Zanga-zangar ƙin jinin baƙin haure ta sake ɓarkewa a Afurka ta Kudu
An samu ɓarkewar zanga-zangar tarzoma a wasu sassan Afirka ta Kudu, kan baƙin haure da suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.
An ƙona motoci a Soweto da Durban, inda rahotanni suka ce an kuma kai hari kan shagunan da ƴan ƙasashen waje suka mallaka.
An kuma samu irin wannan zanga-zanga a Cape Town da Eastern Cape. Ƴansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da suka kutsa cikin wata cibiyar ƴan gudun hijira, inda ɗaruruwan masu neman mafaka suka taru domin shigar da ƙorafe-ƙorafe.
Hakan ya biyo bayan hukuncin kotun tsarin mulkin ƙasar, wanda ka iya bai wa dubban bakin haure damar neman izinin ci gaba da zama a Afirka ta Kudu.
Harin mayaƙan Houthi ya fada makarantar yara a Saudiyya
Hukumar Civil Defence ta Saudiyya ta ce ɓaraguzan wani makami mai linzami da aka kakkaɓo sun lalata wata makarantar yara da kuma cibiyar kula da lafiya a Riyadh, babban birnin ƙasar.
Ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta a Yemen ya ce ya kakkaɓo makamai masu linzami guda biyu da 'yan Houthi da Iran ke marawa baya suka harba zuwa Riyadh.
A nasu ɓangaren, ƴan tawayen Houthi sun ce filin jirgin saman Riyadh ne suka kai wa harin. Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna hayaki mai yawa yana tashi daga filin jirgin saman.
Tashin hankali ya ƙara ƙazancewa tsakanin ƴantawayen Houthi na Yemen da Iran ke marawa baya, da ƙawancen dakarun da Saudiyya da kasashen duniya ke goyon baya.
An sake gabatar da sabbin tuhume-tuhumi kan Maduro
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Amurka ta kai farmakin soji a Venezuela tare da kama shugaba Maduro da mai ɗakinsa
Masu gabatar da ƙara a Amurka sun shigar da ƙarin tuhume-tuhume kan tsohon shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, da matarsa Cilia Flores.
Sabbin zarge-zargen, waɗanda dukkansu suka musanta, sun shafi azabtar da mutanen da aka tsare a ƙarƙashin gwamnatinsa, ciki har da wasu ’yan ƙasar Amurka.
Kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce daga cikin Amurkawan aƙwai wasu shugabannin kamfanonin mai da aka tsare na tsawon shekaru biyar, cikin yanayin da lauyoyinsu suka bayyana cewa ya yi muni.
Maduro da Flores na jiran shari’a a birnin New York kan zargin ta’addanci da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda suka musanta zarge-zargen.
Haka kuma an ƙi amincewa da bukatar Cilia Flores ta samun beli bisa dalilai na rashin lafiya.
Gwamnatin Najeriya za ta rage farashin man fetur na wata ɗaya
Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ‘yan ƙasar za su fara sayen man fetur a farashi mai rahusa a gidajen man NNPC na tsawon kwanaki 30 masu zuwa.
Ministan Kuɗi da daidaita tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce: “Za a samu rangwame kan farashin man fetur a gidajen NNPC na tsawon kwanaki 30 masu zuwa, tare da bai wa masu harkokin sufuri na jama’a fifiko.”
Ministan ya ƙara da cewa gwamnati za ta kuma samar da abin da ya kira “sauke farashin kayayyki da aka yi yarjejeniya a kansa”, wanda za a riƙa sake dubawa duk wata.
A cewarsa, gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne saboda matakan da aka ɗauka a baya ba su magance matsin tattalin arzikin da iyalai da ‘yan kasuwa ke fuskanta gaba ɗaya ba, musamman bayan hauhawar farashin man fetur da kuɗin sufuri.
A ƙarƙashin sabon tsarin da gwamnati ke shirin aiwatarwa na daidaita farashin man fetur, ana tattaunawa kan iyakance farashin litar fetur kan naira 1,350, tare da sake duba wannan farashi a kowane wata.
