Ko matakan Tinubu na rage raɗaɗi na da alaƙa da siyasa?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A daidai lokacin da mutanen Najeriya ke ƙara bayyana ra'ayoyinsu mabambanta kan yanayin tattalin arzikin ƙasar, shugaban ƙasar ya ɓullo da wasu hanyoyi da matakai da ya ce za su rage raɗaɗin da ƴan ƙasar ke ciki.

Gwamnatin ta Tinubu ta shiya bai wa ma'aikatan gwamnati tallafin kuɗin sufuri na naira 70,000 duk wata har tsawon wata shida, lamarin da ya haifar da muhawara a tsakanin al'umma.

Wannan na zuwa ne makonni bayan gwamnatin ta fitar da wasu matakai guda huɗu da ta ce tallafi ne na wata uku.

Haka kuma akwai wani tallafin na rage farashin man fetur wanda shi kuma gwamnatin ta ayyana tare da wasu matakan guda uku da ta ce za ta ɗauka kuma ta ce za su rage raɗaɗi.

Sai dai duk waɗannan matakan suna zuwa ne a daidai lokacin da kakar zaɓen baɗi ta ɗauki harama, wanda hakan ya sa wasu ke ganin ai duk matakan suna da alaƙa da neman zaɓe.

Daga cikin manyan matakan da gwamnatin ta ɗauka akwai:

Sabbin hanyoyi 4 na wata ɗaya

A Oktoban 2026 gwamnatin Najeriya ta sanar da wani sabon mataki na rage wa jama'a raɗaɗin hauhawar farashin fetur.

Matakin, wanda zai yi aiki na tsawon kwana 30, zai bai wa masu sayen fetur a gidajen man mallakin NNPCL damar samun fetur a farashin mai rahusa domin, wanda gwamnatin ta ce ta yi domin rage yanayin da tashin farashin man ya jefa ƴan ƙasar.

A cewar ministan kuɗin Najeriya, Taiwo Oyedele, NNPCL ta amince ta haƙura da ribar da take samu daga dillancin fetur na tsawon kwana 30.

A taƙaice, idan NNPCL ta sayi ko ta shigo da fetur kan N1,300 a lita, za ta sayar wa masu amfani da shi a wannan farashin ko kusa da shi ba tare da ɗora ribar da take sakawa a baya ba.

Sauran matakan na wata huɗu su ne:

Kafa manyan ma'adinan fetur

Wani sabon tsari da gwamnati ta sanar shi ne kafa abin da ta kira National Strategic Fuel Reserve, wato manyan ma'adinan fetur na ƙasa.

Haɓaka aika saƙonni ta Post Office

Gwamnatin ta kuma ce za ta inganta tare da haɓaka amfani da wuraren aika saƙo na Post Office domin rage rage cunkoso ababen hawa da rage man da ake ƙonawa hanya.

Faɗaɗa amfani da CNG

Wata muhimmiyar hanyar da gwamnati ke ganin za ta taimaka wajen rage tasirin tsadar fetur ita ce ƙara yawan motocin da ke amfani da iskar gas ta CNG.

A cewar gwamnati, CNG na da araha sosai idan aka kwatanta da fetur, inda kuɗin amfani da shi ke iya zama ƙasa da na fetur da kashi 60 zuwa 70 cikin 100.

Matakai 6 na kwana 90

Haka kuma a ƙarshen watan Oktoba, gwamnatin ta amince da wani shirin tattalin arziki na gaggawa na tsawon kwana 90, wanda ake sa ran zai taimaka wajen rage tsadar rayuwa da kuma sauƙaƙa wa ƴan ƙasa wahalhalun tattalin arziki.

An amince da shirin ne a yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta a ranar 22 ga Oktoban 2026.

Matakan sun haɗa da:

  • Samar da abinci mai araha
  • Daidaita tsarin haraji
  • Kammala muhimman ayyukan raya ƙasa da ke da amfani kai tsaye ga jama'a
  • Magance matsalolin da ke hana masu zuba jari shigowa Najeriya
  • Bayar da tallafi ga gidaje da iyalai ta hanyoyin da gwamnati za ta sa ido a kansu
  • Kafa tsarin sa ido kan ayyukan gwamnati

Majalisar ta kuma amince da kafa wani tsarin sa ido na ƙasa da zai rika bibiyar ayyukan ci gaba a faɗin ƙasar.

A cewar Oyedele, gwamnati na fatan rage hauhawar farashin kaya da kuma ribar kuɗaɗen ruwa zuwa matakin da bai wuce kaso ɗaya ba nan da shekarar 2027.

70,000 na kuɗin mota na wata shida?

Shirin gwamnatin Najeriya na bai wa ma'aikatan gwamnati tallafin kuɗin sufuri na naira 70,000 duk wata har tsawon wata shida, ya tayar da muhawara kan yadda ake ƙoƙarin rage raɗaɗin matsin tattalin arzikin da jama'a ke fama da shi a faɗin ƙasar.

Gwamnatin ta sanar da hakan ne a ranar Talata bayan wani zama tsakanin wakilan gwamnati da na ƙungiyar Ƙwadogon ƙasar NLC.

Tallafin na zuwa ne a lokacin da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa ke ci gaba da ƙara wa ma'aikata da iyalansu nauyi, lamarin da ya sa ƙungiyoyin ƙwadago ke ta neman ƙarin matakan da za su sauƙaƙa musu halin da suke ciki.

Kodayake gwamnati ta ce manufar tallafin ita ce rage tasirin matsalolin tattalin arziki ga ma'aikata, wasu na ganin adadin kuɗin ba zai wadatar ba idan aka yi la'akari da yadda farashin abinci da sufuri da sauran muhimman buƙatun rayuwa ke ƙaruwa.