Ali Nuhu 'ya mika wuya', Saratu Daso ta cashe? Hotunan 'yan fim na mako

Zango
Bayanan hoto, Jarumi Adam A. Zango da fitacciyar mawakiyar nan Hadiza Blell, wadda aka fi sani da Di'ja a wajen daukar fim din Mati A Zazzau a Bauchi
An wallafa
Zahradeen Sani
Bayanan hoto, Daga hagu: Saddiq Sani Saddiq, Rahama Sadau da Zahradeen Sani a wajen daukar fim din Mati A Zazzau a Bauchi. Fim din na kamfanin Sadau Movies ne.
Saratu Daso da Iman Sani Danja lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar Iman
Bayanan hoto, Saratu Daso da Iman Sani Danja lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar Iman
Ali Nuhu yana karbar lambar yabo daga wurin Aisha Buhari, mai dakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Bayanan hoto, Ali Nuhu ya ziyarci fadar shugaban najeriya inda ya karbar lambar yabo daga wurin Aisha Buhari, mai dakin Shugaba Muhammadu Buhari...ko Sarki ya mika wuya ne?
Ibrahim Maishunku ma na cikin wadanda aka bai wa lambar yabo bisa irin gudunmawar da yake bayar wa a Kannywood da kuma fafutukar zake zaben Shugaba Buhari a 2019
Bayanan hoto, Ibrahim Maishunku ma na cikin wadanda aka bai wa lambar yabo bisa irin gudunmawar da yake bayar wa a Kannywood da kuma fafutukar ganin an sake zaben Shugaba Buhari a 2019
Yaki A Soyayya
Bayanan hoto, A makon nan ne Nafisa Abdullahi ta fitar da sabon fim din da ta dauki nauyin shiryawa, Yaki A Soyayya, wanda za a soma nunawa a sinima ranar 28 ga watan Disamba, 2018
Maryam Yahya da Garzali Miko
Bayanan hoto, Maryam Yahya da Garzali Miko lokacin daukar fim din Gidan Kashe Ahu
Falalu Dorayi
Bayanan hoto, Falalu Dorayi ya wallafa sakon Juma'a mai taken K A D A M U D A L A I F I N K A: "Bai halatta ba ga Mumini, ya ringa bibiyar 'yan uwansa muminai domin ya gano nakasunsu da gazawarsu da aibunsu ko kazantarsu."
Hafsa Idris (Barauniya)
Bayanan hoto, Hafsa Idris (Barauniya) ta wallafa wannan hoto ne ranar Asabar....wankan sukari ko?