Babu wanda za mu bari ya mallaki uranium ɗinmu ba - Iran
Kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran sun ruwaito shugaban Hukumar Makamashin Nukiliyar Iran, Mohammad Eslami, na cewa Iran ba za ta daina haɓaka sinadarin uranium ba, haka kuma ba za ta miƙa tarin uranium ɗin da ta riga ta tace ba.
Mista Eslami ya ce sabunta barazanar da Amurka ke yi kan cibiyoyin nukiliyar Iran ba wani sabon abu ba ne, yana mai jaddada cewa aikin tace uranium wani muhimmin ɓangare ne na shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Ya ƙara da cewa Iran ba za ta yi watsi da wannan ɓangaren na shirinta na nukiliya ba, duk da matsin lamba da barazanar da take fuskanta daga ƙasashen yamma.
Tun da farko, jami’an Iran sun bayyana cewa ci gaba da tattaunawar nukiliya da Amurka na da sharaɗi, ciki har da buƙatar Tehran cewa Amurka ta kawo ƙarshen katangar ruwa da sojojin ruwanta suka ƙaƙaba wa Iran.
Habasha ta zargi Eritrea da girke sojoji a arewacin yankin Tigray
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Bayanan hoto, Sojojin Eritrea sun shiga yaƙin da aje yi a yankin Tigray tsakanin shekarun 2020-2022.
Ya yin da rikici ke ƙara kamari a yankin Tigray na Habasha, hukumomin ƙasar sun zargi Eritrea da keta hurumin ƙasar ta hanyar girke dakarunta a arewacin yankin Tigray.
Ministan harkokin wajen Habasha, Berhanu Tsegaye, ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da shiga tsakani da ɗaukar matakin gaggawa akan Asmara da ake zargin ta na wuce makaɗi da rawa da tsoma baki a harkokin maƙofciyar ta su.
Ya yi garɗi kan ƙaruwar tashin hankali da halin rashin tabbas da ake ciki a ƙasar, da fargabar sake faɗawar kasar cikin yaƙin basasa.
Tashin hankali na baya-bayan nan na zuwa ne, bayan hukumomin Habasha sun yanke duk wata hulɗar Diflomasiyya da maƙofciya Eritrea da korar jami'an diflomasiyyarta, kan zargin haɗa kai da ƙungiyoyin ƴantawayen yankin Tigray da ƙoƙarin kifar da gwamnati.
Ita ma ta maida martaniya ta hanyar sanar da yanke duk wata hulɗar diflomasiyyar tsakaninsu na har illa masha Allahu, ta kuma musanta hannu a tashin hankalin da ke faruwa a arewacin ƙasar ta Habasha.
Ba za mu kai wa Iran hari kafin zaɓen tsakiyar wa'adi ba - Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce: "Muna tattaunawa mai ma’ana da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma ba za mu kai wa Iran hari ta kowace hanya ba kafin zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka da za a gudanar ranar 3 ga watan Nuwamba."
A cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, Trump ya ce: "Ina son in bayyana wa kowa karara cewa duk da mawuyacin halin da Iran ke ciki, ta fuskar tattalin arziki da ta soja, kuma duk da cewa takunkuman da aka ƙaƙaba mata har yanzu suna nan daram, ba za mu kai mata hari ba kafin zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka na ranar 3 ga watan Nuwamba."
Ya kuma maimaita kalamansa kan yadda jiragen dakon mai ke ci gaba da bi ta mashigar ruwa ta Hormuz da adadin man da ba a taɓa gani ba, yana mai cewa ganga miliyoyin na man fetur na ratsa yankin.
Trump ya ce ganga miliyan 22 na man fetur ne suka bi ta yankin a daren jiya kaɗai, ba tare da ko ganga guda ta fito daga Iran ko kuma ta nufi ƙasar ba.
A ƙarshen saƙonsa, Trump ya rubuta cewa: "Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba."
Tun da farko, wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Pentagon ta umarci rundunar CENTCOM, wato rundunar sojin Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya, da ta kammala shirye-shiryenta domin yiwuwar sake fara manyan hare-haren soja kan Iran.
