Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sarautu biyar waɗanda asalinsu na bayi ne a ƙasar Hausa
- Marubuci, Khalifa Shehu Dokaji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
Bayin Sarki sun samo asali ne tun a lokacin mulkin Hausawa waɗanda ake kira Haɓe ko a Hausa.
Hanyar Mallakar bawa a masarautar Kano da sauran masarautu irin su Kebbin Argungu, ya haɗa da samun kyautar bawa, kamar yadda wasu sarakunan ko attajirai suke bayarwa, sai kuma yadda wasu masana tarihi ke cewar a ƙarni na 19 a ƙasar Kano ana yin samame domin kamo bayi.
An fara naɗa sarautun manyan bayin Sarki ne tun lokacin Sarkin Kano Ibrahim Dabo (1819-1846).
Kafin Musulunci, bayi a Kano ba su riƙe da wata sarauta, kawai dai suna nan a matsayin masu aikin bauta. Ba a fara sa bayin sarki a cikin muƙamai na tsarin mulki ba sai a cikin ƙarni na goma 15 a zamanin Sarkin Kano Muhammdu Rumfa 1463-1499.
Sai dai tuni da dama daga cikin wadannan sarautu sun koma hannun zuriyar sarakuna ko masu dangantaka da sarauta a kasar ta Hausa bayan shudewar al’adar mallakar bayi.
Rabe-Raben bayi a ƙasar Hausa
Masana tarihi irin su Kai-komon Makaman Kano, Ibrahim Hussain na cewa bayi sun kasu kashi biyu:
- Bayi na yau da kullum
- Bayi na amana
Ibrahim Hussain ya ce yadda ake mallakar bayi ya bambanta dangane da matsayin mai su a cikin al'umma.
Akwai bayi mallakin sarakuna, da bayi mallakin ƴan kasuwa, sai kuma bayi na gado.
'Zaman mutum bawan amana ko na yarda ba ƙasƙanci ne ba aminci ne, suna bambanta ne kawai da ƴaƴan Fulani masu sarauta saboda hidimar da suke yi musu na yau da kullum.
Bayi na haƙiƙa da kuma bayin yarda duk kuɗin goro ake yi musu, ana kiran su da bayi,' a cewar Kai komon Makaman Kano.
Haka nan su ma bayin Sarki na haƙiƙa sun kasu kashi biyu, akwai "bawa" akwai kuma "Bacucane".
Su Cucanawa bayi ne, kuma ƴaƴan bayi, waɗanda kuma ake gadarsu, saɓanin sauran bayin da su kuma ake mallakar su.
Haka kuma akwai bayin da suke na Sarki, waɗanda ke tsoma baki kan harkokin gududanarwa da suka shafi ayyukan bauta, yayin da sauran bayi kuwa ba su da wannan ikon.
Haka zalika suma a masarautu irin su Kebbin Argungu na da rabe-raben bayi irin na ƙasar Kano: waɗanda aka siyo, da waɗanda aka ciyo wajen yaƙi, sai waɗanda aka bayar a matsayin kyauta.
Alamun tantance bawa a ƙasar Hausa
Bayin Sarki a Masarautar Kano da wasu masarautun na ƙasar Hausa na siga ko alama.
Dr Raliya Zubairu malama a jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, ta ce a Kano, bayi na da tsagen uku-uku, wanda aka ƙirƙira a zamanin sarkin Kano Ibrahim Dabo a (1819-1846) don a bambance su da cucunawa da ƴaƴan sarki.
Sai dai kuma wasu na cewar a zamanin Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi (1855-1855) aka fara wannan tsagu. Bisa dukkan alamu babu wata majiya da ta tabbatar da faruwar tsagun 'yan uku-uku kafin zuwan Fulani.
Siga ta biyu ita ce ba a yi wa bayin Sarki laƙabi da "Malam", kamar yadda ake yi wa ƴaƴan Sarki, idan ka ji an ce Malam, to tabbas ɗan Sarki ne, ko ɗan malami amma ba bawa ba. a cewar Dr Raliya Zubairu.
Waɗanne sarautu ne aka ware wa bayi a ƙasar Hausa?
Galadima
A masarautu irin su Kebbin Argungu Galadima shi ne shugaban dukkan bayin da ake da su a masarautar, saɓanin sauran masarautu da ake bayar da ita ga ƴaƴan Sarki ko kuma wasu manyan ƙasa da ba bayi ba.
A cewar Mallam Yakubu El-Ibrahim, Walkin Kanta na Argungu ya ce 'Galadima shi ne shugaban dukkan bayi, kama daga siyensu, da kyautarsu, da komai da ake yi da su a masarautar Arugungu.
