KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 26 ga watan Mayun 2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Kotu za ta yanke hukunci kan makomar Jonathan ta yin takara a 2027

    ..

    Asalin hoton, @GEJonathan/X

    Yau ake sa rai babbar kotun tarayya a Najeriya za ta yanke hukunci kan ko tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai iya yin takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

    Wani ɗan Najeriya, Johnmary Jideobi ne ya shigar da ƙarar a kotu inda yake neman kotu ta dakatar da tsohon shugaban ƙasar daga komawa kan kujerar shugabancin ƙasar.

    Wanda ya shigar da ƙarar ya ce ya shigar da ƙarar ce saboda a halin da ake ciki Jonathan ya karɓi rantsuwar kama aiki sau biyu kafin wa'adin shugabancinsa ya ƙare a 2015.

    Yana neman kotu ta yi ƙarin haske kan sashe na 1 da 137(3) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 kan cancantar tsayawa takarar shugaban ƙasa da kuma shekarun da aka ƙayyade na wa'adin mulkin.

    Ƙarar kuma na neman a hana hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC karɓa ko wallafa sunan Jonathan cikin jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

    An shigar da ƙarar ce yayin da wani tsagi na Jam'iyyar PDP ke ƙoƙarin ganin Jonathan ya shiga takarar bayan rahotanni da ke cewa sun amince ya tsaya takara ba tare da hamayya ba.

  2. Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran

    Jirgin Yaƙi

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Kudancin Iran da suka shafi cibiyoyin harba makamai masu linzami da jiragen ruwa da ke ƙoƙarin dasa nakiya.

    Farmakin na Amurka an kai su ne da nufin kare kai don kare dakaru daga barazanar sojojin Iran, in ji cibiyar ayyukan soji ta Amurka.

    Kakakin cibiyar, Kyaftin Tim Hawkins ya ce sojojin Amurka "na ci gaba da kare dakarunmu yayin da suke taka tsantsan a lokacin tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu".

    Iran zuwa yanzu ba ta mayar da martani kan hare-haren na Amurka ba. Sai dai mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baqai tun farko ya ce an samu ci gaba a wasu fannonin na tattaunawar da aka yi don kawo ƙarshen yaƙin, ba lalle a cimma yarjejeniya nan kusa ba.

    Zuwa yanzu ba a san tasirin hare-haren kan yiwuwar cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ba.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce akwai yiwuwar a iya cimma yarjejeniya inda ya yi nuni da tattaunawar ranar Talata tsakanin babban jami'in tattaunawa kuma ministan harkokin wajen Iran da Firaministan Qatar.

  3. Maraba

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.