An fara shari'ar kisan Tupac Shakur bayan shekaru 30

Asalin hoton, Getty Images
An fara shari’ar wani tsohon shugaban ƙungiyar daba, Duane “Keffe D” Davis, a Las Vegas kan zargin hannu a kisan fitaccen mawakin Amurka Tupac Shakur, wanda aka kashe a shekarar 1996.
Masu gabatar da ƙara sun ce Davis ne ya shirya kisan tare da samar da bindigar da aka yi amfani da ita wajen harbin Tupac bayan wata takaddama tsakanin ƙungiyoyin da ke da alaƙa da kamfanonin waƙoƙi na gabashi da yammacin Amurka.
Tupac, wanda ya yi fice da waƙoƙi kamar California Love da All Eyez on Me, ya mutu yana da shekara 25 bayan an harbe shi a Las Vegas bayan kallon damben Mike Tyson.
Ana sa ran shari’ar za ta ɗauki kusan wata guda, kuma idan aka samu Davis da laifi, zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai ba tare da beli ba.





















