Zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu
Zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afrika ta Kudu
An wallafa
Ana ci gaba da gudanar da zanga‑zangar ƙyamar baƙi a sassa daban‑daban na Afirka ta Kudu, lamarin da ya sa aka jibge jami'an tsaro saboda fargabar rikice‑rikice.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya buƙaci masu zanga‑zangar su guji tashin hankali, yana mai jaddada cewa dole ne a gudanar da zanga‑zanga cikin lumana ba tare da tsoratarwa ba.
Zanga‑zangar na da alaƙa da wa'adin da wasu ƙungiyoyi suka bai wa baƙin da ba su da takaddar izinin zama cikin ƙasar da su fice.



