Iyalan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir da ke tsare a hannun shukumar ICPC, sun yi zargin cewa jami'an hukumar sun hana su kai masa abinci.
Cikin wata sanarwa da ɗansa, Hon. Muhammed Bello El-Rufai ya fitar ya zargi jami'an hukumar da hana mahimman haƙƙoƙinsa na ɗan'adam.
''Tun da farko sun hana likitansa ganinsa domin su tattauna sakamakon gwajin lafiyar da ya yi masa, suna cewa wai dole sai sun samu takardar izini daga shugaban ICPC'', kamar yadad Bello El-Rufai ya bayyana.
Ita ma mai ɗakin El-Rufai, Aichatou El-Rufai wadda ta kai masa abincin, ta bayyana cikin wata hira da kafar yaɗa labaran DCL Hausa cewa jami'an hukumar sun hana ta shiga ofishin domin kai wa maigidan nata abincin.
''Kullum daidai wannan lokaci muke zuwa domin kawo masa abinci, amma yau ina zuwa suka ce wai ba zan shiga ba, an ba su sabuwar doka dakatar da kawo abinci daga ƙarfe 6:30 na yamma'', in ji shi.
Kawo yanzu babu wata sanarwa daga hukumar ta ICPC game da wannan zargi.
El-Rufai dai ya shafe watanni yana tsare a hannun hukumar - wadda ta kama shi bisa zargin aikata ba daidai ba, zargin da El-Rufai ya sha musanta.