KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman labarai dangane da irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na 03/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge da Abdullahi Bello Diginza

  1. Jirage shida sun wuce ta mashigar Hormuz a ranar Laraba

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bisa ga sabbin bayanan sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa na kamfanin Kepler, wanda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa, jiragen ruwa shida kacal ne suka bi ta mashigin Hormuz a ranar Laraba.

    Rahoton ya zo ne bayan da jiragen ruwa 11 suka ratsa mashigin Hormuz a ranar Talata, lamarin da ke nuna raguwar yawan jiragen da ke amfani da wannan muhimmin hanyar ruwa.

    A cewar bayanan, jiragen da suka bi ta mashigin sun haɗa da Manyan jiragen ɗaukar iskar gas guda biyu, Tankokin mai masu dogon zango guda biyu, Jirgin mai nau'in Supermax guda ɗaya, Da kuma jirgin mai nau'in Panamax guda ɗaya.

    Wannan adadi ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da matsakaicin kwanaki goma da suka gabata, wanda ya kai kusan jiragen ruwa 13 a rana.

    Sai dai kuma, ya kamata a lura cewa alƙaluman zirga-zirgar jiragen ruwa ta wannan mashigin na iya sauyawa, domin wasu jiragen ruwa kan kashe na’urorin aika bayanan wurinsu yayin tafiya, lamarin da kan sa ba a iya bibiyar su gaba ɗaya.

    Mashigin Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar mai da iskar gas a duniya, kuma duk wani tashin hankali a yankin na iya yin tasiri ga zirga-zirgar jiragen ruwa da kasuwannin makamashi na duniya.

  2. An yi taron gaggawa kan tsaro a jihar Plateau

    ,

    Asalin hoton, Mutfwang Facebook

    Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya jagoranci taron Majalisar Tsaro ta Jihar a ranar Laraba domin duba halin tsaro a jihar, yayin da rundunar ’yan sanda ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da hannu a wasu daga cikin hare-haren da aka kai kwanan nan.

    An gudanar da taron ne a Sabon Gidan Gwamnati da ke Little Rayfield, Jos, a daidai lokacin da aka kai wa wasu al’ummomin jihar hare-hare.

    Tattaunawar ta mayar da hankali kan sababbin barazanar tsaro, hare-haren da suka faru kwanan nan, tattarawa da musayar bayanan sirri, ayyukan kariya, haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro da kuma hanyoyin kare rayuka, dukiyoyi da harkokin tattalin arziki a faɗin jihar.

    Da yake magana bayan taron, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Plateau, CP Ayodeji Faniyan, ya bayyana cewa an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a wasu manyan hare-haren da aka samu a jihar cikin watan da ya gabata.

    Ya ce bincike na ci gaba domin gano tare da cafke sauran waɗanda ake zargi da hannu a waɗannan hare-haren.

    Ƙarin labarai:

  3. Hatsarin mota a Egypt ya kashe mutum 22

    ,

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Aƙalla mutane 22 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota bas da ya afku a gabashin ƙasar Masar, kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta ƙasar ta sanar.

    Wasu mutane 28 kuma sun jikkata a hatsarin da ya faru a safiyar Laraba a kan hanyar da ke tsakanin garuruwan bakin Tekun Bahar Maliya na Dahab da Nuweiba, a lardin Kudancin Sinai.

    Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na Masar da Jordan sun ce ’yan ƙasar Jordan har 10 na daga cikin waɗanda suka mutu a hatsarin.

    Har yanzu ba a bayyana musabbabin hatsarin ba.

    Yankin da hatsarin ya faru na ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido da suka yi fice, inda ke jan hankalin baƙi daga sassa daban-daban na duniya.

    Ba a san adadin mutanen da ke cikin motar bas ɗin ba a lokacin da hatsarin ya faru.

    A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Lafiya ta Masar ta ce ana kula da duk waɗanda suka jikkata a asibitoci uku daban-daban.

    Hatsurran mota masu muni na faruwa akai-akai a Masar, inda hukumomi suka bayar da rahoton cewa kusan mutane 6,000 ne suka mutu a hadurran hanya a shekarar 2025. Sau da yawa ana danganta irin waɗannan hatsurran da tuki cikin ganganci da kuma rashin kyakkyawan kula da hanyoyi.

