Tsohon Ministan Sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu tikin takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar PDP bayan da ya koma cikinta.
Ya yi nasarar ne lokacin zaɓen fitar da ƴantakara da aka yi yau a wani wajen taro a jihar Gombe.
Shugaban kwamitin zaɓe na PDP, Hon Gregory Yenlong ne ya ayyana fitaccen malamin addinin a matsayin ɗantakara ɗaya tilo a wani.
Da yake magana jim kaɗan bayan ayyana shi a matsayin wanda zai yi wa PDP takarar gwamna, Farfesa Pantami ya ce hidimta wa al'ummar Gombe ne ya sa yake neman kujerar gwamnan jihar.
Ya yi alƙawari cewa idan har aka zaɓe shi a 2027, zai yi shugabanci bisa gaskiya da adalci.
A halin da ake ciki, Pantami zai fafata da wasu ƴantakarar a zaɓen an 2027, ciki har da Jamilu Gwamna na APC mai mulkin jihar.
Tun farko Farfesa Ali Isa Pantami ya janye daga takarar gwamna a APC bisa zargin 'maguɗi' da 'son rai' da ya ce sun saɓa da dokokin zaɓen Najeriya na 2026, kuma ya yi haka ne bayan tuntuɓa da kuma duba na tsanaki na yadda tsarin zaɓen fitar da gwanin yake.
Da ma dai Farfesa Pantami ya shaida cewa bai aminta da sulhun da aka yi a baya ba, wanda ya fitar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar ta Gombe kuma ya sha alwashin "yaƙar zalunci bisa doka".