'Ba a bi ƙa'ida ba a sammacin kama Andrew'
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mountbatten-Windsor remains under police investigation despite a ruling that the way search warrants were issued was unlawful
Kotu ta sanar da cewa ƴansandan Thames Valley sun amince takardar sammacin da sukai amfani da ita wajen binciken gidan Andrew Mountbatten-Windsor a lokacin da suka kama shi a watan Fabrairu ta saɓawa doka.
Sai dai duk da haka, kayayyakin da ƴansandan suka kama a lokacin samamen gidan Andrew za su ci gaba da kasancewa a hannunsu har sai an sake zaman kotun a shekarar 2027, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike kan muggan laifukan da ake zargin Mountbatten-Windsor da aikatawa.
Tsohon Yariman masarautar ta Birtaniya ya musanta zabe-zargen da akai ma sa, kuma ranar 19 ga watan Fabrairun bana ne ƴansanda suka kama shi aikata ba daidai ba lokacin da ya na bakin aiki kuma tun daga lokacin ya ke kalubalantarsu kan sahihancin samamen da suka kai gidan shi.
Jami'an tsaron sun ce sun amince sammacin ya saɓawa dokar kotu, saboda rashin bayyana takamaimai binciken da za su yi.
A zaman babbar kotun na ranar Alhamis, maishari'a Mista Justice Hilliard ya ce an cimma yarjejeniya tsakanin Mountbatten-Windsor da ƴansanda sun amince da kuskuren da suka aikata.
'Iran ta ce za ta kai hari sansanonin sojin Amurka na Jamus'
Asalin hoton, Getty Images
Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ambato jaridar Wirtschaftswoche ta Jamus na cewa Iran ta sanya sansanonin sojin Amurka da ke Jamus, ciki har da Ramstein da Spangdahlem, cikin jerin wuraren da za ta iya kai wa hari.
Rahoton, wanda ya ambato wasu jami’an leƙen asirin ƙasashen yamma da ba a bayyana sunayensu ba, ya ce Isra’ila ta yi wa abokan hulɗarta na Amurka da Jamus gargaɗi game da yiwuwar barazanar kimanin makonni uku da suka gabata.
Damuwar ta shafi sansanonin da ke ba da goyon bayan ayyukan soja da kuma kayan aiki da suka danganci rikicin da ake yi da Iran.
Ma’aikatar Tsaron Jamus da kuma rundunar sojin Amurka da ke ƙasar Jamus ba su yi wani tsokaci kan batun ba zuwa yanzu.
A wani labarin kuma, wani ɗan ƙasar Iran da aka tsare a wannan mako yayin da ake kama da yi wa wasu mutane tambayoyi kan zargin shirya kai hari kan wani sansanin sojin sama na Birtaniya, ya samu beli kuma an sake shi.
An bayyana mutumin a matsayin ɗan ƙasar Iran mai shekaru 25.
Sansanin jiragen saman soji na Fairford da ke Birtaniya na ɗaya daga cikin wuraren da jiragen ruwan bama-bamai na Amurka ke amfani da su.
'Amurka na duba yiwuwar sake kai manyan hare-hare kan Iran'
Asalin hoton, Reuters
Wasu kafafen yaɗa labarai biyu na Amurka sun ruwaito cewa Ma’aikatar tsaron ƙasar, Pentagon na shirin duba yiwuwar kai wani sabon hari kan Iran a cikin kwanaki masu zuwa.
Shafin labarai na Axios, ya ambatoo jami’an Amurka, na cewa a kwanakin baya-bayan nan Pentagon ta umarci CENTCOM, wato rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya, ta kammala shirye-shiryenta domin yiwuwar sake fara manyan hare-haren soja kan Iran.
Ita ma mujallar The Atlantic, a wani rahoto na musamman da ta wallafa tare da ambato wasu jami’an Amurka biyu, ta ce Fadar White House ta buƙaci Pentagon ta tsara zaɓuɓɓukan kai hare-hare kan wurare a Iran da za a iya aiwatarwa kafin zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka.
