Kotu ta ɗaure iyayen ɗan bindigan da ya harbe yara tara a Serbia

Asalin hoton, Slobodan Maricic/BBC Serbian
An ɗaure iyayen wani yaro da ya harbe yara tara da wani mai gadi a wata makarantar firamare a Sabiya, a wani shari'a da aka sake yi a birnin Belgrade.
Yaron yana da shekar 13 da haihuwa a lokacin da ya harbe wasu yara ƴan mata bakwai, da namiji ɗaya da wani mai gadi a makarantar Vladislav Ribnikar da ke Belgrade a shekarar 2023.
Wata yarinya kuma ta mutu daga baya a asibiti.
Wanda ya yi harbin ya kasance a ƙarƙashin shekarun da za a kama shi da aikata laifuka kuma an tura shi cibiyar kula da masu lallurar ƙwaƙwalwa, amma an zargi iyayensa Vladimir da Miljana Kecmanović da rashin kulawa da cin zarafin ƙaramin yaro, yayin da ake zargin mahaifinsa da aikata babban laifi da ya shafi lafiyar jama'a.
An yanke wa Kecmanović hukuncin ɗaurin shekara 14 da watanni shida a gidan yari ranar Alhamis, matarsa kuma an daure ta na tsawon shekara biyu da wata 11.
Ba kasafai ne ake samun harin bindiga a ƙasar Serbia ba, shi ya sa ƙasar ta kaɗu a lokacin da aka kai harin Belgrade a ranar 3 ga watan Mayun 2023. Yaron ya dauko bindigogi guda biyu daga ma'ajiyar mahaifinsa, ya sanya su a cikin jakarsa ya tafi makaranta, inda ya buɗe wuta a cikin zauren makarantar da kuma wani aji.

















