'Ba ciwon asma ne ya yi ajalin ƴarmu ba'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

An ƙaddamar da bincike akan mutuwar wata ɗaliba a makarantar sakandire ta St. Louis bayan da iyayen ta suka tabbatar da cewa ƴarsu ba ta da ciwon da ake zargi ya yi ajalinta.

Ƙorafin da iyalan marigayiyar suka shigar gaban ƴan sanda a jihar Kano ne yasa aka ƙaddamar da bincike don gano haƙiƙanin gaskiyar abubuwan da suka faru game da rasuwar yariyar.

Mahafiyar yarinyar ta shaida wa BBC cewa, suna zargin an hukuntata ne ta hanyar bulala da kuma tsugunnar da ita na tsawon lokaci ne ya yi sanadin rabata da duniya.

Ta ce," Koda aka zo mini da labarin mutuwarta abin da aka ce mini shi ne an sanyata (Kneel down) wato tsugunno akan gwiwarta na tsawon lokaci, shi ne ta yanke jiki ta faɗi, daga nan kuma ta rasu."

"To bayan da malaman makarantar suka zo mana ta'aziyya sai abin da suka faɗa ya bambanta da abin da aka faɗa mana da farko, inda su suka ce wai ta makara sallah ne shi ne aka hukuntata kuma wai ashe tana da asma shi ne ta yanke jiki ta faɗi." In ji mahaifiyar yarinyar.

Ta ce," Da muka je asibiti bayan sanar damu cewa bata da lafiya an shaida mana cewa dama ko da aka kai ta asibitin daga makarantar a mace aka kai ta."

Mahaifiyar dalibar ta ce, " A gaskiya ni ƴata ba ta da ciwon asma hasali ma ni ban san ko da maganin ciwon guda ba, yarinya lafiyarta ƙalau don ko zazzabi mai zafi bata yi ballantana ciwon zuciya."

"To ace kawai don an Sanya mutum (knell down) tsugunno akan gwiwa sai ya faɗi ya mutu, wannan ba abu ba ne da hankali zai yarda da shi ba."

Ta ce, " Mu fa abin da waɗansu a makarantar da aka yi abin a gabansu suka shaida mana shi ne tsugunno akan gwiwarta aka sanyata a rana na tsawon lokaci, domin da farko an sanyata shara ta ce ba zata yi ba don tana da lalurar asma, to bata da wannan ciwon, ba mamaki ta faɗi hakan ne don ta kare kanta daga yin sharar, to shi ne aka ce ta tsugunna akan gwiwarta a rana, a nan ne kuma saboda daɗewar da ta yi ta yanke jiki ta faɗi."

"Waɗanda suka fadi wannan magana ganau ne ƴan makarantar ne, don haka yanzu mu mun kai ƙara wajen jami'an tsaro, kuma an fara bincike." In ji mahaifiyar yarinyar.

Rundunar ƴan sandan jihar ta Kano dai, ta sanar da kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike akan musabbabin mutuwar ɗalibar.

Rasuwar yarinyar ƴar shekara goma sha huɗu ta haifar da ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta inda ake ta yaɗa bayanai mabanbanta game da musabbabin rasuwar.

Tuni dai kwamishinan ƴan sandan Kano CP Adamu Ibrahim Bakori, ya ƙaddamar da bincike ƙarƙashin jagorancin DCP Shehu Idris tare da haɗin gwiwar jami'an ma'aikatar shari'a ta jihar Kano.

Duk ƙoƙarin jin ɓangaren mahukuntar makarantar sakandire ta St. Louis da BBC ta yi ya ci tura.