Kalmomin Turanci 10 da aka Hausantar da su a shafukan sada zumunta

    • Marubuci, Zulaiha Abubakar
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kowane yare an san shi da aron kalmomi ya mai da su nasa, ko kuma a ƙirƙiro sababbin kalmomi har su zama karɓaɓɓu, ana amfani da su a al'amuran yau da kullum.

A yanzu da muke cikin zamanin kimiyya da fasaha, wasu kalmomi suna da wahalar fassara kai tsaye, musamman zuwa harshen Hausa, ta yadda sai dai a yi kwatanci da su.

Masana harshen Hausa sun bayyana cewa saboda irin wannan salo ne aka fara Hausantar da wasu kalmomi domin taƙaita rubutu, sannan kuma hakan yana sa hira ta kasance cikin sauri.

Sauƙin sadarwa shi ma na daga cikin dalilan da suka sa aka rungumi kalmomin Turanci aka cusa su cikin Hausa.

Idan aka duba yadda yawancin manhajojin kafafen sada zumunta da wayoyin salula suke amfani da Turanci, za a fahimci yadda tasirin fasaha a wannan zamani shi ma ya taka muhimmiyar rawa wajen Hausantar da kalmomin Turanci.

A lokacin aikawa da saƙo ta wasu daga cikin manhajojin sada zumunta, kamar WhatsApp ko TikTok, mutane kan yi rubutu cikin sauri da taƙaice. Ko da kalma tana da tsawo, wannan yanayi ma ya haifar da Hausantar da kalmomin Turanci.

Me ya sa ake Hausantar da wasu kalmomin?

Farfesa Abdullah Uba Adamu, masanin harshen Hausa da al'adu a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, ''Matasa ne suka Hausantar da kalmomin Turanci domin isar da saƙonni cikin sauƙi.''

Ya ƙara da cewa Hausa ta jima tana aron kalmomi tana mayar da su nata, inda ya bayar da misalin kalmomi irin su gwamnati, asibiti da kamfani, waɗanda aka aro daga Turanci aka Hausantar da su.

Ya ce duk da cewa babu wata illa da irin wannan salo zai yi wa harshen Hausa, akwai masana da suke ganin ba daidai ba ne a Hausantar da kalmomin Turanci, alhali kuwa kowane harshe a duniya yana aron kalmomi ya mayar da su nasa.

''Kowane harshe kullum a cikin ɓacewa yake,'' in ji Farfesa Abdalla, wanda ya bayar da misalin cewa a yanzu idan aka ce ''masaki'', zai yi wahala a samu yaron da ya san abin da ake nufi, saboda yanzu an daina amfani da ƙwarya, sai roba ake amfani da ita a gidaje.

Kalmomi 10

Zuwa shafukan sada zumunta ya sa aka samu sabbin kalmomi da ake yawan amfani da su wajen sadarwa, waɗanda idan aka tsaya ana bayyana ma'anarsu dalla-dalla, zai iya ɗaukar lokaci.

Ita kanta kalmar Soshiyal Midiya ana amfani da ita a matsayin gajeriyar hanya ta faɗin shafukan sada zumunta.

Ga wasu kalmomin Turanci da 10 Farfesa Abdallah ya ce ana amfani da su a soshiyal midiya kuma aka Hausantar da su domin sauƙaƙa bayan da kuma yadda BBC ta gano yadda wasu ke fassara su idan suna son su rubuta su da Hausa.

1. Internet – Intanet

2. Browsing – Bincike

3. Share – Turawa/Aika

4. Like – Nuna sha'awa/So

5. Account – Asusu/Shafi/Akawun

6. Posting – Wallafawa/Buga

7. Comment – Sharhi/Tsokaci

8. Online – Shafukan yanar gizo

9. DM – Tura saƙo kai tsaye

10. Follow – Bibiya

Misali, maimakon a ce ''na tura saƙon kai tsaye gare shi'', ana cewa ''na yi masa DM''. Haka kuma ana iya cewa ''ku yi min like'', ''ka yi min follow'' ko ''ka yi share''.

Waɗannan kalmomi, duk da cewa asalinsu na Turanci ne, matasa sun sauya yadda ake furta ko amfani da su, ta yadda suka shiga cikin maganganun Hausa na yau da kullum, musamman a shafukan sada zumunta.

Wannan ya nuna yadda kalmomin suka samu gurbi a cikin Hausa da ake amfani da ita a kafafen sada zumunta.

Shin ko Hausa ta ƙarɓi irin waɗannan kalmomi?

Farfesa Abdalla Uba Adamu ya ce, ''Kalmomi irin su kotu, burodi, bulo, teburi, asibiti, kwamishina, burushi, tasha, gareji da fili duk kalmomin Hausa ne, amma daga Turanci aka samo su.''

Ya ce sun zama kalmomin Hausa, kuma ana amfani da su wajen samar da kyakkyawar jimla.

Ya bayar da misalin kalmomi irin su gwamnati, kwamishinoni da ciyamomi, wadanda asalinsu daga Turanci ne.

Farfesan ya ƙara da cewa idan aka duba yadda harshe yake yin aro, za a fahimci cewa kalmomin da aka aro kan zama 'yan gida.

Ya bayar da misalin kalmomin jaki, itace, teku da takobi, wadanda Hausa ta aro daga Azbinawa, yayin da kalmomin gele da agogo aka aro su daga Yarbanci.

Ya ce hatta Turanci yana aron kalmomi daga wasu harsuna, inda ya bayar da misalin kalmar mansion, wadda ke nufin katafaren gida, ya ce asalin kalmar daga Indiya ne.

Tasirin irin wannan salo a harshen Hausa

Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce abu ne mai kyau domin duk harshen ya aro kalma daga wani wuri shi ne da riba. Amma abinda ya ɓace ya ɓace kuma kowanne harshe na fuskantar ƙlubalen ɓacewa.

Ingausa tana da matukar tasiri a harsuna watau haɗa Turanci da Hausa ya yin aikawa da sako ko magana.

Farfesa Abdalla Uba Adamu ya ce duk da wannan ƙokari na Hausantar da kalmomin Turanci da matasa suka yi har yanzu akwai kalmomin da basu zu zo kansu ba kamar Podcast wataƙila saboda ba dandali ne na yau da kullum ba.