KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 10/05/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 10/05/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Jami'an tsaro sun miƙa Bello Badejo ga hukumar EFCC - Hadiminsa

    Badejo

    Asalin hoton, OTHERS

    Jami'an tsaron Najeriya da suka kama ɗantakarar Sanatan Taraba ta tsakiya a jam'iyar APC, Bello Bodejo, sun miƙa shi ga hukumar yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasar ta'annuti EFCC.

    A kama Badejo, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, a daren Alhamis bayan ya sauka a filin jirgin sama na Danbaba Suntai da ke birnin Jalingo a jihar.

    Hadimin Badejo, Malam Umar, ya shaida wa Daily Trust cewa magoya bayansa ne suka raka shi zuwa ofishin jami'an tsaron da suka kama shi, amma bai bayyana ko su wane ne ba.

    Umar ya ce tuntuni jami'an suka kai Badejo ofishin EFCC da ke Abuja, kuma babu wani ƙarin bayani da aka yi musu game da dalilin kama shi.

    Ya yi zargin cewa wasu abokan hamayyarsa ne suka kitsa kama shi saboda farin jinishi a takarar.

    "Yanzu haka ana tantance ƴantakarar jam'iyar kuma an kusa kammalawa. Manufarsu ita ce su hana shi shiga tantancewar," in ji Umar.

    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi kira hukumomin Najeriya su saki ɗantakarar Sanatan, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa.

  2. Malami ya sayi fom ɗin takarar gwamnan Kebbi a ADC

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, Abubakar Malami/FB

    Tsohon babban lauyan gwamnatin Najeriya, kuma ministan shari'ar ƙasar, Abubakar Malami ya sayi fom ɗin takarar gwamnan jihar Kebbi a jam'iyyar ADC domin shiga zaɓukan 2027.

    Malami ya ce ya ɗauki matakin shiga takarar ne saboda a cewarsa ba zai yi shiru kan abin da ya kira halin rashin tsaro da talauci da yunwa da taɓarɓarewar lafiya da matsin tattalin arziki da jiharsa ta Kebbi ke ciki ba.

    Tsohon ministan ya yi zargin cewa jihar Kebbi na fuskantar ɗaya daga cikin mafiya munin halin jin ƙai da munin shugabanci a Najeriya, inda ya kafa hujja da alƙaluman yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar da kuma matsayin talaucin da jihar ke ciki da yawan mace-macen mata a lokacin haihuwa da rashin abinci mai gina jiki da kuma rashin tsaro.

    A cewar Malami, fiye da kashi 67 cikin 100 na yaran jihar ƴan tsakanin shekara 6 zuwa 15 ba sa zuwa makaranta, yayin da ya ce fiye da kashi 88 cikin 100 na yaran jihar na fama da talauci ta fuskoki daban-daban.

    A yanzu haka dai tsohon ministan na fuskantar shari'ar zarge-zargen almundahanar miliyoyin kuɗaɗe a lokacin da yake riƙe da muƙamin ministan shari'ar ƙasar, tsakanin 2015 zuwa 2023.

  3. Shugaban Faransa ya isa Nairobi a wata ziyara da yake yi a Afirka

    Emmanuel Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya isa Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya a wata ziyara da yake yi don yauƙaƙa dangantaka da Afirka.

    Mista Macron zai gana da shugaban ƙasar Kenya, William Ruto a yau, kafin shugabannin biyu su jagoranci taron zuba jari na Afirka a gobe Litinin.

    Mista Macron zai gana da shugaban ƙasar Kenya, William Ruto

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Kenya, William Ruto ne ya tarbi Mista Macron

    Taron zai samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da jagororin kasuwancin nahiyar domin tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci da ƙirƙira da kuma ci gaba mai ɗorewa.

    A shekarun baya-bayan nan, Faransa ta rasa tasiri a ƙasashen da ta yi wa mulkin mallaka a Afirka ta Yamma.

    A baya-bayan nan ƙasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar suka kori dakarun Faransa da suka shafe shekaru suna yaƙar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a ƙasashen.

