Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da ya tilasta matarsa saduwa da maza 120 ya ƙare a gidan yari
- Marubuci, Aleks Phillips
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Gargaɗi: Wannan labarin na ɗauke da wasu bayanai masu tayar da hankali ga wasu masu karatu.
Wata kotu a ƙasar Sweden ta yanke wa wani mutum mai shekaru 61 hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da watanni biyar a gidan yari bayan samunsa da laifin tilasta wa matarsa saduwa da maza fiye da 120.
Kotun ta ce mutumin ya riƙa sarrafa matar ne ta hanyar yi mata barazanar illata ta da kuma sanya kyamarorin tsaro domin bibiyar ta.
An same shi da laifuka da suka haɗa da yunƙurin fyade, taimakawa karuwanci ta ƙarfi, duka da kuma barazana da rayuwa.
An gudanar da shari'ar ne a garin Härnösand da ke gabashin gaɓar tekun Sweden. Bugu da ƙari, kotun ta samu wasu ƙarin mutum 28 da laifin biyan kuɗi domin yin jima'i da matar.
Lamarin ya ja hankalin duniya, inda wasu suka kwatanta shi da shari'ar Dominique Pelicot a Faransa, wanda aka samu da laifin ba wa tsohuwar matarsa, Gisèle Pelicot, miyagun ƙwayoyi tare da barin wasu maza suna yi mata fyade tsawon shekaru tara.
Mutumin, wanda ya fito daga yankin Ångermanland na Sweden, ya musanta aikata wani laifi. Ya shaida wa kotu cewa abin da ya yi kawai shi ne taimakawa wajen shirya ganawar da aka amince da ita tsakanin matar da sauran mutanen.
Sai dai kotun ta amince da hujjojin masu gabatar da ƙara, inda ta yanke cewa mutumin ya yi amfani da matar ba tare da tausayi ba domin cimma muradunsa.
Ba a bayyana sunayen mutumin ko matar ba.
Yadda ya riƙa tilasta wa matarsa yin jima'i da maza
Masu gabatar da ƙara sun ce mutumin ya fara tilasta wa matarsa saduwa da maza daban-daban domin karɓar kuɗi tun daga shekarar 2022. Maza daga wurare daban-daban na ƙasar Sweden kan je gidan gonarsu da ke wani wurin sirri a Kramfors domin aikata waɗannan ayyuka.
Ya ci gaba da aikata hakan har zuwa watan Oktoban 2025 lokacin da matar ta kai ƙara ga 'yan sanda.
A cewar masu gabatar da ƙara, mutumin ya riƙa ba matar miyagun ƙwayoyi a keɓantaccen wurin da suke zaune, inda ke da ƙarancin mutanen da take hulɗa da su da kuma kyamarorin da ya saka a gidansu domin juya rayuwarta yadda yake so. Wasu daga cikin kyamarorin ma kan ɗauki bidiyon saduwar da ake yi.
"Mutumin ya riƙa yi wa matar barazanar kashe ta, ya zuba mata fetur ya ƙonata da kuma yanke mata yatsu idan ba ta bi umarninsa ba," in ji su.
Rahotanni sun ce matar ta san wuraren da aka saka kyamarorin a gidan, kuma daga bisani ta samu damar tserewa ta wani wuri da kyamarorin ba sa iya ɗauka kafin ta kira 'yan sanda domin neman taimako.
Hukuncin da kotun ta yanke
Kotun ta yanke hukuncin cewa ta ce "mutumin ya yi amfani ƙwayoyi a kan matarsa tare da tilasta mata aikata wasu abubuwan da suka haɗa da yin amfani da sassan jikinta da kanta, kuma ya yaɗa su a intanet yana samun kuɗi da kuma yunƙurin jan ra'ayin maƙwabtansu da kwastomomi su yi jima'i da ita."
Kotun ta ce a lokuta da dama yana yin hakan ne ta hanyar "yawan matsa mata lamba da kuma amfani da kalamai marasa daɗi da wulaƙanci."
Kotun ta gano cewa shi ne ya yanke shawarar fara tallata yin jima'i da matar kuma shi ne yake gudanar da komai.
Sai dai kotun ta yi watsi da tuhume-tuhume takwas na fyade saboda ba ta samu isassun hujjojin da za su tabbatar da cewa matar ba ta amince da wasu daga cikin abubuwan da suka faru ba. Kotun ta kuma ce ba a iya tabbatar da irin ayyukan jima'in da suka gudana ba.
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun ce a ƙarƙashin dokokin Sweden, ana iya gurfanar da mutum kan laifin fyade idan har cin zarafin da ya aikata ya kai matsayin da yake daidai da yin jima'i.
Duk da haka, kotun ta same shi da laifin yunƙurin fyade a wata tuhuma guda, yayin da ta yi watsi da wasu tuhume-tuhume uku.
Baya ga hukuncin ɗaurin shekaru huɗu da watanni biyar, kotun ta umarci mutumin ya biya matar diyya ta kuɗi har krona dubu 200 na ƙasar Sweden, kwatankwacin fam 15,900 na Birtaniya.
Ko da yake hukumomin Sweden sun gano mutum 120 da suka yi hulɗa da saduwa da mutumin ke shirya wa matarsa, mutum 29 ne kawai aka gurfanar dangane da shari'ar.
Yawancin waɗanda ake zargin sun musanta tuhumar da ake musu, inda wasu suka ba su yi jima'i da matar ba wasu kuma ba su biya kuɗi domin aikata hakan ba.
Sai dai kotun ta samu mutum 28 daga cikinsu da laifin biyan kuɗi domin samun ayyukan jima'i har sau 56. An yanke wa mutum biyu daga cikinsu hukuncin ɗauri a gidan yari, yayin da sauran suka samu hukuncin ɗaurin talala da kuma gargaɗi.