    A watan da ya gabata ma, mutane 18 sun mutu yayin da wasu 30 suka jikkata bayan da manyan motoci biyu suka yi karo da juna a lardin Ismailia da ke arewa maso gabashin ƙasar.

  4. Gobarar dajin da ta yi makonni tana ci a Indonesia

    Ga wasu hotuna daga Kalimantan, inda wata gobarar daji suka shafe makonni suna ci gaba da ƙonewa, lamarin da ya rufe yankin da kewaye da shi da hayaƙi mai kauri.

    Wannan hayaƙi mai yawa ya mamaye sararin samaniya a yankin, yana rage gani sosai tare da haddasa matsalolin lafiya ga miliyoyin mazauna yankin.

    Gobarar dazukan da ke ci gaba da ƙonewa na daga cikin manyan abubuwan da suka jawo gurɓacewar iska a Indonesia da ma wasu ƙasashe maƙwabta.

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka da ke Kuwait

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Sa’a guda bayan da sojojin Kuwait suka fitar da wata sanarwa cewa tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar na dakile hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da makamai masu linzami da suka fito daga Iran, kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke da alaƙa da Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran, ya wallafa cewa “Sansanonin sojin Amurka da ke Kuwait sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa na Iran.”

    Sai dai kamfanin dillancin labaran bai bayar da ƙarin cikakkun bayanai game da lamarin ba, kuma zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, Cibiyar da ke lura da ayyukan Sojin Amurka ba ta mayar da martani kan waɗannan rahotanni ba.

    Tsauraran matakan takaita yaɗa bayanai a ƙasashen yankin Tekun Fasha sun sa ya zama da wahala ga kafafen yaɗa labarai su samu damar kai tsaye zuwa wuraren da aka kai hare-haren.

    Haka kuma, Amurka ta samar da wani tsarin saka idanu kan wallafa hotunan tauraron ɗan adam na waɗannan wurare.

    A ranar Laraba, Tasnim ta wallafa wasu hotunan da aka ce an ɗauko su daga sama, waɗanda ta danganta da hare-haren da Iran ta kai ranar Talata kan sansanonin Amurka a Jordan. Kamfanin dillancin labaran ya yi iƙirarin cewa hotunan suna nuna irin ɓarnar da hare-haren suka haifar.

    Karanta ƙarin labarai a nan:

  6. Sakataren MDD ya nuna damuwa kan harin da ya kashe masu biki a Iran

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya, Stephane Dujarric, ya ce a ranar Laraba cewa: “Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya na matuƙar damuwa da sake barkewar musayar hare-haren soji tsakanin Amurka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a daren jiya.

    Ya fi damuwa musamman da rahotannin da ke nuna an sami asarar rayukan fararen hula, ciki har da harin da aka kai wa wani bikin aure. Kai hari kan fararen hula ba abin yarda ba ne ta kowace hanya.”

    Da yake magana a taron manema labarai na yau da kullum, Dujarric ya jaddada cewa, “Babban Sakataren yana kira ga dukkan ɓangarorin da su nuna matuƙar kame kai, su bi wajibcin da ke kansu na dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa, kuma su guji duk wani mataki ko furuci da zai iya ƙara rura wutar rikici.

    Babban Sakataren ya ci gaba da yin imani cewa babu wata mafita ta soja ga wannan rikici. Diflomasiyya ita ce hanya ɗaya tilo ta gaba, kuma yana kira ga dukkan ɓangarorin da su koma teburin tattaunawa da ƙoƙarin diflomasiyya ba tare da jinkiri ba.”

    Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya gudanar da ganawa da tattaunawa da bangarori daban-daban kan rikicin, yana mai jaddada muhimmancin tattaunawa da hanyoyin lumana domin rage tashin hankali da kauce wa ƙarin asarar rayuka.

  7. Mutane 18 sun mutu 142 sun jikkata - Iran

    Hossein Kermanpour, Daraktan Hulɗa da Jama'a na Ma’aikatar Lafiya ta Iran, ya sanar da sabbin alƙaluman waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka jikkata sakamakon hare-haren saman da Amurka ta kai a ranar Talata.