A cewar The Atlantic, shugaban Amurka Donald Trump na da muradin ganin an rage farashin man fetur tare da samun gagarumin ci gaba a rikicin da Iran kafin gudanar da zaɓen.
Sai dai Axios ta ce umarnin da Pentagon ta bayar bai ƙayyade takamaiman ranar da za a fara hare-haren ba, kuma har yanzu Donald Trump bai yanke hukunci na ƙarshe ba kan lamarin.
Duk da haka, majiyoyin Amurka da Isra’ila sun shaida wa Axios cewa ana iya ɗaukar matakin kafin zaɓukan tsakiyar wa’adin mulkin Amurka, watakila ma kafin zaɓukan Isra’ila da ake gudanarwa mako guda kafin na Amurka.
Ana sa ran gudanar da zaɓukan tsakiyar wa’adin mulkin Amurka cikin ƙasa da wata guda, a ranar 3 ga watan Nuwamba.
Axios ta kuma ruwaito, wasu majiyoyin da ta bayyana a matsayin masu cikakken bayani kan lamarin, na cewa idan aka sake fara manyan hare-hare kan Iran, akwai yiwuwar su haɗa da kai hare-hare ta sama kan cibiyoyin makamashi, manyan kayayyakin more rayuwa da kuma wuraren da ke da alaƙa da shirin nukiliyar ƙasar.
'An kashe aƙalla mutum 30 a hare-hare a Ukraine'
Rahotanni daga Ukraine na cewa an kashe aƙalla mutum talatin a wani hari da aka kai kan motocin bas biyu a birnin Kramatorsk da ke gabashin ƙasar.
Hotunan da hukumomin yankin suka fitar sun nuna wata motar bas da ta ƙone ƙurmus, da kuma tarkace a kan hanya.
Shugaban yankin ya zargi Rasha da kai wa fararen hula hari da gangan, tare da karya ƙa’idojin duniya game da yaki.
Ya bayar da umarnin dakatar da zirga-zirgar motoci a Kramatorsk da birnin Sloviansk da ke kusa da yankin, yana mai cewa yanayin tsaro ya tabarbare.
A Kyiv, babban birnin Ukraine, an kuma bayar da rahoton mutuwar mutum uku a wasu hare-hare biyu na daban.
Mayaƙan Houthi sun ce sun harbo jirgi mara matuƙi na Saudiyya
Asalin hoton, Getty Images
MayaƘan Houthi na Yemen sun ce sun harbo wani jirgin leƙen asiri na Bayraktar Akinci da aka ƙera a Turkiyya, wanda suka ce na ƙasar Saudiyya ne. Sun bayyana cewa jirgin yana gudanar da "ayyukan ta'addanci" a sararin samaniyar lardin Taiz.
Kakakin rundunar sojin Houthi, Yahya Saree, ya ce an harbo jirgin ne ta amfani da "makaman da suka dace."
Ya kuma ce ƙungiyar ta yi amfani da makamai masu linzami masu dogon zango wajen kai hare-hare kan wuraren da dakarun da Saudiyya ke marawa baya suka taru a kusa da mashigar ruwan Bab al-Mandab.
Kakakin sojin na Houthi ya kuma sanar a baya cewa sun kai wani hari cikin nasara da makami mai linzami kan Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sarki Khalid da ke birnin Riyadh.
Wannan ne karo na uku a cikin wannan makon da ƙungiyar ta ɗauki alhakin kai hari kan filin jirgin saman.
A nata ɓangaren, Saudiyya ta ce mutum ɗaya ɗan ƙasar Sudan ya mutu, yayin da wasu mutum takwas suka jikkata sakamakon harin da aka kai kan filin jirgin saman.
Ana sa ran tattalin arzikin Najeriya zai riƙa haɓaka da aƙalla kashi 4.4 cikin ɗari a shekara daga yanzu zuwa shekarar 2028.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto na Reuters ta kalato daga bankin duniya, inda ta ƙara da cewa hauhawar farashi kuma za ta ci gaba da raguwa a hankali, sannan kuma talauci ya fara sauƙaƙa.
