Ronaldo ya kafa tarihin cin kwallo a Turai

Asalin hoton, Getty Images
Ronaldo ya zama kan gaba a matakin wanda ya fi cin kwallaye a nahiyar Turai, bayan da ya zura hudu a raga a karawar da Portugal ta ci Lithuania 5-1 ranar Talata.
Kwallo hudu Ronaldo ya ci wa Portugal wadda ta ziyarci Lithuania a wasan neman gurbin shiga gasar Turai da za a yi a 2020, kawo yanzu ya ci 93 kenan jumulla.
Haka kuma karo na takwas yana cin kwallaye uku-uku rigis a wasa, kuma karo na 150 yana zura kwallo tsakanin tawagar kasashe da kulob-kulob.
Wannan bajintar da Ronaldo ya yi, ta sa ya zama na farko a Turai da ya ci wa kasarsa kwallo sama da 90, kuma saura 16 ya kamo tarihin dan kasar Iran, Ali Dae da ke kan gaba a yawan cin kwallaye a duniya.
A wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai kuwa, Ronaldo ya ci 25, hakan ya sa ya bai wa dan wasan tawagar Jamhuriyar Ireland, Robie Keane tazarar kwallo biyu.
Tsohon dan wasan tawagar Jamhuriyar Ireland, Robbie Keane ya taya Ronaldo murnar wannan bajintar da ya yi a shafinsa na sada zumunta wato a Instagram.

Asalin hoton, Robbie Keane Instagram
Keane mai shekara 34 shi ne ke kan gaba a yawan cin kwallaye a Turai a baya can, amma yanzu Ronaldo ya doke shi.
Babu wanda ya kai Ronaldo cin kwallaye a Turai a wasan kasa da kasa, inda ya zura 72 a raga har da kwallon farko da ya ci da ukun da ya zura a raga a Nations League.
Dan wasan da ke taka-leda a Juventus ya zura kwallo 30 a wasannin neman shiga gasar kofin duniya, bangaren nahiyar Turai.
Ronaldo zakaran Ballon d'Or biyar, ya ci kwallo 26 daga cikin 93 saura minti 15 a tashi daga wasa, kuma 25 da kai da 22 da kafar hagu a karawa 61 da ya yi wa tawagar Portugal.
Idan ka cire bugun fenariti, Ronaldo bai taba cin Faransa da Jamus da Italiya da kuma Ingila ba a lokacin da ake murza leda.
Sai dai da akwai kasashen da ya ci kwallo biyar a wasa da suka hada da Andora da Armenia da Latvia da kuma Sweden.











