Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 18/06/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Trump ya ce yana sa ran Isra'ila ta dakatar da duk wasu hare-hare a Lebanon

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce yana sa ran a tsagaita wuta gaba ɗaya a dukkan angarorin da ke rikici a Gabas ta Tsakiya, ciki har da tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon.

    A wani sabon saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce yana fatan ƙasashen yankin za su cika alƙawuran da suka ɗauka domin tabbatar da tattaunawar zaman lafiya ta gudana yadda aka tsara.

    "Muna sa ran a tabbatar da tsagaita wuta baki ɗaya a dukkan ɓangarori, ciki har da a Lebanon tsakanin Hezbollah da Isra'ila," in ji shi

    Sashe na farko na yarjejeniyar da Iran da Amurka suka rattaba wa hannu ya jaddada buƙatar dakatar da duk wasu hare-hare a dukkan wuraren da rikicin ya shafa, ciki har da Lebanon.

    Sai dai duk da hakan, Isra'ila ta bayyana cewa ba ta da shirin janye dakarunta daga Lebanon.

    Haka kuma kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Lebanon sun ruwaito cewa Isra'ila ta kai hare-hare a wasu yankunan kudancin ƙasar a yau.

  2. Duk jirgin ruwan da zai bi ta Mashigar Hormuz sai ya nemi izini - Iran

    Majalisar Tsaron Iran ta bayyana cewa duk wani jirgin ruwa da zai bi ta Mashigar Hormuz sai ya nemi amincewar hukumomin Iran.

    A cikin wata sanarwa da kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Iran suka wallafa, majalisar ta ce an dakatar da karɓar kuɗin harajin da jiragen ruwa ke biya domin amfani da mashigar na tsawon kwanaki 60, kuma Iran ce za ta ɗauki nauyin hakan ƙarƙashin yarjejeniyar da ta ƙulla da Amurka.

    Sai dai sanarwar ta ce duk da dakatar da harajin, jiragen ruwa za su ci gaba da gabatar da buƙatar izinin wucewa ta hannun Hukumar Mashigar Tekun Fasha, wata hukuma da Iran ta kafa a lokacin yaƙin domin ƙara sa ido da iko kan wannan muhimmiyar hanyar ruwa.

    Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin safarar mai da kayayyaki a duniya, kuma duk wata tangara da aka samu a yankin kan jawo hankalin ƙasashen duniya.

    Mataimakin shugaban Amurka, JD. Vance, dai ya shaida wa manema labarai cewa ya kamata hanyoyin ruwa na ƙasa da ƙasa su kasance a buɗe ba tare da karɓar haraji ba, inda ya ce bai kamata a bari a yi amfani da mashigar a matsayin hanyar da za a takura wa duniya ba.

  3. Dole ce ta sa Trump amincewa da yarjejeniya da Iran - Khamenei

    Jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei, ya fitar da saƙo a karon farko bayan sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin Amurka da Tehran.

    Kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka wallafa, Mojtaba ya ce da farko bai amince da sharuɗɗan yarjejeniyar ba, amma shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya shawo kanshi bayan ya ba shi tabbacin za a mutunta al'ummar Iran.

    "Shugaban Amurka ne ya matsu wajen ganin ya yi duk mai yiwuwa an kai wannan matakin," in ji Khamenei.

    "Duk da yake ina da nawa ra'ayin game da yarjejeniyar, na amince a aiwatar da ita a matsayi na jagora saboda tabbacin da shugaban ƙasar [Iran] ya ba ni cewa za a mutunta ƴancin al'ummar Iran."

    Khamenei ya ce sai da Pezeshkian ya tabbatar masa cewa idan Amurka ta miƙa wasu buƙatun da suka saɓa da hankali, ba za su gabatar da su ba.

    Tun da aka naɗa Mojtaba Khamenei mai shekaru 56 a matsayin jagoran addinin Iran a ranar 8 ga watan Maris ba bayyana cikin al'umma ba saboda dalilai na tsaro.