Sai dai rahoton ya ce wannan zai faru ne matuƙar gwamnati ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki tare da inganta ayyukan yi wa jama'a hidima, a cewar Bankin Duniya a ranar Alhamis.
Mutum ɗaya ya mutu, biyu sun jikkata a harin wuƙa a Poland
An sake samun
wani harin wuka a makaranta a Poland, karo na biyu cikin kwana biyu.
Wani tsohon
dalibin makarantar firamare a kauyen Leszczydol-Nowiny, kusa da Warsaw dan
shekara 15 ne ya daba wa wata ma'aikaciyar makarantar wuka har ta mutu, tare da
jikkata wasu mutum biyu.
Bayan ya kai wa
ma'aikaciyar mai shekara 37 hari, yaron ya kuma daba wa wani malami da shugaban
makarantar wuka, kafin su samu nasarar fin ƙarfinsa.
A ranar Laraba
kuma, an kama wani dalibi dan shekara 19 bayan wani hari a wata makaranta a Ostroleka,
arewacin babban birnin kasar.
An wani lamarin
da ya faru kuma, an tsare wani yaro dan shekara 17 wanda ya yi magana kan
shirinsa na aikata "wani abu mai hatsari a harabar makaranta".
An gano wukake biyu a cikin jakarsa.
An kashe 'sojoji 12' a harin ƴanbindiga a Borno da Zamfara
Asalin hoton, TWITTER/@HQNIGERIANARMY
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani babban hari da mayaƙan ISWAP suka kai kan sansanin soji a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, inda ta ce ta kashe aƙalla mayaƙa 25.
Sojojin sun ce mayaƙan sun kai harin ne da yawansu daga ɓangarori huɗu a ranar Laraba. Dakaru tare da taimakon hare-hare ta sama, sun fatattake su, ko da yake wasu daga cikin mayaƙan sun tsere.
Rundunar ta kuma ce wasu daga cikin dakarunta sun mutu a harin, amma ba ta bayyana adadinsu ba.
Rundunar ta ce wasu ƴanbindiga a kan babura
sun kai farmaki kan al'ummomi a Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin
Najeriya.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa da farko ƴanbindigar
sun kai hari kan wani sansanin soji a Bindin, yankin da ake haƙar zinare, inda
suka kashe sojoji 12 kafin su nufi garuruwan Bindin da Gobirawar Chali da
ke maƙwabtaka.
Rundunar sojin Najeriya ta ƙi cewa komai game da lamarin lokacin da BBC ta
tuntuɓe ta, yayin da gwamnatin jihar ta ce za ta yi jawabi idan ta samu karin
bayanai.
Har yanzu ba a
tabbatar da adadin mutanen da suka mutu a harin na Zamfara da aka kai ranar
Litinin ba, duk da cewa mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa fararen hula fiye da 25 ne
suka mutu, yayin da wasu rahotannin suka ce adadin waɗanda suka mutu, ciki har
da masu haƙar ma'adinai, ya haura 100. BBC ba ta samu tabbatar da
waɗannan alƙaluma ba.
Ba a samu labarin hare-haren ba sai bayan wasu kwanaki
saboda matsalar sadarwa a yankin. Mazauna
yankin sun ce sau da yawa ana samun katsewar sadarwa yayin hare-hare saboda
kamfanonin sadarwa ba sa iya zuwa yankunan cikin aminci domin gyara ko kula da
turakun sadarwa.
Sun kuma ce
tashin hankalin na baya-bayan nan ya zo sakamakon rushewar wata yarjejeniyar
zaman lafiya da kungiyoyin 'yan bindiga a yankin.
Jihar Zamfara ta
shafe shekaru tana fama da hare-haren. A baya, wasu al'ummomin jihar sun yi
kokarin cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin, amma kokarin bai samar
da dawwamammen tsaro ba.
Shin sulhun Sanata Barau da Abba Bichi zai ɗore?