  4. Amnesty ta nemi hukumomin Najeriya su bincike kisan wani almajiri a hannun ƴansandan Katsina

    ƴansanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta buƙaci hukumomin ƙasar su binciki mutuwar wani almajiri mai shekara 16 a ofishin ƴansanda na Ƴankara da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce binciken da ta yi ya nuna cewa almajirin ya mutu ne sakamakon azabtarwa ta hanyar dukansa da wayar ƙarfe da ƴansandan suka yi.

    Amnesty ta ce ƴansandan sun kama almajirin ne mai suna Bishir Malam Dauda daga makarantar tsangayarsu bayan da wani abokinsa ya ambaci sunansa a lokacin da ƴansandan ke yi masa binciken zargin satar wake.

    Ƙungiyar ta zargi jami'an ƴansandan Ƴankara da azabtar da yaron har sai da ya mutu, sannan suka kai gawarsa ƙaramin asibitin Ƴanƙara.

    ''Abin da ya faru da almajirin na azabtarwa, tsantsar keta haƙƙin bil'adama ne... Don haka dole ne a gudanar da bincike tare da hukunta duka ƴansandan da ke hannu a lamarin'', in ji sanarwar.

    Malamin Almajirin da BBC ta zanta da shi ya ce ƴansandan sun ɗauke shi daga makarantarsa da nufin gudanar da bincike, amma sai baturen ƴansandan yankin ya sanar masa da mutuwar yaron.

    Kawo yanzu dai rundunar ƴansandan jihar ba ta ce komai ba game da lamarin.

  5. 'Mun aika wa Pakistan amsa kan shawarar Amurka ta kawo ƙarshen yaƙinmu'

    Abbas Araghchi

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce ta aika wa Pakistan amsa kan matsayin da ta ɗauka game da sabuwar shawarar da Amurka ta gabatar na kawo ƙarshen yaƙin ƙasashen biyu.

    Ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ya ce ƙasarsa ''ta fitar da matsayin nata ne'' bayan cikakken bincike na nazari.

    Sai dai ba ta yi arin haske kan abin da ke cikin amsar tata ba.

    Amma rahotonni sun ce saƙon na na Iran ya ƙunshi raba tattaunawar zuwa matakai guda biyu, na farko shi ne mayar da hankali don kawo ƙarshen rikicin da ake yi kan mashigar Hormuz, yayin da mataki na biyun zai ƙunshi tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran da takunkuman da aka sanya mata.

    A makon da ya gabata ne Amurka ta fitar da sabuwar shawarar kawo ƙarshen yaƙin, inda Donald Trump ya ce suna jiran martanin Iran game da hakan.

    A cewar kafofin yaɗa labaran Amurka, sabuwar shawarar Amurka, takarda ɗaya ce mai sakin layi 14.

  6. Jirgin Qatar ɗauke da gas ya tsallaka mashigar Hormuz zuwa Pakistan

    Cibiyoyin kula da sufurin jiragen ruwa na duniya sun ce wani jirgin man Qatar ɗauke da gas ya tsallaka mashigar Hormuz, inda ya kama hanyar zuwa Pakistan

    Idan ta tabbata mai ya fitar - bayan amincewar Iran - zai kasance jirgin Qatar na farko da ya fitar da kaya daga Gabas ta Tsakiya tun bayan fara yaƙin.

    A wani labarin na daban kuwa firaministan Qatar ya soki Iran kan harin da ta kai wa wani jirgin dakon kaya mai ɗauke da tutar Amurka a gaɓar ruwar Qatar.

    Harin ya haifar da ƴar ƙaramar gobarar, amma babu rasa rai.

    Kuwait da UAE sun bayar da rahoton kakkaɓo jiragen Iran marasa matuƙa, da suka zarga da keta sararin samaniyarta.

  7. An yi zanga-zangar adawa da gwamnatin Netanyahu a Tel Aviv kan yaƙin Iran

    Wasu mazauna birnin Tel Aviv sun gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu kan yaƙin Iran.

    masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Jack GUEZ / AFP via Getty Images

    zanga-zanga

    Asalin hoton, Jack GUEZ / AFP via Getty Images

    Zanga-zanga

    Asalin hoton, Jack GUEZ / AFP via Getty Images

    masu zanga-zanga

    Asalin hoton, Jack GUEZ / AFP via Getty Images

  8. Indiya ta yi gwajin sabon makaminta na linzami na zamani

    makami mai linzami

    Asalin hoton, Hindustan Times via Getty

    Rundunar sojin Indiya ta yi nasarar yin gwajin sabon makaminta na linzami na zamani mai suna Agni wanda ya faɗa gaɓar ruwan Odisha.

