Trump ya isa Beijing don ganawa da Xi Jingpin
Shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin Beijing da ke China don halartar wani babban tsaro da shugaba Xi Jingpin.
Wannan ce ziyararsa ta farko cikin shekara 10 tun 2017.
A yayin ziyarar ta yini biyu, Trump zai tattauna da Shugaba Jinping kan batutuwa da dama kuma shugabannin biyu na fatan ziyarar za ta yauƙaƙa dangantaka tsakanin su.
Tun da farko an tsara Trump zai je Beijing ranar 31 ga watan Maris sai dai yaƙin Iran ya haifar da tsaiko na wata biyu.
A tsakiyar watan Maris, ƴan makonni kafin yaƙin ya ɓarke, Trump ya ɗage ganawar inda ya ce ya zama dole ya kasance a Amurka saboda yaƙin.
China - ɗaya daga cikin manyan magoya bayan Iran ta yi ta yin baya baya da batun ganawar sai dai a farkon makon nan, ƙasar ta tabbatar da cewa za a yi taron.