Taiz da wasu
lardunan Yemen na fama da matsalar ƙarancin gas na girki, inda jama'a da dama
ke dandazo a gidajen sayar da gas.
Lamarin na nuna
irin wahalar da jama'a ke fuskanta a kullum sakamakon ƙarancin gas ɗin.
Jama'a na yin dogayen
layuka domin samun gas, inda wasu ke kafa layi tun da sanyin safiya.
Ana kuma samun
turmutsitsi sakamakon yawan mutanen da ke neman gas.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Jirgi mai saukar ungulu ya faɗi a Najeriya
Asalin hoton, Lucky Orimisan/FB
Ƴan sanda a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya sun ce wani jirgi mai saukar ungulu ya yi hatsari a Igbokoda, hedikwatar ƙaramar hukumar Ilaje.
Har yanzu ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba, ko kuma ko an samu waɗanda suka mutu ko suka jikkata.
Hatsarin ya haifar da firgici a yankin da ke gabar teku, yayin da aka tura jami’an agajin gaggawa da na tsaro zuwa yankin.
Wani mazaunin yankin, Olorunlola Oluwafemi, ya shaida wa BBC cewa ana ruwan sama kamar da bakin ƙwarya lokacin da mutanen yankin suka ji “ƙara mai ƙarfi kamar tsawa.”
Ya ce bayan sun fahimci cewa ba tsawa ba ce, “mun fita waje inda muka gano cewa kamar jirgin sama ne.”
Ya ƙara da cewa hayaki na tashi daga wurin da jirgin ya faɗi.
A cewar Oluwafemi, jirgin ya yi hatsarin ne kusa da wani daji da ke makwabtaka da sansanin rundunar sojin ruwan Najeriya na FOB a Igbokoda.
Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun tura jami’ai zuwa yankin, inda ake ci gaba da aikin nema da ceto.
Asalin hoton, Getty Images
Yemen ta ƙaddamar da hari don ƙwato Sana'a daga hannun Houthi
Asalin hoton, AFP via Getty Images
Dakarun gwamnatin Yemen sun ce sun fara ƙaddamar da gagarumin farmaki kan babban birnin ƙasar, Sanaa, da nufin ƙwato birnin daga hannun ƙungiyar Houthi da Iran ke marawa baya.
Wani gidan talabijin mai alaƙa da Houthi ya ruwaito cewa Saudiyya ta kai hari kan Sanaa.
Hakan na zuwa ne bayan gamayyar ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ta kai hare-hare kan ɗaruruwan wurare , a wani yunƙuri na dakile mayaƙan Houthi daga ci gaba da nausawa wasu yankunan.
Jami'an Yemen sun ce dakarunsu sun ƙwace wasu muhimman wurare a mashigar Bab el-Mandeb, bayan sun fatattaki mayaƙan Houthi daga wannan muhimmiyar mashigar ruwa da ke tekun Maliya.
An kashe aƙalla mutum 28 duk da dokar hana fita a Filato
An kashe aƙalla
mutum 28 a sabbin hare-haren da aka kai a ƙananan hukumomi uku na jihar Filato,
duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta ƙaƙaba a ranar 21 ga Satumba domin
dawo da zaman lafiya da hana ci gaba da asarar rayuka.
Yankunan da abin
ya shafa ciki har da Mangu, Bokkos da Barkin Ladi, sun fuskanci hare-hare
akai-akai a 'yan makonnin nan.
Lamarin ya jefa
dubban mazauna cikin fargaba, ya kuma kawo cikas ga ayyukan noma da kiwo, tare
da tilasta wa mutane da dama barin harkokin samun abincinsu.
Jaridar Daily
Trust ta ruwaito cewa a sabon harin da aka kai jiya, an kashe mutum biyu tare
da jikkata wasu shida bayan an kai hari kan makiyaya da ke cikin motar ɗaukar
kaya a kusa da wani gidan mai da ke Bukuru, a ƙaramar hukumar Jos South ta
jihar Filato.
Harin ya faru ne
ƙasa da makonni biyu bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari kan makiyaya a kusa
da garin Kassa da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi, inda suka kashe mutum biyar
tare da jikkata mutum ɗaya.
