Madrid ta sanar da farashin Vinicius, Ina Mo Salah zai tafi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Paris St-Germain na son fam miliyan 145 kan danwasanata na Faransa mai shekara 23 Bradley Barcola, wanda Arsenal da Liverpool ribibinsa. (Times - subscription)

Arsenal ba ta soma tattaunawa ba kan dauko danwasan gaba na Brazil Vinicius Jr, amma Real Madrid ta sanar da farashin danwasan fam miliyan 137 idan har za ta sayar da shi a wannan bazara. (Sport - in Spanish)

Arsenal a shirye take ta lale manyan kudi da ba ta taba yi ba a tarihi domin karabo Vinicius. (Mirror)

Abin da Vinicius ya sa a gaba shi ne sabunta kwangilar shi da Real Madrid. Saura shekara daya yarjejeniyarsa ta kawo karshe. (AS - in Spanish)

Arsenal na shirin hanzarta tattaunawa domin karbo danwasan tsakiya na Brazil Bruno Guimaraes. (TalkSport)

Guimaraes ya shaida wa wakilansa cewa yana son tantance makomarsa kafin karshen mako mai zuwa, ka ya koama atisaye da Newcastle a wasannin share fagen kaka. (TeamTalk)

Tottenham na kan gaba wajen bukatar danwasan gaba na Brazil Savinho, mai shekara 22 daga Manchester City. (Sun)

Real Madrid ta cimma matsaya tsakaninta da danwasan gaba na RB Leipzig da Ivory Coast Yan Diomande mai shekara 19. (Sky Sports)

Al-Hilal ta soma tattaunawa da danwasan gaba na Senegal Iliman Ndiaye, mai shekara 26 na Everton. (Fabrizio Romano)

Chelsea za ta nemi manyan kudi kan danwasanta na gaba na Portugal Pedro Neto, mai shekara 26, wanda Liverpool da Manchester City da wasu kuangiyoyin Saudiya ke ribibi. (Mail)

Besiktas na jiran amsa daga danwasan Masar Mohamed Salah, mai shekara 34, bayan ta sake taya danwasan wanda ya bayar Liverpool. (Mail)

Bournemouth ba ta son sayar da matashin danwasanta na Faransa Junior Kroupi, wanda Barcelona ke bukata. (Marca - in Spanish)

Fulham na son danwasan tsakiya na Argentina Franco Mastantuono idan har Real Madrid ta yanke shawarar bayar da shi aro . (AS - in Spanish)

Juventus na tattauanawa da Manchester United kan danwasan gaba na Joshua Zirkzee, mai shekara 25. (Gazzetta dello Sport - in Italian)