Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Su wane ne manyan ƴan takarar gwamnan jihar Ekiti?
Zaɓen gwamnan jihar Ekiti zai gudana ne a ranar Asabar 20 ga watan Yunin 2026 a ƙananan hukumomi 16 na jihar.
Za a fafata ne tsakanin gwamna mai ci Biodun Oyebanji na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da wasu ƴan takara 11.
Dukkanin jam'iyyun siyasar da suka tsayar da ƴan takara a zaɓen sun gudanar da zaɓen fidda gwani tsakanin ranakun 20 ga Oktoba zuwa 10 ga Nuwamba 2025.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da jerin sunayen ƴan takara gabanin zaɓen.
INEC ta fara fitar da sunayen ƴan takara 12, amma daga baya ɗan takarar jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM) Joseph Anifowose ya janye daga takarar inda ya marawa gwamna mai ci Biodun Oyebanji baya.
Wani muhimmin abin da ya ja hanklai gabannin zaɓen shi ne INEC ta cire sunan ɗan takarar jam'iyyar PDP, Wole Oluyede saboda rikicin shugabanci da batutuwan da suka shafi shari'a da suka dabaibaye jam'iyyar a matakin ƙasa.
Jihar Ekiti ta na da masu kaɗa ƙuri'a 1,059,360. Adadin ya ƙaru da 66,000 idan aka kwatanta da yawan waɗanda suka yi rajista a zaɓen da ya gabata.
Biodun Oyebanji - APC
Biodun Abayomi Oyebanji shi ne ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC). An haife shi a shekarar 1967 a yankin Ikogosi Ekiti.
Biodun ƙwararre ne a fannin gudanarwa kuma gawurtaccen ɗan siyasa.
Ya karanci kimiyyar siyasa a jami'ar jihar Ekiti sannan ya samu digiri na biyu a fannin kimiyyar siyasa daga jami'ar Ibadan.
Yayi aiki a matsayin shugaban ma'aikata sannan kuma a matsayin Sakatare a ƙarƙashin tsohon gwamna Kayode Fayemi. Haka kuma ya riƙe wasu sauran muƙaman siyasa a gwamnatin jihar.
A 2022, ya lashe zaɓen gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC, yana kuma neman wa'adi na biyu zaɓen gwamnan na mako mai zuwa.
Oluwadare Bejide - ADC
Oluwadare Bejide shi ne ɗan takarar jamm'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaɓe mai zuwa.
An haife shi ne a watan Agusta 1959 a yankin mazaɓar Ekiti ta kudu.
Ya halarci Jami'ar Ife (OAU) sannan kuma lauya ne wanda aka rabntar da shi a 1985.
Daga baya ya halarci Jami'ar Obafemi Awolowo tare da yin Digiri na biyu a fannin Shari'ar sufurin jiragen ruwa da na Sama.
Bejide ma'aikacin gwamnati ne lauya kuma ɗan siyasa wanda ya sami gogewaa fannoni daban-daban. Ya kuma kasance jami'in diflomasiyya wanda taɓa zama jakadan Najeriya a Kanada.
A fagen siyasa, ya riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar Ekiti daga 2007 zuwa 2010.
Ya yi takaran kujerun siyasa da dama amma bai taɓa yin nasara ba.
Oyebanji Olajuyin - Labour Party
Oyebanji Olajuyin shi ne ya zama ɗan takarar gwamna na jam'iyyar Labour, bayan matakan sasanci da jam'iyyar ta ɗauka.
Ya fito a matsayin ɗan takara ta hanyar tsarin yarjejeniya yayin zaɓukan fidda gwani na jam'iyyar.
Olajuyin likita ne, malami kuma ɗan siyasa daga yankin Ikere Ekiti.
Ya kasance farfesa a aikin tiyatar kunne da makogwaro, kuma mai bincike a fannin ilimin likitancin sassan jiki a asibitin koyarwa na jami'ar Jihar Ekiti, Ado - Ekiti. Kuma ya wallafa littattafai sama da 50.
Ya yi iƙirarin cewa idan har ya yi nasarar zama gwamna, zai gudanar da mulkinsa cikin adalaci bin doka da sanin ya kamata.
Oluwole Oluyede - PDP
Oluwole Oluyede ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamna da za a gudanar a jihar Ekiti a ƙarshen mako.
An haife shi a watan Yuni 1964 a Ado Ekiti.
Oluyede halarci Jami'ar Ilorin, kuma ya kuma yi zaman sanin makama aikin likitanci a Jami'ar Upstate, Syracuse, ta Jihar New York inda ya samu zama mamba a hukumar kula da lafiya ta Kanada.
Yana aiki a matsayin ƙwararren likita a Najeriya da Kanada da kuma Ostiraliya. kuma shi ne shugaban kamfanin Mayokun Pty Limited da ke Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.
Oluyede ya yi takarar gwamna a zaɓen 2022 ƙarƙashin jami'yyar ADC, amma bai yi nasara ba