    Makamin zai kuma iya harba kayuwa masu yawa a lokaci guda zuwa wurare daban-daban.

    Ma'aikatar taron ƙasar ta ce an yi gwajin makamanin ne a ranar Juma'a, 8 ga watan Mayu.

    "An har makamin ne daga tsibirin Abdul Kalam zuwa Odisha'', a cewar ma'aikatar tsaron cikin sanarwar da ta fitar.

    An fara ƙera makamin na Agni ne a shekarar 1983, inda aka riƙa sabunta shi lokaci zuwa lokaci, har zuwa yanzu da aka sabunta shi a karo na biyar, wanda zai iya yin tafiyar nahiya zuwa nahiya, wanda kuma zai iya ɗaukar kan makamin nukiliya.

    Makamin zai iya yin tafiyar tazarar kilomita fiye da 5,000 kafin ya sauka.

  9. Atiku, Amaechi da Hayatudeen sun sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a ADC

    Atiku da Amaechi

    Asalin hoton, El-Rufai

    Jiga-jigan adawar Najeriya na haɗakar jam'iyyar ADC uku sun sayi fom ɗin takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar.

    Mutanen uku da kawo yanzu suka sayi fom ɗin sun haɗa da jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar, da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da kuma Mohammed Hayatu-Deen.

    Hayatu-Deen ne ya fara sayen fom ɗin, kafin daga baya sauran mutanen biyu suka bi sahunsa.

    Matakin na zuwa ne ƙasa da shekara guda kafin babban zaɓen ƙasar na 2027.

    Yanzu abin da ya rage shi ne zaɓen fitar da gwani tsakanin ƴantakarar uku, domin tunkarar Tinubu na APC da kuma wanda NDC za ta tsayar.

    ADC na ɗaya daga cikin manyan jam'iyyun hamayya a ƙasar, sai dai sakamakon rikicin shugabancin da take fama da shi a baya-bayan nan ta rasa biyu daga cikin manyan jiga-jiganta, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da suka koma NDC.

  10. Fars: Jirgin Amurka aka kai wa hari a gaɓar ruwan Qatar

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito cewa jirgin dakon kayan nan da aka kai wa hari a gaɓar ruwan Qatar na Amurka ne.

    Fars ya ambato wata majiya na cewa jirgin dakon kayan na tafiya ne ɗauke da tutar ƙasar Amurka a jikinsa.

    Kawo yanzu dai Amurka ba ta ce komai ba game da harin jirgin.

    Cibiyar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya - wadda ke lura da hanyoyin sufurin jiragen ruwa na duniya - ta ce wani makami da ba a san daga inda aka harbo shi ba, ya faɗa kan jirgin ruwan a kusa da gaɓar ruwan Qatar.

    Rahotonni sun ce harin ya faɗa kan jirgin ne tazarar kilimota 43 daga arewa maso gabashin Qatar, lamarin da ya sa wuta ta kama jirgin, amma ba wanda ya rasa ransa.

  11. Ƙasashen da suka saka mana takunkumi ba za su wuce ta Hormuz ba - Iran

    Kakakin sojin Iran

    Asalin hoton, Amount

    Rundunar sojin Iran ta ce ƙasashen da ke aiki da takunkuman da Amurka ta sanya wa ƙasar za su fuskanci wahalar wucewa ta Hormuz.

    Kamfanin dillancin labaran ƙasar, IRNA ya ambato kakakin rundunar sojin ƙasar, Mohammad Akraminia na cewa ''daga yanzu duk ƙasar da ke aiki da takunkuman da Amurka ta sanya mana, jiragenta ba za su wuce ta mashigar Hormuz cikin sauƙi ba''.

