Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilai 8 da ke sa matasa sauya addini
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A farkon makon nan ne wani matashi ya fito a wani bidiyo yana cewa ya fice daga addinin Musulunci ya koma na Kirista, lamarin da ya ɗauki zafi tare da haifar da zazzafar muhawara.
Kafin nan ma an samu matasa musamman daga kudancin Najeriya da suke fitowa a soshiyal midiya suna ayyana sauya addini daga Kirista zuwa Musulunci.
Bugu da ƙari, matasa da dama a ɓoye da fili suna sanar da ficewa daga addinansu na asali walau na Musulunci ko na Kirista zuwa aƙidar rashin yadda da kasancewar ubangiji da ake kira "Etheism" a turance.
Shin ko mene ne dalilin da ke sa matasan sauyawa daga addinin da aka haife su zuwa wani addinin ko kuma wata aƙida?
A wata tattaunawa da BBC, Aliyu Samba ɗan jarida kuma mai bincike kan harkokin rayuwa da zamantakewa musamman kan matasa ya yi nuni da wasu dalilai guda takwas.
Ƙarancin ilimin addini mai zurfi
Wani babban dalili shi ne yadda ake koyar da addini ga yara da matasa. A wasu lokuta, an fi mayar da hankali kan haddace abin da aka koya musu fiye da fahimtar dalilin da ya sa aka koyar da shi.
"Da yawa za ka ga matasa sun taso suna karatun ta hanyar haddace abin da suke koya ba tare da samun damar tambayar mene ne wannan abin da ake koya musu ba," in ji Aliyu Samba.
Ya ce matsalar kan bayyana ne lokacin da matashi ya shiga jami'a, ya fara karatun falsafa ko kimiyya, ko kuma ya shiga intanet ya ci karo da tambayoyi masu zurfi game da Allah, halittar duniya, ƙaddara, wahala, nagarta da mugunta, da sauran batutuwan falsafa.
"Idan bai samu wanda zai amsa waɗannan tambayoyin cikin hikima da fahimta ba, tambayar na iya rikiɗewa zuwa shakku, daga shakku kuma zuwa nisantar addini," in ji Samba.
Intanet
Intanet ta sauya yadda matasa ke samun ilimi. A baya, matashi zai dogaro ne da iyaye da malami da makaranta ko wata cibiyar addini domin samun ilimin addini da rayuwa.
Amma yanzu kuwa, a cikin 'yan mintuna kaɗan zai iya sauraron malamin addini, mai sukar addini, masanin falsafa da masanin kimiyya.
Aliyu Samba ya ce: "Yanzu kuma yana iya kallon malamin da ke karantar da addini da wanda yake ilhadi a lokaci guda, kuma ya kalli masanin falsafa da masanin kimiyya."
Samba ya ce ba yana nufin intanet tana tilasta mutane su zama marasa addini ba ne, inda ya fayyace cewa intanet tana iya taimaka wa mutum ya sami ƙarin ilimi na addini.
Ya yi bayanin cewa intanet tana ba matashi damar kwatanta ra'ayoyi daban-daban cikin sauri, kuma hakan na iya sawa ya riƙa tambayar wasu abubuwan da yawa da zai buƙaci amsoshinsu.
Wani bincike na 2026 da ya yi nazari kan matasan Najeriya ya nuna cewa kafafen sada zumunta suna ƙara zama muhimmiyar hanya da matasa ke mu'amala da ra'ayoyin addini, ciki har da batun barin addini.
Rashin samun amsoshi
Aliyu ya ƙara da cewa wasu matasa suna fara tambayoyi masu wahala da suke saka su a ruɗu.
Ya ce a duk lokacin da matashi ya fara tambayoyi ko tunani kan addini da kimiyya da falsafa, yana buƙatar amsoshi ne gamsassu na hikima da za su iya gamsar da shi abin da yake tunani ba haka ba ne.
A cewar Aliyu Samba, matsalar ba wai tambayar ba ce, rashin samun amsar da za ta gamsar da mai tambayar ne matsalar.
Ya ce: "Idan matashi ya yi tambayar nan bai samu amsa ba, sai a ce shaidan ne yake jefa masa shakku."
Ya ce a wasu lokuta, wannan amsar ba ta warware matsalar. "Wasu daga cikin irin waɗannan tambayoyi suna buƙatar ilimin falsafa, hikima ne domin gamsar da masu tambaya."
Ɗan jaridar ya ce wata matsalar ita ce, "Matashi na iya ganin malami, fasto ko wani shugaban addini yana koyar da gaskiya da adalci, amma daga baya ya ga yana aikata abin da ya saɓa da abin da yake wa'azi. Wannan na iya sa matashin ya fara tambayar sahihancin abin da aka koya masa."
Rashin adalci, wahala da matsalolin rayuwa
Talauci, rashin aikin yi da rashin adalci su ma na iya shafar yadda matashi yake kallon addini.
Matashi da yake rayuwa cikin tsananin talauci ko rashin aikin yi na iya tambaya: Ina addini yake a cikin wannan matsalar? Me ya sa ake fama da irin wannan rashin adalci?
Aliyu Samba ya ce, "Idan aka ba shi amsa mai taƙaita komai da cewa "ƙaddara ce" ba tare da ƙarin bayani ba na abin da addini yake buƙatar al'umma ta yi ba, ba dole ba ne ya gamsu,."