    Sai dai ana wallafa saƙonnin da yake fitarwa a kafafen yaɗa labaran ƙasar.

  4. An kashe sojoji 11 a harin filin jirgin sama na Yamai

    Sama da mutum 30 aka kashe a harin da aka kai filin jirgin saman ƙasa da ƙasa da ke birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.

    Ma'aikatar Tsaron ƙasar ta ce daga cikin mutanen da aka kashe akwai sojoji 11 da fararen hula biyu, inda aka kashe mutum 22 daga cikin maharan.

    Da sanyin safiyar yau Alhamis ne aka fara jin ƙarar harbe-harbe da fashewar abubuwa a babban filin jirgin saman. Sai dai har yanzu ba a san waɗanda suka kai harin ba.

    Hukumomin ƙasar sun ce an daƙile harin da aka kai filin jirgin, kuma za a iya ci gaba da zirga-zirga.

    Nijar da maƙotan ƙasashe irinsu Mali da Burkina Faso na fuskantar ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga.

  5. Ya zama wajibi Isra'ila ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiya - JD Vance

    Mataimakin shugaban Amurka, J. D. Vance, ya ce ba za a iya hana kowace ƙasa tsakanin Isra'ila ko Iran haƙƙin kare kanta ba, amma ya jaddada cewa dole ne Isra'ila, kamar sauran ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki, ta mutunta yarjejeniya zaman lafiyar da ake ƙoƙarin tabbatarwa.

    Da yake amsa tambayoyin manema labarai game da sukar da shugaban Amurka Donald Trump, ya yi wa hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon, Vance ya ce ba ya son tauye haƙƙin Isra'ila na kare kanta.

    "Da alama muna gab da samun gagarumar nasara wajen cimma yarjejeniya, sai kuma ba zato ba tsammani aka samu wani babban fashewa a wani yanki da jama'a ke zaune a Beirut. Wannan abu ne da ba za a amince da shi ba," in ji shi.

    Vance ya ƙara da cewa Amurka na son haɗin kan Isra'ila tare da samar da wani tsari na haɗin gwiwa a yankin da zai taimaka wajen katse hanyoyin samun kuɗaɗen ƙungiyar Hezbollah da kuma hana ta kai hare-hare kan Isra'ila.

  6. Ana ci gaba da kai hare-hare a Lebanon duk da yarjejeniyar Amurka da Iran

    Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankulla a Lebanon duk da yarjejeniyar da Amurka da Iran suka cimmawa na kawo ƙarshen yaƙi a kowane ɓangare.

    Kafar watsa labaran gwamnatin Lebanon ta ce mutum guda ya rasu yayin da aka jikkata wani a harin jirgi marar matuƙi da Isra'ila ta kai kudancin Lebanon.

    Isra'ila ta ce sojanta guda ya rasu jiya Laraba a wajen musayar wuta da Hezbollah.

    Isra'ila ta nace cewa dole ne dakarunta su ci gaba da kasancewa cikin wasu yankuna na Lebanon.

  7. Kotu ta ɗaure mutumin da ke tara buhunan ba-haya a ƙofar gidansa a Kano

    Wata kotu a arewacin Najeriya ta yanke hukuncin ɗauri na mako biyu ga wani mutum bayan maƙwaftansa sun yi ƙorafi kan yadda yake tara buhunan ba-haya a ƙofar gidansa, lamarin da ke cutar da mazauna unguwar.

    Maƙwafta ne suka kai ƙarar Mohammed Sa'idu kotu a birnin Kano, bayan sun ce warin ya buwaye su.

    Mai shari'a Halima Wali ta yanke hukuncin a tsare mutumi na tsawon wata huɗu sannan an buƙaci ya biya tarar naira 100,000.

  8. Firaministan Equatorial Guinea ya yi murabus saboda gaza cika alƙawuran da ya ɗauka

    Gwamnatin ƙasar Equatorial Guinea ta yi murabus bayan gaza sauke nauyin da aka ɗora mata, kamar yadda Mataimakin Shugaban Ƙasar, Teodoro Nguema Obiang Mangue, ya bayyana.