Asalin hoton, Sanusi Bature D-Tofa/Facebook
A wani mataki da masu sa ido kan siyasar Kano ke ganin zai iya rage zaman ɗar-ɗar da ya mamaye wasu sassan jam'iyyar APC a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci sulhun siyasa tsakanin Sanata Barau I. Jibrin, da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bichi Abubakar Kabir Bichi.
Sulhun ya zo ne a daidai lokacin da lissafin siyasar shekarar 2027 ke ƙara jan hankali, inda manyan jam'iyyun siyasa ke yunƙurin haɗa kan shugabanninsu da magoya bayansu domin fuskantar zaɓe mai zuwa.
Taron sulhun wanda ya gudana a Abuja a ranar Laraba, mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature ya ce shugabannin biyu sun samu damar tattauna saɓanin da ke tsakaninsu, tare da duba hanyoyin da za su yi aiki tare domin ci gaban jam'iyyar APC a Kano da kuma ƙasa baki ɗaya.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci Sanata Barau da Abba Bichi da magoya bayansu da su ajiye duk wani saɓani a gefe, inda ya jaddada cewa nasarar APC a matakin ƙasa da jiha ba za ta samu ba sai an samu haɗin kai, fahimtar juna da sadaukarwa daga kowa.
Ya ce yayin da ake shirin babban zaɓen shekarar 2027, wajibi ne shugabannin jam'iyyar su haɗa kai domin tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin Kano da kuma dukkan ƴan takarar APC.
Kuna iya samun ƙarin bayani kan wannan labarin idan kuka latsa nan.
Mutum 33 sun mutu a harin da Rasha ta kai Ukraine
Asalin hoton, Prosecutor General's Office
Jami'an ceto sun ce mutum 33 sun mutu sakamakon wani harin
Rasha kan wata motar bas a birnin Kramatorsk da ke gabashin Ukraine.
Hotunan da hukumomin yankin suka fitar sun nuna yadda motar
bas din ta kone, yayin da tarkace suka bazu a kan titin.
Gwamnan yankin ya zargi Rasha da kai wa fararen hula hari da
gangan. Ya bayar da umarnin dakatar da zirga-zirgar motocin haya a Kramatorsk
da birnin Sloviansk da ke kusa, saboda abin da ya bayyana a matsayin
tabarbarewar yanayin tsaro.
A Kyiv, babban birnin Ukraine, an bayar da rahoton mutuwar
mutum uku a wasu hare-hare biyu da aka kai lokuta daban-daban.
An kama yaron da ya ƙona gidan babansa har mutum 4 suka mutu
Asalin hoton, Yobe Police Command
Bayanan hoto, Kwamishinan ƴansandan jihar Yobe
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta kama wani
yaro dan shekara 13 bisa zarginsa da cinna wa wani gida wuta, lamarin da ya
yi sanadin mutuwar kishiyoyin mahaifiyarsa biyu da kannensa maza biyu a Rugan
Badali, karamar hukumar Karasuwa da ke jihar.
Tun da farko an zargi yaron da satar kaza, lamarin da ya sa mahaifinsa ya yi masa duka.
A wata hira da gidan
Talabijin na Channels Television, yaron ya amsa cewa shi ne ya cinna wutar,
yana mai cewa ya aikata hakan ne saboda fushin dukan da mahaifinsa ya yi masa.
Yaron ya ce ya
dauki daya daga cikin kajin domin ya sayar, amma mutane suka sanar da
mahaifinsa saboda karancin shekarunsa, wanda daga bisani ya yi masa duka. Ya
ce washegari ya sayi ashana ta naira 50 a unguwarsu, sannan ya cinna wa gidan
wuta a lokacin da matan mahaifinsa biyu da kannensa biyu ke barci.
Ya ce bayan da wutar ta kama gidan, ya yi ihu domin neman
taimako, inda mutane suka zo kokarin ceto wadanda ke ciki. Sai dai bai bayyana
cewa shi ne ya cinna wutar ba sai bayan kwana uku, kafin daga bisani 'yan sanda
su kama shi tare da kai shi Damaturu.
