AC Milan na sanya ido kan Fernandez, Trabzonspor ta dawo zawarcin Richarlison

Bruno Fernandes
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

AC Milan na sa ido kan yanayin da ɗan wasan tsakiya na Portugal, Bruno Fernandes, mai shekara 32 ke ciki, inda har yanzu bai cimma yarjejeniyar tsawaita kwantiragi da Manchester United ba. (Corriere dello Sport)

Trabzonspor ta sake nuna sha'awarta kan ɗan wasan gaba na Brazil, Richarlison, mai shekara 29, yayin da Tottenham ke neman kuɗi kimanin fam miliyan 10. (The i Paper)

Manchester United na shirin fafatawa da Tottenham wajen neman ɗan wasan gaba na Croatia, Igor Matanovic, mai shekara 23, wanda ke buga wa Freiburg wasa kuma ake kimanta darajarsa kan fam miliyan 50. (Goal)

Ɗan wasan tsakiya na Norway, Martin Odegaard, mai shekara 27, da ɗan wasan gaba na Jamus, Kai Havertz, mai shekara 27, sun kusa shiga cikin watanni 18 na ƙarshe na kwangilolinsu a Arsenal, amma har yanzu ba a fara tattaunawa da su kan batun tsawaita kwangilolin nasu ba. (Standard)

Juventus na ƙoƙarin ganin ta ɗauki Nick Woltemade, wanda ke buga wasa a Newcastle United a matsayin aro. Suna iya bayar da ɗan wasan gefe na Portugal, Francisco Conceicao mai shekara 23, a matsayin wani ɓangare na musayar ƴan wasa domin samun ɗan wasan gaba na Jamus mai shekara 24. (Gazzetta dello Sport)

Celtic ba ta da sha'awar ɗaukar Jack Grealish, mai shekara 31. A halin yanzu, wasu ƙungiyoyi da dama na sa ido kan tsohon ɗan wasan tsakiya mai kai hari na tawagar Ingila, wanda kwangilarsa da Manchester City za ta ƙare a lokacin bazara, kuma a yanzu yake buga wasa a Everton a matsayin aro. (Football Insider)

Ɗan wasan gefe na Nottingham Forest kuma ɗan ƙasar Ingila, Callum Hudson-Odoi mai shekara 26, na ɗaya daga cikin ƴan wasan da Roma za ta iya ƙoƙarin ɗauka a watan Janairu. (Teamtalk)

Ɗan wasan baya na Uruguay, Ronald Araujo mai shekara 27, ya bayyana cewa har ya yi sauri a yi tunanin sauya yarjejeniyar aron da ya sanya shi barin Barcelona zuwa Liverpool, ta zama ta dindindin. (Athletic)

Sai dai Barcelona ta bai wa Liverpool damar kammala yarjejeniyar sayen Araujo kan kudi £47m. (Mirror)

Ana sa ran ɗan wasan gaba na Tottenham, Mikey Moore, mai shekara 19, zai kammala abin da ya rage a kakar wasa ta bana a ƙungiyar Cologne; kasancewar babu wani tanadi a kwangilar ɗan wasan na tawagar Ingila ƴan ƙasa da shekara 21 (England U-21) da zai bai wa Tottenham damar dawo da shi gida kafin wa'adin ya ƙare. (Talksport)

Tottenham ta shiga sahun ƙungiyoyi irin su Juventus, da Como da Galatasaray wajen nuna sha'awar ɗaukar kyaftin ɗin tawagar ƙasar Turkiyya, Hakan Calhanoglu, mai shekara 32, yayin da ɗan wasan tsakiyar ke ci gaba da tattaunawa kan tsawaita kwangila da ƙungiyarsa ta yanzu, Inter Milan. (Tuttomercato)