Shugaban ƙungiyar
makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, wanda ya
tabbatar da faruwar lamarin a Jos, ya ce 'yan bindigar sun kai wa motar hari ne
da misalin ƙarfe 5:30 yayin da mutanen ke dawowa daga kasuwar shanu zuwa
ƙaramar hukumar Bassa.
Shugaban ya yi allah-wadai
da harin, tare da kira ga jami'an tsaro su gano waɗanda suka aikata shi tare da
gurfanar da su a gaban shari'a.
Yadda Kanawa ke murnar dawowar ruwan famfo
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don ganin yadda Kanawa ke murnar dawowar ruwan famfo
Wasu al’ummun jihar Kano na murnar samun ruwan famfo a karon farko bayan fiye da shekara 10 wanda gwamnati ta kashe kimanin naira biliyan 22 don samarwa.
Wasu daga cikin mutanen da ke murna sun bayyana mana farin cikinsu.
An rufe makarantu kusan 500 kan zanga-zangar ɗalibai a Faransa
Asalin hoton, Reuters
Faransa na fara
wani sabon makon karatu yayin da aka rufe makarantu kusan 500 sakamakon ci gaba da zanga-zangar da dalibai
ke yi.
Ministan Ilimi ya
bayyana cewa an dauki matakin rufe makarantun ne saboda dalilai na tsaro, inda
ya kara da cewa an kona ko kuma an yi mummunar barna a makarantu ashirin da hudu a cikin makonni
uku na zanga-zangar.
Daliban na cewa
rashin malamai, da tsawon lokacin karatu a makaranta, da kuma rashin kayan aiki
masu inganci na kawo cikas ga karatunsu.
Wannan yunkuri ya
samo asali ne daga wata makaranta a birnin Paris kafin daga bisani ya bazu zuwa
sassan kasar baki daya.
Ƴansanda sun gano sansanin da ake tsare da ƴan NYSC da aka sace
Asalin hoton, Getty Images
Yan sanda a jihar
Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun ce sun gano wani sansani da ake tsare
da aƙalla matasa 19 masu yi wa ƙasa hidima da ƴanbindiga suka sace a baya-bayan nan.
Kwamishinan ’yan
sandan jihar, Audu Bosso, ya ce jirage marasa matuƙa sun taimaka wajen gano
sansanin, amma jami’an tsaro ba su kai ga isa wajen ba saboda ana kyautata
zaton an dasa abubuwan fashewa a zagayen wajen.
Da yake magana da
manema labarai ranar Asabar, Bosso ya ce: “Jiya mun shiga daji, mun bi sawunsu
har zuwa wani wuri. Amma a
lokacin ba mu iya kutsawa zuwa wurin da bayananmu suka nuna mana cewa suna can
ba.”
Ya ce binciken da
aka yi da jirgi marar matuƙi ya tabbatar da inda sansanin yake.
“Jirgin marar
matuƙin ya nuna mana ainihin inda suke. Amma matsalar da muke fuskanta ita ce,
bisa bayanan sirrin da muke da su, an dasa abubuwan fashewa a sansanin,” in ji
Bosso.
Ya ce ana tura
motocin katapila da motocin yaƙi masu sulke yayin da ’yan sanda ke shirin
gudanar da aikin ceto mutanen.
Omotosho Adewale,
wanda ɗansa ke cikin waɗanda aka sace, ya shaida wa BBC cewa kuɗin fansar da
masu garkuwar ke nema sun fi ƙarfinsa.
Ya ce “Naira
miliyan 50 suke nema,”.
Ya ƙara da cewa “Don
Allah, duk abin da gwamnati za ta iya yi ta taimaka mani... Na samu damar rainon yaron nan ne kawai
saboda taimako da goyon bayan da na samu daga kowa,”.
Biyan kuɗin fansa
abu ne da ya saɓawa doka a Najeriya, kuma hukumomi sun sha gargaɗin iyalan waɗanda
aka sace kada su biya. Sai dai iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kan
fuskanci matsin lamba na biyan kuɗi domin a sako ’yan uwansu.
Ba a bayyana
takamaiman wurin da sansanin yake ba, kuma ’yan sanda ba su bayyana waɗanda ke
da alhakin sace mutanen ba.
