Adadin waɗanda suka mutu a harin da Rasha ta kai kan Ukraine ya kai 30

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Rasha sun kai wani mummunan harin makami mai linzami kan Kyiv cikin daren Alhamis, inda suka kashe aƙalla mutum 30, abin da magajin garin ya bayyana a matsayin "hari mafi muni" da aka kai babban birnin Ukraine.
Mutum 91 sun ji rauni, in ji shugaban gwamnatin sojin Kyiv, Timur Tkachenko.
Magajin gari Vitaly Klitschko ya ce wata tashar motocin asibiti na daga cikin wuraren da abin ya shafa.
Duk da cewa hare-haren da aka kai a baya sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wannan harin shi ne wanda ke da mafi yawan bama-bamai da aka zazzaga a babban birnin ƙasar.
An kwashe mutane daga unguwanni da dama yayin da aka kai hare-hare a birnin sa'o'i bayan shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gargaɗin cewa Rasha na shirin kai hari.
Moscow ta ce dakarunta sun kai hari kan abin da ta kira masana'antar soji a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da ake kai wa farar hula a Rasha.
Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai jiya Alhamis cewa, Rasha za ta ci gaba da ƙara matsawa gwamnatin Kyiv lamba har sai ta cimma muradunta.
















