Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare a Lebanon
Duk da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Iran da Amurka da ta ƙunshi kawo ƙarshen rikicin Isra'ila da Lebanon, ana ci gaba da musayar wuta tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah da ke cikin Labanon.
Jami'an kiwon lafiya na ƙasar Lebanon sun sanar da cewa hare-haren da Isra'ila ta kai a kudancin ƙasar ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum 18.
Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa ta kashe mayaƙan Hezbollah da dama a hare-haren da ta kai kan wurare 80 a faɗin ƙasar.
Har ila yau, a cewar sojojin Isra'ila, kwamandan bataliya ta 52 masu sulke tare da sojojinsa uku sun mutu a musayar wuta da ƙungiyar Hezbollah.