Birtaniya, Faransa, Jamus da Italiya sun yi maraba da yarjejeniyar Iran da Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Birtaniya, da Faransa, da Jamus da Italiya sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa inda suka yi maraba da yarjejeniyar, suna masu cewa sake buɗe mashigar Hormuz abu ne mai matuƙar muhimmanci.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa bai kamata Iran ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba.
Kasashen huɗu na Turai sun ce a shirye suke su ɗage takunkuman da suka sanya wa Iran din idan har ta ɗauki matakai bayyanannu da za su ba da damar bibiyar shirinta na makamashin nukiliya don tabbatar da cewa ba ta sauka daga layi ba.















