Yadda batun gyaran dokar zaben Najeriya ke janyo ce-ce-ku-ce gabanin zaben 2027

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

'Yan siyasa, ƙungiyoyin farar hula da masana harkokin mulki na ci gaba da kira da a yi gyare-gyare a tsarin zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027, suna masu cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa gaskiya, da kuma ingancin zabe, da ita kanta dimokuraɗiyyar.

Wannan kira na ƙaruwa ne yayin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da nazarin darussan da aka koya daga zaɓukan baya, waɗanda wasu daga cikinsu suka haifar da ce-ce-ku-ce kan rajistar masu kaɗa ƙuri'a, da tattara sakamakon zaɓe, da kuɗaɗen kamfen da kuma yadda ita kanta hukumar zaben kasar INEC ke gudanar da ayyukanta.

A watan Fabrairu ne dai shugaban Najeriyar Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar zaɓen ƙasar ta 2026, wanda aka yi wa gyara.

Sai dai duk da haka jam'iyyun adawa na nuna buƙatar yin karin wasu gyare-gyare, domin a cewarsu, na baya da aka yi ba su magance dukkan matsalolin da ake fama da su ba.

Wasu fitattun 'yan siyasa, ciki har da Peter Obi, sun ce akwai bukatar a fara aiwatar da gyare-gyaren tsarin zaɓe tun da wuri domin kauce wa cece-kuce a lokacin gudanar da zaɓe. Sun bayyana cewa amincewar jama'a da sakamakon zaɓe na da alaƙa kai tsaye da yadda aka tsara dokoki da kuma yadda ake aiwatar da su.

A cewar Dr Tanko Yunusa, wani na hannun daman Peter Obi, dole ne gyaran da za a yi ya tanadi wani tsari da za a tabbatar da sahihancin takardun makarantar 'yan takara da sahihancinsu, domin a cewarsu ana samun wadanda ba su da shaidar karatu na ainihi suna shiga takarar kujeru daban daban ciki har da na shugaban kasa.

Kana ya ce amfani da fasahar zamani wajen rajistar masu zaɓe, da tantance masu kaɗa ƙuri'a da kuma sanar da sakamakon zaɓe na da matukar muhimmanci ga tsarin zabe.

''Dole ne su fito su yi muhawa mu ji me suke son su yi wa Najeriya domin haka ake yi a duk duniya, sannan ya kamata a ce yawan wadanda suke fitowa zabe ya zarce wanda ake gani a yanzu, sannan dole ne a ƙarfafa 'yancin kai na hukumomin zaɓe tare da tabbatar da cewa ba su fuskantar tasirin siyasa daga kowanne ɓangare, hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa an gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci'' inji shi

Ya ce amincewar jama'a da hukumomin zaɓe na daga cikin manyan abubuwan da ke tabbatar da zaman lafiya bayan kammala zaɓe, kana duk wani gyara da za a yi tun da wuri zai ba da damar wayar da kan jama'a, horas da jami'an zaɓe da kuma gwada sabbin tsare-tsare kafin ranar zaɓe.

Ya ci gaba da cewa ''Inganta tsarin rajistar masu zaɓe da kuma aika sakamakon zaɓe ta Internet zai ƙara inganci da rage yiwuwar samun kura-kurai ko zarge-zargen maguɗi''

Har ila yau, batun kuɗaɗen kamfen ya kasance cikin muhimman batutuwan da ake son a sake dubawa. Masu fafutuka na ganin ƙara tsaurara dokokin bayyana hanyoyin samun kuɗaɗen kamfen da yadda ake kashe su, domin tabbatar da adalci tsakanin masu neman muƙamai.

A nata ɓangaren, jam'iyyar APC ta amince cewa akwai buƙatar ci gaba da nazarin tsarin zaɓe, amma ta jaddada cewa duk wani gyara dole ne ya bi tanade-tanaden kundin tsarin mulki da sauran dokokin ƙasa.

Sai dai duk da cewa mutane da dama sun amince da muhimmancin inganta tsarin zaɓe, har yanzu ba a cimma matsaya guda kan irin gyare-gyaren da ya kamata a bai wa fifiko ba.

Yayin da wasu ke kira da a yi manyan sauye-sauye a dokokin zaɓe, wasu kuwa na ganin cewa dokokin da ake da su sun isa, sai dai a tabbatar an aiwatar da su yadda ya kamata.

Masu sa ido kan harkokin siyasa sun ce watanni masu zuwa za su kasance masu muhimmanci wajen fayyace makomar gyare-gyaren da ake tattaunawa a kai. Yayin da shirye-shiryen zaɓen 2027 ke kara matsowa, ana ci gaba da matsa lamba ga 'yan majalisa, hukumomin zaɓe da shugabannin siyasa su bayyana matakan da za a ɗauka.

Ga masu goyon bayan gyaran tsarin, batun ya wuce sauya dokoki kawai. Sun ce ƙarfafa tsarin zaɓe na da muhimmanci wajen kare dimokuraɗiyya, ƙarfafa amincewar jama'a da kuma tabbatar da cewa sakamakon zaɓe yana nuna ra'ayin masu kaɗa ƙuri'a.

Yayin da tattaunawar ke ci gaba, idanu za su kasance a kan masu yanke shawara da hukumomin zaɓe domin ganin ko za a iya cimma matsaya kan gyare-gyaren da za su taimaka wajen gudanar da sahihin zaɓe mai gaskiya da karɓuwa a shekarar 2027.