    ''Amurka ba za ta iya tare duka wannan na Tekun Arewacin Indiyan mai faɗin gaske ba, da abin da take na datse jiragenmu ba'', in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa ''babu shakka maƙasudin wannan datsewar shi ne matakin farfaganda na yunƙurin kisan jami'an Iran masu lura da mashigar Hormuz, kuma yaƙin da muke yi na ci gaba da tafiya yadda muke so, kawo yanzu jirage ƙalilan aka kama, yayin da mu kuma muka samu nasarar hana jiragen gwamnatin Yahudawa zirga-zirgar muka kuma kama wasu''.

  12. An rantsar da tauraron fina-finan Indiya a matsayin babban ministan Tamil Nadu

    C Joseph Vijay

    Asalin hoton, Getty Images

    An rantsar da tauraron fina-finan Indiyan nan da ya jagoranci jam'iyyarsa wajen lashe zaɓen majalisar dokokin jihar Tamil Nadu a kudancin Indiya, a matsayin babban ministan jihar.

    C Joseph Vijay, jagoran jam'iyyar TVK (Tamilaga Vettri Kazhagam), ya sha rantsuwar kama aiki a gaban dubban magoya bayansa a Chennai, babban birnin jihar.

    Mista Vijay zai jagoranci gwamnatin haɗaka, wadda jam'iyyarsa ta lashe kujeru 108 a majalisar dokokin jihar.

    Jam'iyyarsa ta TVK ta ƙulla ƙawance da wasu jam'iyyun uku domin samun rinjayen kujeru 118 da take buƙata domin kafa gwamnati.

  13. Firaministan Qatar ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya gana da firaministan Qatar a birnin Miami na Amurka.

    Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ya ce Mista Rubio da Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani sun tattauna buƙatar aiki tare ''domin kawar da barazana da inganta zaman lafiya da tsaro a faɗin Gabas da Tsakiya.''

    Yanzu haka dai Amurka na jiran martanin Iran kan sabuwar shawarar yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin da ƙasashen biyu ke yi, domin fara zaman tattaunawar zaman lafiya tsakanin ɓangarorin.

    A ƴan kwanakin nan an yi musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu a kewayen mashigar Hormuz, karon farko tun bayan fara aiki da yarjejeniyar dakatar wuta.

    Tun bayan fara yaƙin ne dai Iran ta hana jiragen ruwan da ba nata ba wucewa ta mashigar.

  14. 'An kai wa jirgin ruwan ƴan kasuwa hari a gaɓar ruwar Qatar'

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Cibiyar kula da zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya - wadda ke lura da hanyoyin sufurin jiragen ruwa na duniya - ta ce wani makamai da ba a san daga inda aka harbo shi ba, ya faɗa kan wani jirgin ruwa na ƴan kasuwa a kusa da gaɓar ruwan Qatar.

    Rahotonni sun ce harin ya faɗa kan jirgin ne tazarar kilimota 43 daga arewa maso gabashin Qatar, lamarin da ya sa wuta ta kama jirgin, amma ba wanda ya rasa ransa.

    Matakin na zuwa ne yayin da rundunar juyin juya halin Iran ta sake yin barazanar kai hare-hare kan cibiyoyin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, idan har aka kai wa jiragen Iran hare-hare, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar a mashigar Hormuz.

  15. Ina ganin yaƙin UKraine ya zo ƙarshe - Putin

    Sojojin Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce yana ganin yaƙin Ukraine ya zo ƙarshe, amma kuma ya ce zai gana da Shugaba Zelensky na Ukraine ne kawai idan an cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa.

    Mista Putin na magana ne da manema labarai a fadarsa ta Kremlin bayan da Rasha ta gudanar da bikin faretinta na soja don tunawa da nasara da ta samu a kan sojojin Jamus na Nazi a lokacin yaƙin Duniya na Biyu.

    Ana gudanar da bikin ne a kowace ranar 9 ga watan Mayu.

    Waɗanda suka halarci taron na bana sun ce Rasha ba ta fito da manyan motocin yaƙinta na igwa-igwa ba da sauran manyan kayan yaƙi - waɗanda ta saba nuna wa duniya irin ƙarfinta na soji.

  16. Marabanku

    Assalamu alaikum masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku ci gaba da ta tafka muhawara kan labaran da muke wallafa a shafukanmu na sada zumunta