    Obiang, wanda kuma ɗa ne ga shugaban ƙasar, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya ce firaminista Manuel Osa Nsue Nsua ya miƙa takardar murabus ɗinsa da dukkan muƙarraban gwamnatin bayan sun kasa cika ko da kashi 10 cikin 100 na nauyin da aka ɗora musu.

    Bai fayyace waɗanne manufofi ne gwamnatin ta kasa cimma ba.

    Sai dai wata sanarwa daga jam'iyyar gwamnati ta PDGE ta fitar, ta ce shugaban ƙasar ya lura cewa gwamnatin ta gaza waje yaƙi da cin hanci da rashawa, sannan ba ta yi nasarar bunƙasa tattalin arzikin ƙasar ta hanyoyi daban-daban ba.

    Shugaba Obiang, wanda ya kwashe lokaci mafi tsawo yana mulki a duniya, ya jagoranci ƙasar mai arzikin man fetur tun daga shekarar 1979.

    A tsawon wannan lokaci ya ci gaba da naɗa 'yan uwansa da na kusa da shi a manyan muƙaman gwamnati.

    Shugaban ya naɗa gwamnatin da ta yi murabus ne a shekarar 2024, tare da Manuel Osa Nsue Nsua a matsayin firaminista.

    PDGE ta ce shugaban ƙasar bai gamsu da yadda gwamnatin da ta sauka ta gudanar da ayyukanta ba, kuma ana sa ran za a naɗa sabuwar gwamnati nan gaba kaɗan.

  9. Abu 14 da ke ƙunshe a yarjejeniyar da Iran da Amurka suka sanya wa hannu

    Da yammacin ranar Laraba ne shugaban Amurka, Donald Trump ya rattaɓa hannu kan yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran da za ta kawo ƙarshen yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.

    Donald Trump ya sanya hannu a kan yarjejeniyar ne a Faransa.

    Shi ma shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya saka hannu a kan yarjejeniyar ta hanyar intanet.

  10. An soke bikin sanya hannu kan yarjejeniyar Amurka da Iran a Geneva

    Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Ishaq Dar, ya ce an soke bikin sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran da aka shirya gudanarwa a Geneva da ke Switzerland ranar Juma'a

    Kamar yadda ya shaida wa BBC, an soke bikin ne saboda tuni an rattaba hannu kan yarjejeniyar ta hanyar sadarwa.

    Tun da farko wani babban jami'in gwamnatin Pakistan ya shaida wa BBC cewa Firaministan ƙasar, Shehbaz Sharif, ya dakatar da shirinsa na zuwa Geneva. Jami'in ya ce mataki na gaba zai gudana ne ta hanyar tattaunawa kan batutuwa daban-daban da yarjejeniyar ta ƙunsa.

    Pakistan ta ce yarjejeniyar da ka iya zama matakin farko na kawo ƙarshen yaƙin da ake tsakanin Amurka da Iran, za ta fara aiki nan take.

    Firaminista Shehbaz Sharif, ya ce Iran za ta buɗe mashigar Hormuz ba tare da ɓata lokaci ba, sannan kuma za a buɗe duk wasu tasoshin gaɓar ruwan Iran da Amurka ta rufe.

    Shugaba Trump ya ce ya sanya hannu kan jadawalin.

  11. Ebola ta kashe fiye da mutum 200 a DR Kongo

    Hukumar Lafiya ta tarayyar Afirka ta ce fiye da mutum 200 ne suka mutu sakamakon cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

    Har yanzu cutar na ci gaba da bazuwa zuwa yankunan ƙasar, duk da sanya idanu da ake ci gaba da yi a ƙasar.

    Jami'an lafiya sun ce akwai kusan mutum 800 da ake sa ran sun kamu da cutar a lardunan arewa maso gabashin ƙasar.

    Hukumomi na ci gaba da neman wata yarinya mai shekara shida da ke ɗauke da Ebola da aka ɗauak daga wani asibiti arewacin ƙasar.