'Haka kuma ta hannun Galadiman ake neman kowacce irin sarauta da kayan da kowane basarake zai riƙa sanyawa, sannan shi ke kula da tsarin yadda za a yi hawa da kowane irin biki da za a gudanar,' a cewar Walkin na Kanta.
Har ila yau, ya ce Galadiman yana cikin ƴan majalisar sarki, kuma yana cikin masu zaɓen Sarki.
Kamar yadda sauran sarautu ke da hakimai shi ma Galadima na da hakimai a ƙarƙashin sa kamar haka:
- Magajin galadima
- Saraki (Shi ke kula da rawani/naɗin rawani, shigar hakimai, ko uban ƙasa)
- Wundi
- Walkin
- Dankadu
- Tulli, da sauran su
Shamaki
A bisa tsari Shamaki shi ne babba kuma shugaban duk wani bawan Sarki a ƙasar Kano. An fara wannan sarauta ne a shekara ta 1819, zamanin Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo.
Shamaki yana daga ɓangaren ƙofar Arewa shi ne wanda yake tsayawa a hannun daman Sarki idan ana tafiya a kan doki, sannan kuma a fada yana da wurin zama a gaban Sarki, daga dama kusa da limamai, sai dai babu wanda ke zama a wajen sa idan ba ya nan, sai dai idan har Sarki ne ya ce ya zauna.
A cewar Kai koman Makaman Kano, Ibrahim Husannin, 'Shamaki yana da ayyuka da yawa waɗanda suka ƙunshi 'kula da dukkan bayi maza waɗanda suke fada, tun daga kan ƴan aike, masu kula da shuke-shuke, masu shara, masu gadin ƙofa wato sarakunan ƙofofi), zuwa leburori', in ji shi.
Ya kuma ce Shamaki shi ne ke kula da Dawakin Sarki da kayan hawansu, da tsarin kayan mahayan dawakin.
A cewar wani masanin tarihi na masarautar Kano, Mallam Bello Mohammad Dambazau, kuma ma'aikaci a majalisar Sarakuna ta Kano, ya ce Shamaki shi ne ke kula da ayyukan da suka shafi gini ko ƙira ko dukanci.
"Idan aka samu giɓi a gurbin Sarki, shi ke riƙe dukkan kayan sarautar da sarki ke riƙewa, ya ajiye su, har sai an naɗa sabon sarki, kuma shi ke bayar da kayan naɗin Dagatai da Limamai duk da cewa su ba bayi ba ne, sannan shi ne ke kula da wani sashe na gandun Sarki - inda ake yi wa Sarki noma," a cewar Bello Mohammad Dambazau.
Wasu daga cikin hakiman Shamaki sun haɗa da:
- Chiroman Shamaki
- Babban Zagi
- Sarkin Dogarai
- Majasiddi
- Madakin Shamaki
- Makaman Shamaki
- Turakin Shamaki
- Jarman Shamaki
- Barden Shamaki
- Garkuwan Shamaki
- Malafa
- Barwan Shamaki
- Kenkendi
- Sarkin Hawa
- Jakadan Garko
- Sarkin Ruwa
- Sarkin Kofa70
- Sarkin Kiɗa
- Sarkin Busa
- Mai Dawakai, da sauransu
Ɗanrimi
Ɗanrimi shi ne na biyu a matsayi bayan Shamaki, a cikin bayin da ake da su a fada a zamanin Fulani a masarautar Kano. Gidan sarautar Ɗanrimi ya na daga ɓangaren ƙofar Arewa, shi ne wanda yake tsayawa a hannun hagun Sarki idan ana tafiya a ƙasa, ko a kan doki, sannan kuma a fada ya na da wurin zama a gaban Sarki.
A cewar Kai Komon Makaman Kano: 'Ɗanrimi na da ayyuka da suka ƙunshi jakadan sadarwa tsakanin fada da sauran wurare ko duniya, kafin zuwan Turawa, sai dai bayan zuwan Turawa Ɗanrimi shi ne jakadan sadarwa tsakanin Masarautar Kano da turawa masu gudanar da harkar mulki'.
"Shi ne kuma yake sanar da lokacin da Sarki zai yi hawa ta hanyar buga kugensa don sauran mahaya su sani, shi ne kuma a zamanin baya yake lura da ganuwar cikin birni da ganuwar gidan Sarki," a cewar Ibrahim Hussain.
Sannan ya ce Ɗanrimi idan an zo naɗa shi, Sarki ya na bayar da riga da alkyabba da rawani ɗan kura, amma hular da ake yi masa naɗin a kai haɓar kada ce ta yadin Ilaji, shi ya sa ake yi masa kirari da "Mai haɓar kada ta Ilaji".