Saɓanin malamai a cikin addinai
Matashi na iya samun kansa cikin ruɗani idan ya ji malami ɗaya ya ce abu kaza haram ne, wani ya ce halal ne; wani ya ce wata ƙungiya kafira ce, wani kuma ya ce ba haka ba ne.
Aliyu Samba ya ce idan babu isasshen ilimi da zai taimaka masa ya fahimci dalilin wannan saɓanin, zai iya ɗauka cewa addinin kansa ne yake da matsala.
Matsalar tana ƙara tsananta idan kowanne bangare yana gabatar da kansa a matsayin shi kaɗai yake da gaskiya, ba tare da koya wa matashi yadda ake bambance abin da yake tabbatacce da abin da yake akasin haka ba.
Salon wa'azin da bai dace da matasa ba
Matasa suna rayuwa a wani zamani daban da na iyayensu. Suna amfani da YouTube, TikTok, podcasts, X, Facebook da sauran kafafen sadarwa wajen samun bayanai ne a yanzu.
Wannan ya sa Aliyu Samba yake da fahimtar cewa idan ana son isar da ilimin addini ga matasa, salon koyarwa ma yana da muhimmanci. Ba wai dole ne a sauya koyarwar addini ba, amma ana iya sauya yadda ake gabatar da ita.
Aliyu Samba ya yi nuni da cewa idan ilimin da zai taimaka wajen warware shubuhohi yana nan ne kawai a tsohuwar hanyar koyarwa, amma ba a kawo shi inda matasa suke ba, to wasu matasa ba za su same shi ba.
Wannan batu ya samu goyon baya daga binciken da aka yi a Najeriya kan yadda cibiyoyin addini ke amfani da kafafen yaɗa labarai wajen isa ga matasa. Binciken ya nuna cewa intanet ta zama muhimmiyar hanya ta sadarwa da matasa da kuma yada koyarwar addini.
Haɗuwar falsafa da ilimin zamani
Jami'a, intanet da sauran hanyoyin samun ilimi suna gabatar da matashi ga tambayoyi da ra'ayoyi da dama waɗanda wataƙila bai taɓa cin karo da su ba a lokacin baya.
Wannan ba yana nufin falsafa ko kimiyya ne suke sa mutum ya bar addini kai tsaye ba. A wasu lokuta ma, suna iya ƙarfafa imani. Amma suna iya sa mutum ya sake binciken abin da ya gada daga iyaye da kakanni.
Wani lokaci dangantakar matashi da addini tana iya lalacewa saboda abin da ya faru tsakanin shi da iyaye, malamai ko makaranta.
Misali, idan aka yi masa abin da ya ɗauka a matsayin zalunci ko raini da sunan addini, yana iya fara alaƙanta abin da aka yi masa da addinin kansa.
Wannan yana da muhimmanci domin mutum ba ya koyon addini daga littafi kawai; yana kuma koyonsa ne daga mutanen da yake ganin suna wakiltar addinin. Idan abin da yake gani daga gare su ya ci karo da abin da ake koya masa, hakan na iya haifar da ruɗu a zuciyarsa.
Aikata laifuka da sunan addini
Wani babban abin da zai iya jefa matashi cikin shakku shi ne ganin mutane suna aikata munanan abubuwa da sunan addini.
Aliyu Samba ya ce matashi da aka koya wa cewa rayuwar ɗan'Adam tana da daraja zai iya kasa fahimtar yadda ake iya kashe mutum saboda bambancin addini, ra'ayi ko ƙungiya, musamman idan masu aikata hakan suna ikirarin cewa suna yi ne domin Allah.
Wannan na iya haifar da tambaya mai zurfi: Idan addini yana koyar da adalci da tausayi, ta yaya ake samun irin wannan tashin hankali da sunan addini?
Samba ya nuna cewa irin wannan rikici tsakanin abin da addini yake koyarwa da abin da wasu masu addini suke aikatawa na iya sa wasu matasa su sake duba matsayinsu na addini.
Yana da muhimmanci a bambanta tsakanin barin addini, sauya addini, canza mazhaba ko ƙungiyar addini, da kuma zama ba tare da addini ba. Ba dukkan waɗannan abubuwa ne suke da ma'ana ɗaya ba.
Binciken Pew Research Center na 2025 kan sauyin addini a ƙasashe 36 ya nuna cewa a Najeriya sauyin addini a tsakanin manya ya kasance ƙasa sosai idan aka kwatanta da wasu ƙasashe: kashi 95% ko fiye na manyan Najeriya sun ce har yanzu suna cikin addinin da suka tashi a kai.
Wannan yana nuna cewa, duk da cewa akwai mutane da ke sauya matsayinsu na addini, lamarin bai kai a ce ya mamaye Najeriya ba.
A ƙarshe, Aliyu Samba ya bayyana cewa lamarin na faruwa ne ta hanyar wani tsari da ya taƙaice:
Tambaya → shakku → neman amsa → rashin samun amsa → takaici → nisantar addini → sabon tunani → karɓar sabon matsayi na aƙida.
Sai dai wannan ba dole ne hakan ya faru ga kowane mutum ba, domin wani matashi zai yi tambaya ya samu amsa, shakkunsa ya ragu ko ya kau, sannan kuma imaninsa ya ƙara ƙarfi.
Hakan ke nufin cewa tambayar ba matsala ba ce, wataƙila yadda amsoshin suka zo ya fi tasiri a kan tambayar.