Atiku ya buƙaci magoya bayan ADC su kwantar da hankalinsu bayan hukuncin kotu

Asalin hoton, Atiku/X
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci mambobin jam'iyyar ADC da sauran ƴan Najeriya su kwantar da hankalinsu bayan hukuncin klotun ɗaukaka ƙara kan shugabancin jam'iyyar.
A cikin wata sanarwa da kakakinsa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce saɓanin yadda wasu ke yaɗawa, hukuncin kotun bai soke zaɓen fidda gwani da jam'iyyar ADC ta gudanar domin tsayar da ƴan takararta a zaɓen 2027 ba.
Ya ce "abin da wasu ke yaɗawa cewa hukuncin ya kawo ƙarshen takarar shugaban ƙasa ta ADC wani yunƙuri ne na yaɗa bayanan da ba su dace ba domin raunana ƴan adawa da kuma ruɗar da ƴan Najeriya."
Atiku ya bayyana cewa hukuncin kotun ya shafi zaɓen shugabannin jam'iyyar a matakin ƙananan hukumomi ne da kuma wa'adin shugabannin kwamitocin riƙo na jihohi, ba zaɓen fidda gwani na tsayar da ƴan takara ba.
Atiku ya ce su na girmama hukuncin kotun, amma sun umarci lauyoyinsu da su ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli domin ta yanke hukunci na ƙarshe kan lamarin.
Ya kuma buƙaci magoya bayan ADC kada su karaya, inda ya ce "gwagwarmayar ceto Najeriya ba ta za ta ta'allaka kan hukuncin kotu guda ɗaya ba"

























