Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa na 31 Agusta zuwa 6 Satumba 2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 31 ga watan Agusta zuwa 6 ga watan Satumba 2026.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Mohammed, Haruna Kakangi, Buhari Fagge

  1. Valencia na son ɗaukar aron Elliott daga Liverpool

    Valencia na tattaunawa da Liverpool kan ɗaukar Harvey Elliott a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasan bana.

    Ɗan wasan mai shekara 23 ya kamala kakar wasa ta bara a matsayin aro a Aston Villa amma wasa ɗaya kacal ya buga a gasar Premier.

    Valencia, wadda ta ƙare a matsayi na tara a gasar La Liga a kakar wasa da ta gabata kuma ba ta cancanci shiga gasar Turai ba, tana aiki don nemo hanyar da za ta dace don tabbatar da yarjejeniyar.

    Ƙungiyar ta Spain tana son Liverpool ta biya rabin albashin ɗan wasan.

    Elliott ya yi wasa akai-akai a lokacin wasannin share fage na fuskantar kakar bana a ƙarƙashin sabon kocin Andoni Iraola amma daga baya an cire shi daga cikin wasanni biyu na farko na Premier League na ƙungiyar.

  2. Munoz ya koma Nottingham Forest daga Crystal Palace

    Nottingham Forest ta kammala cinikin daukar dan wasa Daniel Munoz daga Crystal Palace kan kudi £22m.

    Ɗan wasan bayan na gefen dama, wanda ɗan ƙasar Colombia ne, zai sake haɗuwa da koci Oliver Glasner a filin wasan City Ground, bayan sun lashe kofin FA da kuma Conference League tare a kungiyar Palace.

    Ya rattaba hannu kan kwantiragin shekara uku bayan ya shafe shekaru biyu da rabi a Selhurst Park, inda ya zura ƙwallaye 11 a wasanni 109 da ya buga.

    Munoz ya bi sahun Liam Delap, wanda aka ɗauko kan kuɗi £50m, kuma yana iya fara buga wa ƙungiyar wasa a karawar da za ta yi da Tottenham Hotspur a gasar Premier ranar Asabar mai zuwa.

    Munoz, wanda ya buga wa ƙasarsa wasanni 51, ya kuma taimaka wa Palace wajen lashe kofin Community Shield a shekarar 2025.

  3. Manchester City ta kammala ɗaukar Allan daga Palmeiras

    Manchester City ta kamala daukar dan wasan gefe Allan Elias daga Palmeiras kan yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 34.

    A tashin farko dai City ta biya fam miliyan 32 a kan dan wasan na Brazil mai shekara 22, tare da karin fam miliyan 2.2 idan aka cika wasu sharudda, ya kuma rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyar.

    Allan ya zo ne domin ya maye gurbin takwaransa dan kasar Brazil, Savio, wanda ya kammala komawa Tottenham Hotspur kan fam miliyan 75 a makon da ya gabata.

    Dan wasan mai buga gefen dama ya zura kwallaye tara tare da taimakawa aka ci wasu guda 12 a wasanni 96 da ya buga a dukkan gasanni da kungiyar Palmeiras.

    Allan shi ne sabon dan wasan da aka kara a tawagar Enzo Maresca a wannan bazarar.

    Ya zuwa yanu dai City ta kashe sama da fam miliyan 230 a wannan bazarar, inda ta dauki Elliot Anderson daga Nottingham Forest kan fam miliyan 116 da kuma Ayyoub Bouaddi daga Lille kan fam miliyan 85.6

  4. Barcola ya koma Liverpool daga PSG kan kuