Fashewar bam ta yi ajalin aƙalla mutum 11 a Pakistan
Ƴansanda a arewa maso yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 ne suka mutu, yayin da wasu 30 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a yankin Dera Ismail Khan.
Ƴansandan sun ce wata mota ɗauke da abubuwan fashewa ta yi karo da wata mashigar binciken jami’an tsaro.
Daga cikin jami’an tsaron da aka kashe har da mata biyu da wani yaro. Ya zuwa yanzu, babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.
Mayaƙan Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP) sun taɓa kai irin waɗannan hare-haren bam kan jami’an tsaro a baya.
Lamarin ya faru ne kwana biyu bayan da Pakistan ta sanar da cewa ta kai hare-haren sama kan wasu mayaka da take zargi da ke Afghanistan, waɗanda ke kai hari kan dakarunta a yankunan da ke kan iyaka.