Da yake gabatar da yaron tare da mahaifinsa, Abubakar Idi,
kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Yusuf Adamu-Ali, ya ce duk da cewa
wanda ake zargin karamin yaro ne, ba za a kyale shi kawai ba, domin matakin ya
zama darasi ga sauran yara da ka iya aikata irin wannan laifi.
Ya kuma bayyana damuwa kan irin wadannan abubuwa, musamman a
daidai lokacin da jihar ke farfadowa daga matsalolin da rikicin Boko Haram ya
haifar.
Abin da ya sa jirgin soja ya yi saukar gaggawa a Benue - Sojoji
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce wani jirgin helikwafta
da aka gani yana sauka a wata gona a Jihar Benue yana dawowa ne daga wani
samame kan mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutane.
Wasu hotuna da ba a tabbatar da sahihancinsu ba da suka
bayyana a intanet sun nuna jirgin helikwaftan na soja a cikin wata gona, inda
rahotannin farko suka ce ya yi saukar gaggawa.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar yau Alhamis, Rundunar
Sojin Saman ta ce jirgin ya sauka ne don kauce wa hadari a wani wuri mai
tazarar kusan mil 10 daga sansaninsa, bayan kammala wani samame.
Rundunar ta ce jirgin helikwaftan ya bai wa sojojin kasa
taimako ta sama yayin wani farmaki kan mutanen da ake zargi da yin garkuwa da
mutane a Ogbadigbo, kusa da iyakar jihohin Enugu da Benue.
A cewar rundunar, samamen ya tarwatsa kungiyar da ake zargi
da aikata laifukan, tare da taimaka wa sojojin kasa wajen ci gaba da kutsawa
yankin.
Rundunar Sojin Saman ta ce matukin jirgin ya yi saukar
gaggawar ne a matsayin matakin kariya, bisa ka'idojin tsaro da ake bi bayan
kammala samame.
Sanarwar ta ce jirgin helikwaftan ya koma sansaninsa sannan rundunar
ba ta bayar da rahoton jikkatar kowa ko lalacewar jirgin ba.
Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da
kasancewa babbar matsalar tsaro a Najeriya, musamman a arewacin kasar.
A tsakanin Yulin 2025 da Yunin 2026, an bayar da rahoton
sace mutum 7,825 a hare-hare 1,411, a cewar SBM Intelligence, wata kungiyar
nazarin harkokin tsaro da ke Legas.
Jihar Benue da ke
tsakiyar Najeriya ta shafe shekaru tana fama da tashe-tashen hankula da suka
shafi kungiyoyi masu dauke da makamai, rikicin manoma da makiyaya,
rikice-rikicen tsakanin al'ummomi da kuma garkuwa da mutane.
Tsakanin Janairun
2024 da Agustan 2025, ACLED ta tattara bayanan afkuwar matsalolin tsaro 406 da
suka yi sanadin mutuwar mutum 1,338 a jihar.
Har ila yau, tashe-tashen hankulan sun tilasta wa dubban
daruruwan mutane barin muhallansu.
Mun lalata jiragen yaƙin Amurka 81 - Iran
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce
hakikanin barnar da aka yi wa kayan aikin sojin Amurka ta fi yawan da aka sanar
a hukumance.
A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta na X, ya ce:
“A watan Mayu, Majalisar Dokokin Amurka ta amince cewa dakarun Iran sun lalata
jiragen yakin Amurka 42. Yanzu adadin ya kai 81.”
Araghchi ya ci gaba da cewa: “Ina hujjar? Rundunar Sojin
Amurka da ke kula da yankin Gabas ta Tsakiya, CENTCOM, ba ta bari ko da sanata
daga Majalisar Dokokin Amurka ya ziyarci sansanonin da take ikirarin cewa komai
yana tafiya yadda ya kamata domin ya duba su ba.”
A sakon nasa,
Abbas Araghchi ya kara da cewa ba za a iya ci gaba da “yaudarar”
mutane kan wannan batu har abada ba.