Sojojin Sudan sun ƙwace babbar hanyar Khartoum zuwa El-Obeid daga hannun RSF
Sojojin Sudan sun sanar da cewa sun sake ƙwace ikon babbar hanyar da ta haɗa birnin Khartoum da arewacin El-Obeid a jihar Kordofan, bayan kwana biyu ana gwabza kazamin faɗa da mayaƙan rundunar RSF.
Tun bayan ɓarkewar yaƙin basasar Sudan a watan Afrilun 2023, mayaƙan RSF ne ke iko da wannan babbar hanya mai tsawon kusan kilomita 350.
Mai magana da yawun sojojin Sudan ya ce dakarunsu sun kuma ƙwace iko da garuruwa da ƙauyuka da dama a yankin, yayin da mayaƙan RSF suka tsere daga wuraren.
Nasarar na zuwa ne yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke ci gaba da gargadin tabarbarewar halin jin ƙai a birnin El-Obeid, inda ta ce kusan fararen hula 500,000 ke cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren bama-bamai da jirage marasa matuƙa da RSF ke kai wa.
A wani rahoto kuma, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasta cewa sama da mutum 400,000 ne suka mutu tun bayan fara yaƙin Sudan, yayin da fiye da mutane miliyan 15 suka rasa muhallansu sakamakon rikicin.