Yadda ambaliyar ruwa ta fara ɓarna a arewacin Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ruwan sama mai tafe da iska mai karfi ya rusa gidaje fiye da 200 a yankin karamar hukumar Kusada a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Sannan akwai shaguna da dama da suka rushe, lamarin da ya janyo hasarar dukiya mai dimbin yawa. Babu wasu bayanai da ke nuna an samu asarar rayuka.

Ambaliyar ta ruguza gidajen jama'a da dama a garuruwan Janbango da Dangamau da kuma Kusada lamarin da ya bar iyalai da dama ba tare da matsuguni ba, baya ga rashin abinci da sutura.

Dama tuni hukumar kula da yanayi ta ƙasar Nimet ta yi gargadin cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a jihohi daban-daban na ƙasar a cikin watan Yuli.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, hukumar ta ce ruwan sama da aka samu a sassan ƙasar cikin watan Yuni ya sa ƙasa ta ɗuri ruwa sosai, kuma hakan zai rage yadda ƙasa ke tsotse ruwan sama da zai ci gaba da sauka a wannan wata.

Hukumar ta ce "saboda haka, yankunan da ke a wuri mai kwari da birane da wuraren da ke kusa da rafuka da kuma wuraren da babu isassun magudanan ruwa za su iya fuskantar ambaliyar ruwa a cikin kwanaki masu zuwa."

A shekarar da ta gabata an samu mummunar ambaliyar ruwa a jihar Neja da ke arewacin ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka masu ɗimbin yawa.

Daruruwan mutane sun rasa muhallansu a garin Dangamau, kamar yadda wani mazauni yankin ya shaida wa BBC.

Ya ce ruwa ne mai iska tare da ƙanƙara aka yi wanda ya haddasa rushewar gidaje.

"Akwai gidaje da dama da iska ya ƙware su, sannan kuma bangwaye sun zube," in ji shi.

Ya kara da cewa lamarin ya jefa al'ummar yankin cikin mawuyacin hali inda wasu kara suka samu suka yi danni, yayin da wasu kuma wadanda rufin kwanonsu ya kware sun nemi wasu gidajen na aro ko haya suka fake.

Tun a farkon watan Yuli hukumar kula da yanayi ta Najeriya (Nimet) ta yi gargaɗin cewa jihohin Najeriya za su fuskanci ambaliya tare da yin kira ga hukumomi su gaggauta daukar mataki.

Al'ummar Dangamau sun ce sun dade suna fuskantar irin wannan ambaliya a duk shekara sakamakon rashin ingantattun magudanan ruwa.

Mazauna yankin Janbango roki gwamnatin jihar Katsina da hukumomin da abin ya shafa su aiwatar da ingantattun matakan magance ambaliya ta hanyar samar da magudanan ruwa domin kare rayuka da dukiyoyi a lokacin damina.

Me hukumomi suka yi?

Shugaban ƙaramar hukumar Kusada, Hon. Sani Aminu Dangamau ya shaida wa BBC cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu domin ganin sun taimaka wa wadanda abin ya shafa.

A cewarsa, sun bayar da agajin gaggawa a matakin ƙaramar hukuma nan take bayan lamarin ya faru.

"Mun yi tanadin kwano da siminti wadanda za a ba wadanda lamarin ya shafa domin su gyara gidajensu," cewa Hon Sani Aminu.

Sai dai ya ce babu wani wuri da gwamnati ta ware domin tsugunnar da mutanen da matsalar ta shafa.

"Yawancin garin ƴan'uwan juna ne shi ya sa lamarin na faruwa suka taimaki junansu," in ji shi.

Mutanen sun shaidawa BBC cewa jami'an hukumar baayar da agajin gaggawa, NEMA sun bi gida-gida sun ɗauki sunayen waɗanda lamarin ya shafa domin ganin yadda za a taimake su.

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Ummaru Radda ya kai ziyarar gani da ido tare da jajantawa wadanda lamarin ya shafa, inda ya bada umarnin tantance girman ɓarnar domin soma taimakawa al'ummomin.

Jihar Katsina na cikin jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ambaliyar ruwa a ahasashen hukumar kula da yanayi ta Najeriya (Nimet).

Kuma yankunan da ke ciki kwari da wuraren da ke kusa da rafuka da kuma wuraren da babu isassun magudanan ruwa za su iya fuskantar ambaliyar ruwa.

Me ya sa ake yawan samun ambaliyar ruwa a Najeriya?

Jihohi da dama musamman na arewacin Najeriya sun sha fuskantar ambaliyar ruwa, da ke lakume rayuka da dukiya mai dimbin yawa.

Ambaliyar ta fi shafar garuruwan da ke kusa da manyan koguna a Najeriya.

A 2024 ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a jihar Borno inda ta mamaye gidaje da gonaki a birnin Maiduguri - ambaliya mafi muni da jihar ta gani cikin shekara 30.

An alakanta ambaliyar Maiduguri da ɓallewar madatsar ruwa ta Alau, kuma hukumomi sun ce daya daga cikin makwararar kogin ce ta ɓalle sakamakon tumbatsa.

Tumbatsar koguna a Najeriya sakamakon tafka ruwan sama kan haifar da ambaliyar ruwa da ke yin ta'adi.

Ruwan sama mai karfi yana daya daga cikin abubuwan da ke jawo tumbatsar koguna.

Yadda za ku kare kanku a lokacin ambaliya

Ƙwararru sun zayyana abubuwan da ya kamata a yi idan ambaliya ta faru:

  • Idan akwai barazana ga rayuwar wani ko wata, to a gagguta kiran lambobin agajin gaggawa domin samun ɗauki
  • Kada ku yi tafiya ko tuƙi cikin ruwan da yake ambaliya ko kuma neman shiga cikin ruwan domin tsallakewa. Ruwan yana zuwa da ƙarfin gaske ta yadda zai iya janye mota.
  • Kada a yi tafiya a kan katangar da ta kange rafi, ko kuma a gaɓar rafin
  • A guji duk wani abu da zai a shiga cikin ruwan da ke ambaliya domin kuwa zai iya yaɗa cutuka. Idan kuma har aka taɓa ruwn, to a gaggauta wanke hannu ko wajen da ruwan ya taɓa da ruwa mai tsafta
  • Kada a bari ƙananan yara su yi wasa a kusa da wajen da ake ambaliya