Arsenal na son Rogers, Utd kuma Williams, Salah zai tafi Besiktas

Hoton Morgan Rogers

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Arsenal ta sanya ɗan wasan tsakiya na Ingila daga Aston Villa, Morgan Rogers, mai shekara 23, a matsayin babban wanda take son ɗauka domin ƙarfafa gabanta. Ana sa ran ƙungiyar za ta tuntuɓi Aston Villa kan cinikin, sai dai rahotanni sun nuna cewa farashinsa na iya haura fam miliyan 100. (Sky Sports)

Tsohon tauraron Liverpool kuma kyaftin ɗin ƙasar Masar, Mohamed Salah, mai shekara 34, na dab da kulla kwantiragi da kungiyar Besiktas ta Turkiyya, domin ci gaba da taka leda a can.(Foot Mercato)

Manchester United na nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gefe na Nottingham Forest kuma ɗan ƙasar Wales, Neco Williams, mai shekara 25, wanda ke iya taka leda a ɓangarorin hagu da dama. (Football Insider)

Real Madrid na sha'awar ɗan wasan gefe na Faransa, Michael Olise, mai shekara 24, na Bayern Munich, wanda rahotanni ke cewa yana da sha'awar komawa filin wasa na Santiago Bernabeu. (L'Equipe )

Tottenham Hotspur ta yi watsi da tayin fam miliyan 46 da Newcastle United ta gabatar domin sayen ɗan wasan tsakiya na Sweden, Lucas Bergvall, mai shekara 20.(Athletic - requires subscription)

A wani labarin kuma, Chelsea za ta biya fam miliyan 55 idan har tana son ɗaukar mai tsaron bayan Faransa na Crystal Palace, Maxence Lacroix, mai shekara 26, a wannan bazarar. (Times )

An mika sunan danwasan tsakiya na Guinea na kungiyar Celta Vigo, Ilaix Moriba, mai shekara 23, ga kungiyar Sunderland da Crystal Palace da Nottingham Forest da Aston Villa da kuma Hull City. Ana ganin zai iya tafiya kan kuɗin da ya kai yuro miliyan 20, kwatankwacin fam miliyan 17. (Nos Diario)

Bayern Munich ta bai wa ɗan wasan tsakiya na Portugal, Joao Palhinha, mai shekara 31, ƙarin lokaci kafin ya koma sansanin kungiyar, bayan da ya fito daga cikin shirye-shiryen kocinta Vincent Kompany. Aston Villa na daga cikin masu sha'awar ɗaukar shi. (Record via SportWitness)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tottenham kuma na son ɗaukar ɗan wasan gefe na Netherlands, Crysencio Summerville, mai shekara 24, daga West Ham United. Ana ganin ɗan wasan zai iya barin kulob ɗin bayan da West Ham ta fadi daga gasar Firemiya zuwa ta Championship. (Give Me Sport)

Yawan sababbin 'yan wasan da Tottenham ta ɗauka a wannan bazarar na nufin wasu za su fice daga ƙungiyar, kuma ana ganin mai tsaron bayan Argentina Cristian Romero, mai shekara 28, na daga cikin waɗanda za su iya tafiya. (Team Talk)

Manchester United da Newcastle United duk suna sha'awar ɗan wasan tsakiya na Sweden daga Eintracht Frankfurt, Hugo Larsson, mai shekara 22, sai dai har yanzu babu daya daga cikin kungiyoyin biyu da ta gabatar da tayi a kansa. (Bild)

Juventus ta miƙa tayin euro miliyan 6.5, kwatankwacin fam miliyan 5.5, domin sayen mai tsaron ragar Argentina na Aston Villa, Emiliano Martinez, mai shekara 33. Sai dai Aston Villa na neman yuro miliyan 12, kusan fam miliyan 10.2 ne (La Gazzetta dello Sport)

Juventus ce ke kan gaba wajen neman ɗan wasan gaba na Amurka daga Monaco, Folarin Balogun, mai shekara 25. Sai dai Borussia Dortmund da Sunderland su ma na nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan. (Mundo Deportivo)