Ana neman mutum 150 a cikin shari’ar “Trustees”
Ma’aikatar shari’a ta Iran ta ce ana neman mutum 150 da kuma kamfanoni ko hukumomi 25 dangane da wata shari’a da aka fi sani da “Trustees”, wadda ta shafi sayar da man Iran ta hanyoyin kauce wa takunkuman ƙasa da ƙasa.
Kakakin ma’aikatar shari’a ta Iran, Ali Kazemi, ya bayyana a wani taron manema labarai na mako-mako cewa wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma sun ba da haɗin kai wajen binciken. Ya ce an ɗauki matakai domin dawo da waɗanda ke wajen ƙasar, ciki har da: Fitar da jan sanarwar neman kama mutum (Red Notice) ta hannun ‘yan sandan ƙasa da ƙasa (Interpol). Neman mika waɗanda ake zargi ga Iran ta hanyoyin shari’a na ƙasa da ƙasa. Kwace kadarorin waɗanda ake tuhuma.
A tsarin doka, “trustees” su ne mutane ko hukumomi da ake yi wa rijista a matsayin masu mallakar wasu kadarori, amma a zahiri suna riƙe kadarorin ne a madadin waɗanda ainihin suka mallake su.
Iran ta fara amfani da wannan hanya domin kauce wa takunkumi, musamman bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA sannan ta sake kakaba takunkumi kan man fetur da harkokin bankunan Iran.
Kimanin shekara guda da ta gabata, jaridar Sharq ta wallafa wani rahoto inda ta yi hasashen cewa kusan mutane ko hukumomi 100 da suka yi aiki a matsayin “trustees” sun tara kusan dala biliyan 50 na ribar da aka samu ta hanyar abin da ta kira cin hanci da rashawa na tsari, cikin fiye da shekara goma.