya, su guji tukin ganganci da satar hannu/hanya, tare da bin umarnin jami’an kula da hanya.

  19. An sauya masu tsaron shugaban ƙasar Kenya bayan kutsen wani matashi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin ’yan sanda a Kenya sun sanar da yi wa manyan masu tsaron Shugaban ƙasar William Ruto garambawul bayan wani mutum ya tsallake matakan tsaro inda ya kusta ya kai ga kusa da shugaban yayin taron jama’a a gundumar Kilifi.

    Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a Bamba, inda Shugaba Ruto ke yi wa jama’a jawabi daga kan dandali.

    Bidiyon da ya yaɗu ya nuna wani matashi riƙe da Littafi Mai Tsarki yana kutsa kai cikin jama’a kafin ya kai ga kusa da shugaban na ɗan lokaci kafin aka kama shi.

    Babban Sufeton ’yan sanda Douglas Kanja ya ce wannan lamari ne mai matuƙar muhimmanci kuma ba za a amince da shi ba, inda ya umarci a binciki yadda aka samu wannan gibi a tsarin tsaro.

    Hukumomi sun kuma amince cewa akwai matsala a daidaiton aiki da kula da taron jama’a.

    Bayan faruwan lamarin ne aka sauya shugabannin wasu rukunin tsaro na musamman ciki har da masu gadin shugaban ƙasa, sannan an kafa kwamitin bincike domin gano yadda aka samu wannan gazawa a tsaron taron.

  20. Ƙasashen DR Congo, Uganda da Sudan sun haɗa kai kan yaƙi da cutar Ebola

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministocin lafiya na ƙasashen DR Congo da Uganda da Sudan ta Kudu sun gana a Uganda a ranar Asabar domin ƙarfafa haɗin gwiwa kan dabarun daƙile cutar Ebola a iyakokin ƙasashen.

    Sun amince da haɗin kai wajen sa ido kan cutar da binciken masu ɗauke da ita da kuma musayar bayanai, yayin da aka saka Sudan a shirin duk da cewa ba ta sanar da ɓarkewar cutar a hukumance ba.

    A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, tawagogin agaji na ci gaba da aiki, inda aka kafa ɗakin gwaje-gwaje a Bunia da babban birnin lardin Ituri, lamarin da ya rage jinkiri wajen gwaje-gwaje.

    Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙarin tabbacin cewa mutum 101 sun kamu da cutar, yayin da aka gano kusan mutane 904 na cikin haɗarin kamuwa da cutar inda ake sa musu ido. Haka kuma, akwai wasu 1,817 da ake zargin sun yi mu’amala da masu dauke da cutar a cikin iyalai da al’umma.

    Haka kuma, ana zargin waɗanda suka mutu sakamakon cutar sun kai 119 zuwa ranar 23 ga Mayu, 2026.

    A halin da ake ciki, cutar ta bazu daga yankuna uku zuwa yankunan lafiya 11 a gabashin Kongo, yankin da ke fama da rikici da gudun hijira.