Ba za mu buɗe mashigar Hormuz ba sai an cika mana sharuɗɗa bakwai - Iran

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce Iran ba za kwashe tare da fitar da sinadarin Uranium daga ƙasar ba, amma akwai yiwuwar samun mafita kan taƙaddamar.
A wata hira da ya yi da jaridar gwamnatin Iran, lokacin da aka tambaye shi game da makomar kusan kilogram 400 na uranium da aka tace zuwa kaso 60 cikin ɗari, ya ce: “Ina ganin za a iya samun wata dabara da za ta warware wannan matsala.”
Araqchi ya jaddada cewa Iran na da matsaya biyu da ba za su bari a tsallaka ba: kada a fitar da kayan nukiliyar daga cikin ƙasar, da kuma amfani da uranium ɗin bisa ga bukatun Iran.
A cewarsa, masu shiga tsakani sun gabatar da wasu shawarwari daban-daban, kuma akwai wasu daga cikinsu da za a iya la’akari da su. Ya ƙara da cewa ba za a iya ware batun uranium daga sauran rikice-rikicen da ake tattaunawa a kansu ba, domin dole ne a yanke shawara a cikin cikakken ƙunshin yarjejeniya.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce buƙatar farko ta Tehran ita ce shugaban Amurka Donald Trump ya fito fili ya bayyana cewa yana son a cimma yarjejeniya, sannan Amurka ta ɗauki matakan amincewa domin Iran ta gamsu cewa Washington da gaske take wajen tattaunawar.
Ya jaddada cewa shirin kwana biyu na Iran na sake buɗe mashigin ruwa na Hormuz tare da fara tattaunawa har yanzu yana nan. A ƙarƙashin wannan shiri, Amurka za ta fara aiwatar da alƙawurran da Iran ke buƙata, sannan a ranar da ta biyo baya Tehran za ta buɗe mashigin Hormuz kuma za a iya fara tattaunawa.
Araqchi ya ce Iran na da sassauci dangane da lokacin aiwatar da shirin, amma dole ne a cika sharuɗɗa bakwai na Tehran kafin a bude mashigin Hormuz.
Ya kuma ce musayar sakonni tsakanin Iran da Amurka na ci gaba ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar da Pakistan, kuma Tehran na fatan cimma yarjejeniya da za ta hana sake barkewar yaki.
A gefe guda kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya ce a wani taron manema labarai da aka gudanar a Fadar White House ranar Juma’a cewa Iran na son yarjejeniya, amma ba ta shirya ta amince da yarjejeniyar da shi ke ganin za ta dace ba.
Ya kara da cewa: “Muna son yarjejeniya ta hakika, ba yarjejeniya ta bogi ba.”
