Arsenal na son Alvarez, Aston Villa na son Manzambi

Julian Alvarez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Julian Alvarez
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal na son ɗaukarAtletico Madrid da Arjantina Julain Alvarez. (Independent)

Aston Villa na ƙoƙarin kamala tattaunwa kan ɗan wasan Freiburg da Switzerland Johan Manzambi, da ya ke kan son komawa Newcastle. (Athletic - requires subscription)

Tsohon mai horar da ƴan wasan Manchester City, Pep Guardiola, na cikin jerin wadan da za su iya zama mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Italiya, bayan Poulo Maldini. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Bayern Munchi na da ƙarfin guiwar za su iya shawo kan ɗan wasan Ingila Harry Kane, don sanya hannu kan sabuwar yarjejinya tsawaita zamansa a ƙungiyar, duk da irin harin da manyan ƙungiyoyi turai ciki har da Real Madrid ke nunawa, na son daukar ɗan wasan. (TeamTalk)

Ɗan wasan bayan Sassuolo Tarik Muharemovic, na ci gaba da jan hankalin ƙungiyoyin da ke buga gasar Firimiya, inda Newcastle, da Sunderland, da Leeds sannan Bournemouth na son ɗaukar sa. (Corriere dello Sport via Football Italia)

Chelsea na son ɗaukar ɗan wasan Crystal Palace da Ingila Adam Wharton bayan Liverpool da Manchester United suka sasauta aniyar su na ɗaukar ɗan wasan. (Caught Offside)

Roma na son ɗan wasan Chelsea da Ajantina Alejandro Garnacho kuma suna son daukar ɗan wasan Belgium Diego Moreira, daga Strasbourg. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Celtic na son mai tsaron ragar Manchester United Radek Vitek, bayan rawar da ya taka a matsayin dan wasan aro da ya ke taka leda a Bristol a kakar wasannin da ta gabata. (Football Insider)

Atalanta na tattunawa da Ederson ka tsawita kwantarginsa, bayan komawarsa Manchester United ya fusknacin komawa baya. Har yanzu Newcastle na son dauko dan wasan Brzail ɗin. (L'Eco di Bergamo - in Italian)

Sunderland na son ɗauko ɗan wasan Roma Matias Soule, wanda hakan yasa zai zama ɗan wasan farko da za us dauka a wannan kaka. An sa masa farashin euro miliyan 35 (kwatankwacin fam miliyan 30). (Northern Echo)

Newcastle na tattunawa da Parma wajen ɗaukar mai tsaron ragar JapanZion Suzuki, yayin suke neman sabon mai tsaron raga. (Newcastle Chronicle)

Tottenham da Newcastle na son dan wasan Manchester City da Masar Omar Marmoush. (TeamTalk)