Sterling zai iya zama kamar Messi ko Ronaldo - Guardiola

Sterling ya ci kwallaye biyar a wasanni hudu na gasar Premier a kakar wasa ta bana

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sterling ya ci kwallaye biyar a wasanni hudu na gasar Premier a kakar wasa ta bana

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce Raheem Sterling na da damar kai matsayin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

Bayan rawar ganin da ya taka a wasanni biyu da Ingila ta buga a makonnan, kocin tawagar Ingila Gareth Southgate ya ce Sterling na da kwazon da zai iya zama kamar wadancan 'yan wasan biyu.

Guardiola ya ce "babu wanda zai iya hada kanshi da su biyu," a yanzu amma Sterling zai iya kokarin da zai kai matsayinsu.

"Hakan zai iya zama burinsa da namu baki daya," inji kocin dan asalin Sipaniya.

"Idan Raheem zai sa himmar kamo wadannan biyu" kai! da abin yayi kyau.''

"Za muyi duk abin da za mu iya domin taimakonsa, tabbas zai iya amma ba zan ka'ide masa yadda zai yi ba, ba na tunananin zan masa haka, gaskiya ina so ya zama.''

Ya kuma ce "amma a halin da ake ciki, babu wani dan kwallo a duniya da zai iya abinda wadannan mutanen biyun suke yi a ko wane mako cikin tsawon shekaru 10.''

Sterling ya jefa kwallaye 8 cikin wasanni 8 da ya buga a kungiyarsa da kuma kasarsa a wannan kakar wasannin.

Sai dai Guardiola yana fatan kokarin da Sterling ya ke yi ba zai rude shi ba ya kuma kasa komi a gaba.