Satar mutane
domin neman kuɗin fansa na ci gaba da kasancewa babbar matsalar tsaro a
Najeriya.
A kudu maso
gabashin ƙasar, an danganta wasu sace-sacen da aka yi a baya da ƙungiyoyin ƴan
aware, ciki har da IPOB. Sai dai hukumomi ba su danganta wannan satar da wata
ƙungiya ba.
Lamarin ya jawo
damuwa sosai, kasancewar sace mutane da yawa lokaci guda ba kasafai ake samun
irin sa a kudancin Najeriya ba kamar yadda ake samu a wasu sassan arewacin
ƙasar.
Waɗanda aka sace
sun taso ne daga Ibadan zuwa sansanin horas da masu yi wa ƙasa hidima a jihohin
Abia da Akwa Ibom, lokacin da ’yan bindiga suka kai wa motocin bas ɗinsu hari
kusa da Umunoha a jihar Imo a ranar Alhamis da ta gabata.
Mun kai hare-hare 1,122 kan sansanonin Houthi - Yemen
Asalin hoton, EPA
Wani mai magana da yawun dakarun da ke goyon bayan gwamnatin
Yemen ya ce sun kai hare-hare 1,122 kan wuraren mayaƙan Houthi, ciki har da
wuraren da aka girke manyan bindigogi, na'urorin harba rokoki da cibiyoyin
bayar da umarni.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin X, Majed Abdullah
Nazili ya ce an kai hare-haren ne ta hanyar amfani da jiragen yaƙi, jirage
marasa matuƙa, makamai masu linzami, rokoki, manyan bindigogi a lardunan Saada,
Jawf da Taez, da kuma yankunan gabar tekun Yemen.
Sanarwar ta kuma ce an kashe dakarun Houthi kusan 1,747 a
hare-haren.
Mutanen da Boko Haram ta kashe baya-bayan nan a Borno ya ƙaru zuwa 28
Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Najeriya na cewa adadin mutanen da aka kashe sakamakon wani hari da Boko Haram ta kai a makon nan ya ƙaru zuwa 28.
Boko Haram sun farwa mutanen ne lokacin da suka je yin ita ce.
Wannan ne harin baya-bayan nan da aka kai a jihar Borno da wasu sauran jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.
Tun da farko an bayar da rahoton kashe mutum 15 da tuni aka yi jana'izarsu ranar Alhamis a ƙauyen Marte sai dai an sake gano wasu gawawwaki 13 a ƙarshen mako.
Wata ƙungiya reshen IS da ke iƙirarin Jihadi tana da hannu a sace-sacen jama'a domin neman kuɗin fansa duk da tabbacin da gwamnatin ƙasar ke bayarwa cewa ana samun daidaito da kwanciyar hankali a yankin.
Abubuwa 10 da ke kashe aure a arewacin Najeriya - Malamai
Asalin hoton, Social Media/Multiple
A shekarun baya idan aka ji aure ya mutu a unguwa ko a gari akan shiga zulumi ko tambayar dalili bisa makomar miji ko matar ko 'ya'ya saboda rabuwar iyayensu.
Sai dai yanzu zamani ya zo da sauyi ta yadda a wasu lokutan mutuwar aure bai zamo wani babban abin jimami ba, inda ake samun ma'aurata 'yan ƙasa da shekaru 30 aurensu yake mutuwa, a wani lokacin ma fiye da mutuwa daya, wani abu da masu lura da al'amuran yau da kullum ke ganin akwai firgici a cikinsa.
Wata ƙididdiga ta Hukumar Hizba ta jihar Kano ta nuna cewar aƙalla gwamman aure ne ke mutuwa a wata guda, a jihar da tafi kowacce yawan al'umma a arewacin Najeriya.
Malam Aminu Daurawa ya ce wannan ƙididdigar ta iya hukumar Hizba ce wadda kuma su aikinsu ya fi ƙarfi a gyaran aure da sulhu ga ma'aikata.
Ya ce ba su da ƙididdigar kotu da ta ɓangaren fada, "kuma mafi yawan auren da ke mutuwa yana mutuwa ne a kotu".
