Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ministan Indiya mabiyin addinin Hindu da ya yabi Musulunci ya tayar da ƙura
Sa'ilin da yake jawabi a wani taro ranar Lahadi a jihar Karnataka ta ƙasar Indiya, ministan ilimi mai zurfi na ƙasar Roy Reddy ya yaba wa Musulunci, inda ya bayyana shi a matsayin "addini mai kyau."
Sai dai kalaman nasa sun tayar da ƙura a siyasance.
Jam'iyyar ƴan kishin addinin Hindu ta BJP ta buƙaci a kori ministan daga aiki ko kuma ya nemi afuwa kan kalaman nasa, musamman ga mabiya Hindu.
Daga baya Reddy ya yi ƙarin haske kan kalaman nasa, inda ya ce: "Mece ce matsalar game da abin da na ce? Kawai na ce ne Musulunci na da koyarwa mai kyau. Ban ce ya fi wasu addinan ba."
Sai dai jagoran jam'iyyar BJP, R Ashok ya buƙaci a tursasa wa Roy Reddy ya janye kalamansa tare da neman afuwa ga mabiya addinin Hindu, saboda a cewarsa kalaman ba su yi musu daɗi ba.
Abin da Roy Reddy ya faɗa
Lokacin da yake yi wa mutane jawabi a garin Kokanor da ke gundumar Koppal, Roy Reddy ya ce: "Ina so na faɗa muku cewa Musulunci addini ne mai matuƙar kyawu idan aka kwatanta da sauran addinai. Yana tausaya wa ɗan'adam."
Ya ƙara da cewa: "Ba na zuwa wuraren ibada, to amma zan so na samu damar zuwa aikin hajji koda sau ɗaya ne a rayuwata."
Duk da muhawarar da kalamansa suka haifar a fagen siyasar ƙasar, da alama ministan ya dage kan matsayarsa.
Da ya yi ƙarin bayani kan kalaman nasa, ya ce: "Idan na ce Musulunci addini ne na ƙwara, mene ne laifin hakan?"
'Ka nemi afuwa ga masu bin addinin Hindu'
A cikin wani rahoton jaridar 'The Deccan Chronicle', Ashok ya ce idan har Roy Reddy ya ƙi neman afuwa kan kalamansa, ya kamata babban ministan jihar, DK Shivakumar ya sauke ministan daga kan muƙaminsa.
Ashok ya ce a yanzu an fara gane ainihin manufar jam'iyyar Congress Party da siyasarta.
Ya ce jam'iyyar BJP ba za ta lamunci duk wani abu da zai nuna rashin girmamawa ga mabiya Hindu ba, kawai domin siyasa.
Lokacin da ya mayar da martani, shugaban jam'iyyar BJP na jihar kuma ɗan majalisar dokoki, BY Vijender ya ce: "Wadannan kalamai za su zama matsala ga Roy Reddy a nan gaba."
Vijender ya yi wa Reddy gatse cewa idan da gaske abin da Reddy ke so kenan, sai ya Musulunta ya yi hijira zuwa Makka."
Jagoran jam'iyyar BJP Mahesh Tanjakai ya ce: "Wannan babban abin kunya ne a ce mutumin da ke bin addinin Hindu zai yi irin wannan kalami."
Ya ƙara da cewa: "Abin da ya faɗa kuskure ne gaba ɗaya. Jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) ta yi Allah wadai da wannan kalami nasa kuma ya kamata Roy Reddy ya sauya matsayarsa."
Ya ƙara da cewa: "Idan kana son Musulunci to ka tafi. Tafiyarka ba za ta yi wa mabiya Hindu illa ba."
Wane ne Basavaraj Roy Reddy?
Roy Reddy minista ne kuma ɗan majalisa mai wakiltar gundumar Yelabuga da ke yankin Koppal. An zaɓe shi har sau shida.
A baya ya riƙe muƙamin ministan ilimi mai zurfi da ministan gidaje.
Ya fito ne daga al'ummar Lingayat kuma yana goyon bayan amincewa da addinin Lingaya, a matsayin addini mai zaman kansa daga addinin Hindu.