Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhimman mutanen da za su jagoranci yaƙin zaɓen Tinubu na 2027
A daidai lokacin da siyasar Najeriya ta fara ɗaukar zafi bayan buɗe ƙofar yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027, shugaban kasar Bola Tinubu ya fitar da jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin sake zaɓensa a zaɓen mai zuwa.
A makon da ya gataba ne a hukumance aka fara yakin neman zabe, kamar yadda jadawalin zaben kasar, wanda hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato INEC ta tsara.
Jerin ya nuna cewa shugaban na Najeriya Bola Tinubu shi ne shugaban kwamitin, sannan mataimakinsa Kashim Shettima ne mataimaki na ɗaya, yayin da shugaban jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar Nentawe Yelwadta ke a matsayin mataimaki na biyu.
Daga nan ne kuma aka jero sauran manyan ƴan siyasa da aka ɗora wa alhakin jan ragamar ainahin ayyukan yaƙin neman zaɓen.
Abdul'aziz Yari:
A cikin jerin sunayen da aka fitar a safiyar Asabar, an naɗa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta Janar (DG) na kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC.
Abdul'aziz Abubakar Yari a halin yanzu sanata ne mai wakiltar Zamfara ta arewa a majalisar dattijan Najeriya.
Ya yi gwamnan jihar Zamfara daga shekarar 2011 zuwa 2019 kuma yana ɗaya daga cikin ƴan siyasar da suka ɗauki hankali bayan kafa gwamnatin Bola Tinubu a 2023, musamman a lokacin da ake fafutikar kafa jagorancin majalisar dokokin tarayya.
Waɗanda za su taimaka wa Yari a matsayinsa na darakta janar su ne:
- Godswill Akpabio - (Shugaban Majalisar dattawan Najeriya) - Mataimaki yankin Kudu I
- Sanata Bamidele Opeyemi - Mataimaki yankin Kudu II
- Mai Mala Buni (Gwamnan jihar Yobe) - Mataimaki a yankin Arewa I
- Tajuddeen Abbas (Shugaban majalisar wakilai) - Mataimaki yankin Arewa II
- Barau Jibril - Mataimaki yankin Arewa III
Sakatariyar yaƙin zaɓen
Muhimmin wuri a yakin zabe shi ne sakatariya, inda a wajen ne ake shirya yadda kamfe zai wakana, da kuma yadda za a tsara shiga zabe da tsare-tsaren samun nasara.
A wannan karon, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ke jam'iyyar mai mulki ta naɗa a matsayin sakataren kwamitin yaƙin zaɓen, inda zai yi aiki tare da sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman, wadanda za su kasance mataimakin sakatare da mataimakiyar sakatare.
Haka kuma a kwamitin an tsara wasu fitattun 'yan siyasa da dattawan jam'iyya da suka haɗa da Chief Bisi Akande, Chief Segun Osoba, Sanata Rochas Okorocha, Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Florence Ita Giwa a matsayin wadanda za su ba shugaban kasa kuma shugaban kwamitin, Bola Tinubu shawara kan harkokin yakin zaben.
Sanata Adams Oshiomhole zai jagoranci ɓangaren tattara magoya baya, yayin da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa zai kasance mataimakin Darakta Janar mai kula da harkokin gudanarwa.
Aikin shirya zabe
James Abiodun Faleke, wanda ya taka muhimmiyar rawa a kamfen ɗin APC na 2022/2023, zai sake kasancewa cikin kwamitin, a wannan karon a matsayin mataimakin Darakta Janar mai kula da tsare-tsaren zaɓe, daidaita ayyuka da sa ido kan gudanar da zaɓe.
Zai yi aiki ne tare da daraktocin shiyya daga sassan ƙasar shida, ciki har da Sanata Olushola Adeyeye a Kudu maso Yamma da Dr Ngozi Olejeme a Kudu maso Kudu da Sanata Uche Ekwunife a Kudu maso Gabas da Muntaqha Rabe a Arewa maso Yamma da Ahmed Muhammed Ketso a Arewa ta Tsakiya da Sanata Sani Danladi a Arewa maso Gabas.
Muiz Adeyemi Banire zai jagoranci sashen shari'a na kamfen, tare da Dr Liman Hassan da Babatunde Ogala a matsayin mataimakansa.
Gwamna Sheriff Oborevwori ne zai jagoranci kwamitin kudi, inda zai yi aiki da mataimaka irin su Gwamna Abubakar Usman Ododo da dan majalisa Abubakar Bichi da Tanimu Yakubu, sai kuma Gwamna Dapo Abiodun da zai jagoranci kwamitin tattara kudaden yakin zabe.
A ɓangaren yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a, Mohammed Idris Malagi ne zai kasance Daraktan da ke daidaita harkokin sashen, tare da Dele Alake, Bayo Onanuga da Lanre Issa-Onilu.
Haka kuma, Tunde Rahman, Sunday Dare, Daniel Bwala da Felix Morka za su kasance cikin masu taimakawa wajen jagorantar dabarun sadarwar kamfen.
Segun Dada zai sake jagorantar sashen kafofin sadarwa na zamani, kamar yadda ya yi a kamfen ɗin 2022, yayin da Solomon Arowolo zai kasance sakataren sashen.
Sai kuma Abdulaziz Abdulaziz wanda zai yi aiki tare da Temitope Ajay da Arabinrin Aderonke da Fredrick Nwabufor a matsayin sakatarorin kula da harkokin kafofin sadarwa na zamani.
An kuma naɗa Dele Alake a matsayin jagoran masu magana da yawun kamfen, tare da Alwan Hassan, Ayobami Oyalowo, Kemi Asekun-Shittu da Adamu Fanda.
Sauran wadanda aka nada sun ha da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda aka nada a matsayin daraktan tattara dattawan jam'iyya, da Sheikh Halliru Maraya wanda zai yi aiki a bangaren tattara malaman addini (Musulunci), sai Aliyu Magatakarda Wammako da zai jagoranci yankin arewa maso yamma a bangaren tattara dattawa.
APC da zaben 2027
A saƙon ga kwamitin, Shugaba Tinubu ya umarci mambobin kwamitin da su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da nasarar APC a zaɓen Janairu 2027.
Tinubu ya kuma ƙarfafa shugabannin sassa daban-daban da su tuntubi sauran 'yan jam'iyyar da ba a saka sunayensu cikin jerin farko ba, domin su ba da gudummawarsu wajen yaƙin neman zaɓen.
Shugaban ya ce gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta ɗauka a lokacin kamfen tare da sanya Najeriya kan hanyar ci gaban tattalin arziki. Ya kuma yi kira ga tawagar kamfen ɗin da ta bayyana wa jama'a abubuwan da gwamnatin ta cimma tare da neman ƙarin goyon baya.
APC ce dai ta shige gaba wajen fara kafa kwamitin yaƙin zaben, wanda hakan ya sa aka fara dakon kwamitocin zaben sauran jam'iyyun, musamman manyan jam'iyyun hamayya na kasar.