Za a gurfanar da 'ƴan Boko Haram' 400 a gaban kotu
Aƙalla ƴan Boko Haram 400 ne za a gurfanar a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a yau kan zargin aikata laifukan ta’addanci, a ɗaya daga cikin manyan shari’o’in ta'addanci da aka taɓa yi a Najeriya.
Shari’ar na nuni da wani muhimmin mataki a ƙoƙarin gwamnati na ƙarfafa ɗaukar alhaki da kuma magance matsalar tsaro da ƙasar ke fama da ita tsawon lokaci.
Waɗanda ake tuhuma na fuskantar zarge-zarge daban-daban da suka haɗa da kai hare-hare da tallafawa ayyukan ƙugiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da ta'addaci.
Wannan na zuwa ne bayan wata babbar shari’a a watan Afrilun 2026, inda aka gurfanar da sama da mutane 500 kan zargin aikata laifukan ta'addanci kuma an samu kusan 400 da laifi.
Mahukunta sun ce wannan mataki na da nufin kammala sauran shari’o’i da kuma gurfanar da ƙarin waɗanda ake zargi domin a hukunta su.
Najeriya na ci gaba da fama da rikicin ta’addanci na tsawon shekaru 16, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da miliyan biyu da muhallansu, yayin da matsalar garkuwa da mutane ke ci gaba da ƙaruwa a sassa daban-daban na ƙasar.