Ƴanwasan da suka fi tsada a premier league a bana

Premier
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ƙungiyoyin Premier sun karya tarihin cinikayyar ƴanwasa na kakar wasa ta bana, inda suka kashe kuɗi kimanin fam biliyan 3.49.

An kashe jimillar £506.5m a ranar ƙarshe ta kasuwar, wanda ƙari ne daga £391m a bara.

Jimillar kuɗin da aka kashe a lokacin hutun kakar wasa ya ninka fam biliyan 1.13 da ƙungiyoyi suka kashe shekara biyar da suka gabata, kuma hakan ya nuna cewa manyan ƙungiyoyin Ingila suna da ƙarfin da za su jawo hankalin ƙwararru, a cewar alƙaluman da Paul Macdonald, wanda ya kafa FootballTransfers.com, ya bayar wa BBC Sport.

An ci kasuwar uku daga cikin ƴanwasa 10 mafi tsada a tarihin ƙwallon ƙafa a wannan bazarar kuma dukkansu ƴanwasa ne na ƙungiyar Premier.

Ga fitattun cinikayyar ƴanwasa biyar da suka fi tsada a kasuwar hada-hadar ƴanwasa ta bazarar b

Fernandez - Man City

Manchester City ta saya Enzo Fernandez daga Chelsea kan fam miliyan 125, wanda shi ne mafi girman kuɗin da aka saya ɗan wasa a tarihin Birtaniya.

Ɗan wasan tsakiya na Argentina ya taɓa aiki tare da sabon kocin City, Enzo Maresca, lokacin da Maresca yake horar da Chelsea.

Ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar tare da kulob ɗin, inda ya ce: "Zan iya ƙoƙarina kamar yadda na saba a duk inda nake wasa, kuma zan ci gaba da yin hakan yanzu da na koma Manchester City."

Farashin Fernandez ya yi daidai da wanda Liverpool ta biya wajen sayen ɗan wasan gaba Alexander Isak daga Newcastle United a bara.

Haka kuma, wannan ya sa Manchester City ta kafa sabon tarihin Premier League na mafi yawan kuɗin da kulob ɗaya ya kashe a kasuwa ɗaya ta saye da sayar da ƴan wasa, inda ta kashe fam miliyan 458, ta karya tarihin Liverpool na fam miliyan 415 da ta kashe a bazarar da ta gabata.

Ɗan wasan mai shekara 25 ya zama ɗan wasa na farko a tarihin ƙwallon ƙafa da aka sayar da shi kan fiye da fam miliyan 100 sau biyu a rayuwarsa ta wasa.

A shekarar 2023, ya koma Chelsea daga Benfica kan kuɗi fam miliyan 106.8, wanda a lokacin shi ne mafi girman kuɗin cinikin ɗan wasa a tarihin Birtaniya.

Barcola - Liverpool

Liverpool ta saya ɗanwasan gaba na Faransa, Bradley Barcola, daga Paris Saint-Germain (PSG) kan kuɗi fam miliyan 123.

PSG da farko ta ƙiyasta darajar ɗan wasan mai shekara 23 kan fam miliyan 145, amma Liverpool ta biya fam miliyan 106 a matsayin kuɗin farko, tare da ƙarin fam miliyan 17 da za a iya biya idan wasu sharudda suka cika.

Barcola ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar, inda ya zama ɗan wasa na biyar da ya koma Anfield a wannan bazarar, bayan zuwan ɗan wasan gefe Victor Munoz da masu tsaron baya Jeremy Jacquet, Ronald Araujo, da Ifeanyi Ndukwe.

Da yake magana bayan kammala cinikin, Barcola ya ce: "An ɗauki lokaci mai tsawo, amma ina matuƙar farin ciki da na samu damar bugawa Liverpool wasa. Abin da nake so kawai shi ne in shiga fili in taka leda."

Barcola zai sanya riga mai lamba 29 a Anfield.

Kodayake ya fi son bugawa a matsayin ɗan wasan gefe na hagu, yana iya taka rawa a kusan dukkan matsayin harin gaba.

Rogers - Chelsea

Haka kuma Chelsea ta saya ɗanwasan tsakiya na Ingila, Morgan Rogers, daga Aston Villa kan kuɗin fam miliyan 117, wanda ya zama mafi tsada a tarihin kulob ɗin.

Ɗan wasan mai shekara 23 zai sanya hannu kan kwantiragin shekara shida a Stamford Bridge, tare da zaɓin ƙara shekara guda.

Rogers ya kuma zama mafi tsadar ɗan wasa a tarihin Chelsea, inda ya karya tarihin fam miliyan 107 da kulob ɗin ya kashe wajen sayen ɗan wasan Argentina Enzo Fernandez a shekarar 2023.

Wannan sauyin sheƙa ya zo ne yayin da sabon kocin Chelsea, Xabi Alonso, ke ƙoƙarin tsara da ƙarfafa tawagarsa kafin fara sabon kakar gasar Premier League.

Anderson - Man City

Anderson kuma ya koma ƙungiyar Manchester City ne a kan cinikin fam miliyan 116

Ɗanwasan tsakiya mai shekara 23, Elliot Anderson, ya kammala komawarsa Manchester City daga Nottingham Forest, inda ya sanya hannu kan kwantiragin da zai ci gaba har zuwa watan Yunin shekarar 2031.

Anderson ya bayyana cewa bai yi wata-wata ba lokacin da aka ba shi damar komawa ɗaya daga cikin manyan kulob ɗin duniya.

Ya ce: "A lokacin da na samu labarin cewa Manchester City na zawarcina, nan na nan na yanke shawarar ganin lamarin ya tabbata."

Anderson na ɗaya daga cikin manyan sababbin ƴanwasan da Manchester City ta ɗauka, yayin da kulob ɗin ke ƙoƙarin ƙarfafa tawagarta domin ci gaba da fafatawa a manyan gasa na cikin gida da na Turai.

Tonali - Tottenham

Ita ma Tottenham Hotspur ta karya tarihin sayen ɗanƙwallo mafi tsada da ta taɓa yi, bayan ta saya ɗanwasan tsakiya Sandro Tonali kan kuɗin da zai iya kaiwa fam miliyan 100.

A baya, Spurs ta gabatar da tayin kusan fam miliyan 80, amma Newcastle ta yi watsi da shi.

Sai daga baya kuma Tottenham ta amince da biyan fam miliyan 92.5 a matsayin kuɗin farko, tare da ƙarin fam miliyan 7.5 a matsayin ƙari idan wasu sharuɗɗa suka cika.

BBC Sport ta ruwaito a baya cewa kocin Tottenham, Roberto de Zerbi, ya daɗe yana sha'awar ɗan wasan na ƙasar Italiya.

De Zerbi ya fara nuna sha'awarsa ga ɗanwasan na Italiya tun lokacin da yake horar da Sassuolo shekaru da dama da suka gabata, lokacin da Tonali ke taka leda a gasar Serie A ta Italiya.