Shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa Makkah domin yi wa ƙasa addu'a
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Alhamis zuwa birnin Makkah da ke Masarautar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wannan tafiya za ta bai wa Shugaban Ƙasar damar gudanar da ayyukan ibada da kuma yi wa Najeriya addu'o'in samun zaman lafiya, haɗin kai, kwanciyar hankali da ci gaba mai ɗorewa.
Kafin barinsa Abuja, Shugaban ƙasar zai ƙaddamar da wasu kayan aiki da rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta saya domin ayyukanta. Za a gudanar da bikin ƙaddamarwar a sashen shugaban ƙasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai koma Najeriya mako mai zuwa bayan kammala wannan aikin ibada na ruhaniya.