Kamar dai shi ma yadda shamaki ke da hakaimai a ƙarƙshinsa, shi ma Ɗanrimi na da su kamar haka:
- Makaman Ɗanrimi
- Ɗansarai
- Galadiman Ɗanrimi
- Sarkin Tafarki
- Turakin Ɗanrimi
- Madakin Ɗanrimi
- Sarkin Tukurwa
- Sarkin Taushi
- Sarkin Bambaɗawa
- Sarkin Jauje
- Sarkin Kalangu
- Galadiman Lifida (mai Lema)
- Kwando
- Gawaji
- Kuge
- Tiridanda (Mai Tafari)
Wambai ko Wan bayi
Sarautar Wambai na daga cikin sarautu da asalinsu ta bayi ce. Ya na kuma daga cikin masu faɗa a ji da ke aiki kai tsaye da sarki a zamanin baya, kama daga masarautu irin su Kano da wasu da ke maƙwabtaka da ita, da ma irin su Kabbin Argungu.
A cewar Bello Mohammad Dambazau na majalisar sarakuna ta Kano, a baya Sarautar Wambai ana kiran ta 'Wan bayi', kuma yana kula da samarin bayi, da ake zaɓo su don ba su horon tafiya yaƙi, kuma suna zama ne ƙarƙashin majalisar sarki.
Sai dai kuma kamar yadda masanin tarihin nan Mallam Ibrahim Hussain ke cewa "bayan wasu zamunna sarautar ta tashi daga ta bayi ta koma ta ƴaƴan sarki, ko a ce Fulani, wanda har kawo yanzu tana cikin manyan sarautu a masarautu irin su Kano.
Shi ma Mallam Yakubu El-Ibrahim, Walkin Kanta ya ce Wambai ko Wan bayi, na ƙarƙashin Galadima ne wanda shi ne shugaban dukkan bayin da ke masarautar, kuma ya kasance shi ke kula da harkokin da suka shafi kula da sutura ko rawanin da wani hakimi ko uban ƙasa ya sa.
"Wambai shi ne ke kula da irin suturar da masu sarauta ke sawa, wanda idan mutum ya sa kaya saɓanin na masarautar, ko ya yi shigar da ta kai ta Sarki, shi ke umartarsa da ya sasauta ko ya koma shigar da aka ƙayyade masa.
Wanda yanzu wannan aikin nasa ne Saraki ya koma yi, bayan da sarautar ta bar hannun bayi, ta koma ga iyayen ƙasa ko ƴaƴan sarki," a cewar Walkin Kanta.
Sallama
Sallama shi ne na uku a matsayi, yana bin Ɗanrimi a masarautar Kano. A zamanin Fulani, Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ne ya fara naɗa sarautar.
Da fari dai ana yi mata laƙabi da Turakin Soro, kuma bayi ne da ake dandaƙewa ko fiɗiyewa ake bai wa sarautar. Saboda sarauta ce da ke sadar da sarki da cikin gida, wadda ta ƙunshi isar da saƙo tsakanin sarki da iyalinsa.
Sai dai a cewar Ibrahim Hussaini da yake yanzu babu irin waɗannan bayi da aka fiɗiye, masu lafiya ne ke riƙe da sarautar.
"Sallama yana tsayawa a bayan Sarki idan ana tafiya a ƙasa, ko a kan doki, sai dai ba shi da wurin zama a gaban Sarki," a cewar Ibrahim Hussaini, Kai komon Makaman Kano.
Har Ila yau masanin tarihin ya ce wasu daga cikin ayyukansa sun haɗa da sanar wa sarki waɗanda suke son ganin shi, waɗanda ba hakimai ba.
"Idan za a naɗa hakimi Sallama ne yake naɗa shi, kuma shi ne mai kula da kayan yaƙi wanda kuma har yanzu ma haka ne, bindigogi a hannunsa suke, ƙarƙashin kulawar Mai Tafari wanda hakimin gidansa ne," a cewar masanan tarihin.
Har wa yau, Sallama ne yake kula da dukkan kyaututtukan da Sarki yake yi wa baƙinsa da sauran jama'ar ƙasarsa.
Hakimansa Sun haɗa da:
- Sarkin Sayi
- Kilishi
- Galadiman Sallama
- Chiroman Sallama
- Barden Sallama
- Garkuwan Sallama
- Sarkin Fadar Sallama
- Sarkin Takubba
- Mabuɗi
- Mai Tafari
- Turakin Soro
- Magajin Ɗan Kana
- Sarkin gidan Sallama
- Galadiman Lufudda
- Sarkin Bagarmi
- Maikano ɗan Yura
- Lifidi
- Nalako