Wannan ne ya sa BBC ta tuntubi wasu malamai kuma masana zamantakewar rayuwa, wadanda suka haɗa da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Farfewa Mansur Isa Yelwa da kuma Dakta Abdallah Usman Gadon Ƙaya.
Malaman uku sun yi ittifaƙin cewa dalilai 10 na janyo mutuwar aure ƙarƙashin rabe-rabe huɗu da suka hada da ta ɓngare miji da na ɓangren mata da na iyaye da 'yan uwa da kuma na al'umma.
Tsananin zafi na jefa masu juna biyu da jarirai cikin haɗari - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da batun
sauyin yanayi ya yi gargadin cewa yanayin tsananin zafi na sanya mata masu juna
biyu da jarirai cikin babban hadari.
Wakiliyar BBC ta ce a cewar Simon Stiell, ana ƙara danganta
tsananin zafi mai nasaba da sauyin yanayi
da matsalolin haihuwa kafin
lokaci, da haihuwar jaririai da suke zuwa babu rai, da kuma
matsalolin lafiya ga uwa.
Ana sa ran zai
sanar da wakilai a wani taron sauyin yanayi a Fiji cewa sakamakon wani sabon bincike
ya nuna cewa kusan kashi uku cikin huɗu na kwararru a fannin lafiyar mata masu
juna biyu sun bayar da rahoton karuwar matsalolin lafiya da ke faruwa sakamakon
tsananin zafi a cikin shekaru biyar da suka gabata.
Amurka ta janye jiragen yaƙinta daga sansanin sojin saman Birtaniya
Asalin hoton, Getty Images
Amurka ta janye
dukkan jiragen yakinta masu jefa bama-bamai daga wani sansanin sojin sama a
Ingila wanda aka yi zargin cewa an yi yunkurin kai wa hari.
Ma'aikatar Tsaron
Amurka Pentagon ba ta bayar da wani dalili na janyewar ba, amma wakilin BBC
ya ce yadda aka yi janyewar ta ba-zata ya nuna alamun cewa akwai wani yanayi
mai kama da fargaba a cikin lamarin.
Wakilin BBC ya ce Amurka ta yi amfani da sansanin RAF Fairford wajen gudanar da hare-haren bam
ta sama kan Iran ta hanyar amfani da jiragen B-1 da B-52, hare-haren da
gwamnatin Birtaniya ta bayyana a matsayin na kare kai.
A makon da ya
gabata, hukumomin Birtaniya sun ayyana wani babban lamari bayan sun tare wasu
motocin dakon kaya da ake ganin suna kan hanyarsu ce ta zuwa sansanin.
Zaben shugaban ƙasa a Brazil zai shiga zagaye na biyu
Asalin hoton, AFP
Zaɓen shugaban kasa a Brazil zai shiga zagaye na biyu, bayan
da aka kasa samun wanda ya samu rinjayen kuri'u tsakanin Shugaba Lula da Silva
da abokin hamayyarsa Flavio Bolsonaro.
Mista Bolsonaro, wanda dan tsohon shugaban kasa Jair
Bolsonaro ne da ke tsare a halin
yanzu, zai shiga zagayen na biyu, wanda za a gudanar nan da mako uku,
yana da tazarar da ba ta kai kashi biyu cikin dari ba a gaban abokin hamayyar nasa.
Wakiliyar BBC ta
ce Flávio Bolsonaro ya yi alkawarin yi wa mahaifinsa, da magoya bayansa da suka
kai hari kan gine-ginen gwamnati bayan shan kaye a zabe, afuwa daga hukuncin da
suke fuskanata a halin yanzu.
Shugaba Lula
dai ya bayyana sakamakon zaben a matsayin wanda ba a yi tsammaninsa ba, amma
ya kara da cewa a shriye ya ke ya tunkari zagaye na biyu.
Marabanku
Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa kai-tsaye, barkan mu
da safiyar wannan rana ta Litinin – tushen aiki.
Nabeela Mukhtar Uba ke fatan kasancewa da ku a wannan shafi,
domin kawo irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da
makwabtan ƙasashe.
Kuna iya tofa albarkacin bakinku kan labaran da muke
wallafawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook; X, Instagram, har ma da
Youtube.