Arsenal na zawarcin Osimhen,Mourinho zai iya koma wa Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham ta nuna matukar sha'awar daukar dan wasan Manchester United Marcus Rashford, mai shekara 28, idan har suka kauce wa faduwa daga gasar firimiya bayan da Barcelona ta nuna shakkun mayar da dan wasan Ingila na dindindin wanda aka ba ta shi aro .(Sport - in Spanish), external
Akwai yuwuwar"dan wasan Ingila Anthony Gordon mai shekaru 25 ya bar Newcastle a bazara. (Athletic - subscription required), external
Chelsea ta tuntubi kocin Bournemouth mai barin gado Andoni Iraola kan mukamin kocinta.(Football London), external
Daraktan wasanni na Arsenal Andrea Berta ya je Istanbul a ranar Lahadi don kallon Galatasaray a yayin da ake rade-radin cewa Gunners na son dan wasan kungiyar da kuma Najeriya Victor Osimhen mai shekara 27. (AS - in Spanish), external
Jose Mourinho zai iya koma wa Real Madrid a matsayin kocinta a karo na biyu a lokacin bazara inda kocin na Benfica shi ne wanda shugaban kungiyar Florentino Perez ya fi so a cikin wadanda su ke zawarci (Athletic - subscription required), external
Liverpool na fatan dangantakar da ke tsakaninsu da RB Leipzig za ta taimaka mu su wajen siyan dan wasan Ivory Coast Yan Diomande mai shekaru 19 a farkon kasuwar musayar 'yan wasa ta bazara.(Football Insider), external
Har ila yau Liverpool na bibiyar dan wasan Napoli Sam Beukema, mai shekara 27, wanda kocin kungiyar Arne Slot ya dade yana so. (Teamtalk), external
Everton na shirin zawarcin dan wasan Manchester City Nathan Ake, mai shekara 31, a bazara yayin da dan wasan Netherlands ke neman karin lokacin wasa.(Football Insider), external
Newcastle da Aston Villa na sha'awar dan wasan Sporting da Uruguay Maxi Araujo,mai shekara 26. (Sport Witness), external
Dan wasan Feyenoord Ayase Ueda, mai shekara 27, ya shiga cikin jerin sunnayen 'yan wasa masu kai hari da Everton ke so a wannan bazara kuma Leeds da Tottenham da Brighton sun nuna su ma su na son dan kasar Japan . (Teamtalk), external
Valencia ta kosa dan wasan Belgium Largie Ramazani ya koma dan wasan dindindin daga Leeds bayan dan wasan mai shekara 25 da aka bada shi aro ya nuna kwazo sosai a gasar La liga .(ElDesmarque - in Spanish)














