'Sama da mutum 100 aka sace a jihar Neja'
Sama da mutum 100 ne aka sace a hare-haren da aka kai wasu kauyuka da dama a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, kamar yadda ’yan sanda da mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Maharan, wadanda rahotanni suka ce suna sanye da kayan da suka yi kama da na sojoji, sun kai hari kan al’ummomin da ke karamar hukumar Borgu bayan sallar Juma’a.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya ce an kuma kashe mutane fiye da 40 a hare-haren da aka kai kauyukan Dekara, Gidan Zana, Sabon Gida da Masaka.
Ya ce hukumomi na zargin maharan ’yan bindiga ne kungiyoyin masu aikata laifuka da ke yin garkuwa da mutane da kuma wawure dukiyoyi domin neman kudin fansa a sassan Najeriya.
Mazauna yankin sun ce ’yan bindigar sun shiga Dekara bayan sallar Juma’a, inda suka tattara mutane tare da tafi da su cikin dazuzzukan da ke kusa, kafin daga bisani su wuce zuwa wasu kauyukan makwabta.
Wani dan majalisar yankin, Jafar Muhammad Shetiman Borgu, ya tabbatar wa BBC cewa an kai hare-haren.
Hare-haren sun zo ne a daidai lokacin da kungiyoyin dauke da makamai ke kara yawan ayyukansu a yankin Borgu, wanda ke da iyaka da jihohin Kebbi da Kwara, da kuma kasar Benin.
Wadannan sabbin hare-haren sun bambanta da wasu hare-haren sace mutane da aka kai a yankin a baya.
A farkon wannan watan, ’yan sanda sun ce an ceto mutum 145 bayan da aka sace su daga kauyuka hudu na Borgu Konkoso, Kasuwan-Daji, Tungan-Makeri da Shafachi.
Mutanen na cikin 308 da hukumomi suka ce an ceto a wani gagarumin samame na tsaro, ciki har da sama da mutane 160 da aka sace a jihar Kwara makwabciya.