    Bisa ga waɗannan alƙaluma, adadin waɗanda suka mutu ya kai mutane 18, yayin da adadin waɗanda suka jikkata ya kai 142.

    A cewar wannan jami’in lafiya na Iran, daga cikin waɗanda suka mutu akwai yaro guda da mata biyu.

    Haka kuma, daga cikin waɗanda suka jikkata akwai mata 61 da kuma mutane 44 da shekarunsu ba su kai 18 ba.

    Waɗannan alƙaluma na nuna cewa fararen hula, ciki har da mata da yara, na cikin waɗanda hare-haren suka shafa, lamarin da ya ƙara jawo damuwa kan tasirin rikicin ga rayukan jama'a.

  8. Hazon gobarar daji na barazana ga rayuwar miliyoyin mutane a Indonesia

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsawon makonni da dama, ƙasar Indonesia na fama da mummunar gobarar dazuka wadda ta haddasa yaɗuwar hayaƙi mai guba da ya rufe manyan sassa na ƙasar.

    Miliyoyin mutane a yankunan Sumatra da Kalimantan sun kasance cikin haɗarin shaƙar gurɓatacciyar iska, inda dubban mutane tuni aka kwantar da su a asibitoci saboda cututtukan da suka shafi numfashi.

    Hayaƙin da gobarar ta haifar ya kuma bazu zuwa ƙasashe maƙwabta kamar Malaysia da Philippines, lamarin da ya jawo damuwa a faɗin yankin Kudu maso Gabashin Asiya.

    A yau, za mu ci gaba da kawo muku sabbin bayanai kai tsaye daga yankunan da abin ya shafa, tare da bayyana yadda wannan hayaƙi mai guba ke taɓa rayuwar yau da kullum a wasu daga cikin manyan yankuna masu yawan jama'a a Kudu maso Gabashin Asiya.

  9. Shirinmu na murƙushe Iran ba zai ɗuki lokaci ba - Trump

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwana guda bayan harin da aka kai wa Iran a daren jiya, Donald Trump ya bayyana a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Fadar White House cewa sabon shirin sojin Amurka na murƙushe ba zai ɗauki lokaci mai tsawo ba.

    Ya bayyana hare-haren na daren jiya a matsayin “masu tsananin ƙarfi sosai,” yana mai cewa Amurka a shirye take ta sake kai wa Iran hari a kowane lokaci idan buƙatar hakan ta taso.

    Mista Trump ya ce Iran na ƙoƙarin ƙera makami mai linzami da zai iya jefa nakiyoyi, kuma Amurka ta lalata wannan shiri.

    A cewarsa, Iran ta kuma kasance tana sake gina tsarin radar da na makamai masu linzami, waɗanda hare-haren Amurka suka kai wa hari.

    Trump ya jaddada cewa sojojin Amurka za su ci gaba da sa ido kan duk wani yunkuri da Iran za ta yi na sake ƙarfafa ƙarfin sojinta, kuma za su ɗauki mataki idan suka ga ya zama dole.

  10. Kuwait ta kunna na'urar da ke kare sararin samaniyarta

    Sojojin ƙasar Kuwait sun fitar da wata sanarwa a safiyar yau Alhamis, inda suka bayyana cewa tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar na dakile “harin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa na abokan gaba” bayan abin da jami’an ƙasar suka kira “hari daga Iran.”

    A safiyar Laraba, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran da kuma sojojin Iran sun sanar da kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa kan sansanonin sojin Amurka da ke Bahrain, Jordan da Kuwait, a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren saman da Amurka ta kai.

    Sai dai, zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga hukumomin sojin Iran da ta tabbatar da sabbin hare-haren makamai masu linzami ko jiragen sama marasa matuƙa da ƙasar ta kai.

    Sanarwar Kuwait ta nuna ci gaba da zaman ɗarɗarwa na ci gaba kan rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da hukumomi ke sa ido kan halin da ake ciki da kuma yiwuwar ƙarin tashe-tashen hankula.

  11. Farashin dalar Amurka a Iran ya haura Toman 220,000.

    Bisa ga sanarwar da ofisoshin canjin kuɗi a cikin Iran suka fitar, mafi girman farashin da aka yi cinikin dala a ranar Laraba ya kai Toman 220,230 kan kowace dala ɗaya ta Amurka.