  12. Amurka ta janye toshewar da take yi wa tasoshin ruwan Iran

    Sojojin ruwan Amurka sun janye daga toshewar da suke yi wa tasoshin ruwan Iran bayan da ƙasashen biyu suka sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi tsakaninsu.

    Tuni dai jiragen na Iran suka fara zirga-zirga bayan janyewar sojojin na Amurka.

    Bayanai daga manhajar da ke bibiyar sufurin jiragen ruwa ta ce wani jirgin ruwan Iran cike da mai da ya kai dubban gangunana ya fita daga da'irar tare da tsallakawa tekun Oman, kodayake ba a bayyana inda ya nufa ba.

  13. Taliban ta haramta wa ma'aikata zuwa aiki da manyan wayoyinsu

    Ma'aikatan gwamnati a Afghanistan sun shaida wa BBC cewa an haramta masu zuwa da manyan wayoyi wuraren ayyukansu.

    Hakan na zuwa ne bayan soma amfani da dokar haramta amfani da waya ga ma'aikatan soji da na gwamnati.

    Wasu daga cikin ma'aikatan sun ce an umarce su kada su yi amfani da wayoyinsu ko a gida.

    Wani jami'in gwamnatin Taliban ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da ma'aikatan sun yi aikin da ke gabansu maimakon latsa wayoyi.

    Sai dai masu sa ido na ganin cewa Taliban na ƙoƙarin ganin ta toshe duk wata hanya da wasu bayanai masu mahimmanci ka iya fita.

    Rahotanni sun ce an jiyo wani ɗan Taliban a cikin wani saƙon murya na shaida wa wani ma'aikacin gwamnati cewa duk wanda ya karya dokar za a gurfanar da shi gaban kotun sojoji.

  14. UAE ta kayyade wa yara shekarun amfani da shafukan sada zumunta

    Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ƙayyade shekarun amfani da shafukan sada zumunta a ƙasar domin hana ƙananan yara amfani da shafukan.

    Sabbin ƙa'idojin sun buƙaci kamfanonin sada zumunta su hana ƙananan yara amfani da shafukan.

    Za a bar ƙananan yara ƴan shekara 16 su yi amfani da shafukan ne bisa amincewar iyayensu.

    Kamfanonin sada zumuntar na da shekara ɗaya kafin aiwatar da hukuncin.

    Ƙasashe irin su Australia da Faransa da Birtaniya tuni suke da irin waɗannan dokoki.

  15. Jiragen ruwa sun fara wucewa ta mashigar Hormuz

    Manyan manhajojin da ke bibiyar sufurin jiragen ruwa sun ce aƙalla jirage huɗu sun wuce ta mashigar Hormuz bayan da Amurka da Iran suka sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi tsakaninsu.

    Jirgi na farko da ya fara wuicewa ta mashigin ɗauke da gas na ɗauke da tutar Faransa, daga nan sai uku da ke ɗauke da tutar Saudiyya.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar, Iran za ta buɗe mashigar Hormuz sannan Amurka za ta janye rufewar da take yi wa tasoshin ruwan Iran.

    Tun baya fara yaƙin, Iran ta rufe mashigar, wadda ta nan ne ake fitar da kashi 20 cikin 100 na man fetur ɗin duniya.

    Masana dai sun ce yaƙin ya fito da hatsarin dogara da hanya ɗaya wajen fitar da mai zuwa kasuwannin duniya.

  16. Babban sifeton ƴansandan Najeriya ya umarci ƙara jami'ai a makarantun Katsina

    Babban sifeton ƴansandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayar da umarnin ƙara ƙarfafa tsaro a makarantun jihar Katsina, a wani ɓangare na kare ɗalibai da malamai da kuma gine-ginen daga barazanar tsaro.

    Babban mataimakin sifeton ƴansandan mai lura da harkokin mulki da kuɗi, DIG Sulaiman Abdul ne ya bayyana haka lokacin wata ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai jihar, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    DIG Abdul ya ce an ɗora wa rundunar yansandan jihar alhakin ƙarfafa sanya idanu da yawaita sintiri a kusa da makarantun jihar, da ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri, da kuma ci gaba da kasancewar jami'an tsaro a harabar makarantun jihar.

    Ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin daƙile ayyukan ɓata-gari, da inganta ayyukan kai ɗaukin gaggawa, tare da tabbatar da cewa makarantun sun samu kariya, domin ci gaba da harkokin koyo da koyarwa.

    Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalar ƴanbindiga masu satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne tsohon babban janar ɗin sojin Najeriya ya mutu a hannun ƴanbindiga bayan kwashe kwanaki a hannunsu, tare da matarsa, kodayake daga baya jami'an tsaro sun kuɓbutar da matar.

  17. Farashin mai ya ci gaba da faɗuwa bayan cimma yarjejeniyar Amurka da Iran

    Farashin man fetur na ci gaba da sauka a kasuwannin duniya bayan Amurka da Iran ta sanya hannu kan yarjejeniyar cikin daren da ya gabata.

    Yarjejeniyar ta ƙunshi buɗe mashigar Hormuz, wadda ta kasance ɗaya daga cikin hanyoyin fitar da mai zuwa kasuwannin duniya.

    A farkon mako an riƙa sayar da gangar mai samfurin Brent kan dala 86.80, yayin da a yanzu ake sayar da shi kan dala 74.80

  18. Yarjejeniyar Amurka da Iran ta ƙunshi kawo ƙarshen hare-hare a Lebanon

    Saɗarar farko ta yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran ta ƙunshi cewa Amurka da ƙawayenta za su ayyana ''kawo ƙarshen ayyukan soji na dindindin cikin gaggawa'' a duka ɓangarori ciki har da Lebanon.

    Hare-haren Lebonon sun kasance wani ɓangare na yaƙin, yayin da Hezbollah mai samun goyon bayan Iran da Isra'ila ke zargin juna da karya yarjejeniyoyin tsagaita wuta.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei ya bayyana a shafinsa na Telegram cewa idan Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a Lebanon, Iran za ta ɗauki hakan a matsayin karya yarjejeniyar.

    Gidan talbijin na ƙasar ya ambato shi yana cewa ci gaba da kasancewar sojojin Isra'ila a Lebanon ka iya zama ''saɓa wa'' yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

  19. Japan na inganta ƙarfin sojin ƙasarta don hana ɓarkewar rikici

    Ministan Tsaron Japan ya shaida wa BBC cewa inganta ƙarfin sojin ƙasar na da matuƙar muhimmanci domin hana ɓarkewar yaƙi a yankin.

    Shinjiro Koizumi, ya ce dole ne ƙasar ta yi abin da ya dace da yadda yanayin tsaro yake a yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

    Ya ce ƙara ƙarfafa ɓangaren tsaro da kuma ƙarfafa alaƙar Japan da Amurka na daga cikin abin da ya kira dabarar kariya mai matakai daban-daban.

    A wani sauyi da ƙasar ta yi daga tsoffin manufofinta, a baya bayannan ne ta dage haramcin da aka shafe shekaru ana yi akan fitar da makamai zuwa ƙasashen waje.

  20. Labarai da dumi-dumi, An ji ƙarar harbe-harbe a babban filin jirgin saman Nijar

    Mazauna Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar sun bayyana jin ƙarar harbe-harbe a babban filin jirgin saman birnin.

    Lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe agogon ƙasar, kmar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato, yana mai cewa an shafe kusan sa'a guda ana jin ƙasar.

    An jin ƙarar harbe-harben daga ƙofar shiga filin jirgin, kamar yadda wasu shaidu biyu suka bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Jamhuriyar Nijar ta shafe fiye da shekara 10 tana fama da matsalar masu iƙirarin jihadi da ke kai hare-hare kan hukumomin ƙasar.

    Ko a watan Janairun wannan shekara ma masu iƙirarin jihadi sun kai wani harin a filin jirgin saman na Yamai, wanda ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kai shi.

    Kamar dai sauran makwabtanta Burkina Faso da Mali, Nijar na ƙarƙashin mulkin soji.