    Wannan sabon mataki daa farashin dala ya kai na nuna ƙarin matsin tattalin arziki da kuma raunin darajar kuɗin Iran, yayin da kasuwannin canji ke ci gaba da fuskantar sauye-sauye da rashin tabbas.

  12. Harin da Amurka ta kai Iran a faren jiya ya kashe mutum 18 ya jikkata 108

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Lafiya na Iran, Mohammad Reza Zafarghandi, ya sanar da cewa mutane 18 sun mutu yayin da wasu 108 suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai a larduna daban-daban n Iran a daren jiya.

    Wannan na ɗaya daga cikin mafi munin hare-haren da Amurka ta kai tun bayan yaƙin kwanaki 40.

    Tsaunukan Sirik na daga cikin wuraren da hare-haren Amurka suka shafa.

    Jami’an Iran sun sanar da cewa mutane huɗu, ciki har da wata mace da wani yaro da suka halarci wani bikin aure, sun mutu yayin da wasu 65 suka jikkata sakamakon hare-haren.

    Pejman Shahrokhi, shugaban Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Hormozgan, ya ce shida daga cikin waɗanda suka jikkata a lamarin da ya faru a tsaunukan Sirik na cikin mawuyacin hali a sashen kulawa ta musamman, yayin da wasu 26 ke kwance a sashen tiyata.

    Da yake amsa tambayar BBC Persian, kakakin CENTCOM Kyaftin Tim Hawkins bai musanta harin ba, yana mai cewa ya san komai game da rahotannin. Ya jaddada cewa sojojin Amurka ba sa kai hari kan fararen hula.

    A lardin Khuzestan, an ruwaito cewa mutane bakwai sun mutu yayin da wasu takwas suka jikkata a hare-haren da aka kai a yankunan da ke Ahvaz da Aghajari. An gano cewa aƙalla ɗaya daga cikin waɗanda suka mutu mamba ne na wata rundunar tsaro.

    Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kuma tabbatar da cewa mambobi huɗu na rundunar sararin samaniyarta sun mutu a lardin Kermanshah.

    Rahotanni sun kuma ce mayaƙa uku na rundunar Basij sun mutu bayan harin Amurka a tsibirin Lavan.

  13. Za a tilasta wa ƙasashen G20 kafa cibiyoyin AI

    Manyan shugabannin kamfanonin fasaha na Amurka da gwamnatin Trump sun tilastawa ministocin ƙasashen G-20 su rungumi fasahar AI da kuma kafa cibiyoyin bunƙasa ta.

    Yayin wani taro a North Carolina, Shugaban kamfanin fasaha na Nvidia, Jensen Huang, ya ce AI ya shiga jerin abubuwan more rayuwa masu muhimmancin gaske ga duniya, kamar dai ruwa da hanyoyin sufuri.

    Ga ƙasashen da suka zuba jari a wannan fanni, hanya ce da za ta taimaka wajen bunƙasa al'ummarku da kuma masana'antunku, cikin saurin da ba ku taɓa zato ba.

    Shugaban OpenAI, Sam Altman ya bayyana fasahar AI a matsayin abin da ya zama wajibi ga rayuwar da ake ciki yanzu.

    An dai gudanar da zanga-zangar adawa da matsayar ta su a ƙofar shiga zauren taron.

  14. Amurka ta musanta satar man Venezuela

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren makamashi na Amurka ya musanta cewa ƙasarsa na satar man fetur ɗin Venezuela, bayan ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta bai wa Washington damar iko da kashi ɗaya bisa biyar na rijiyoyin man ƙasar ta Kudancin Amurka.

    Chris Wright ya dage cewa yarjejeniyar wadda ke shan suka a yanzu, za ta share fagen cin gajiyar zuba jari na biliyoyin dala ga al'ummar Venezuela.

    Akwai gagarumin aiki da ya rage a yi kafin wannan babbar yarjejeniya tsakanin Washington da Venezuela ta fara aiki, amma ɓangarorin biyu na fatan cimma nasarar ta.

    A jiya Laraba, Mista Trump ya ce ba ya tunanin Venezuela ta shirya yin zaɓe a yanzu.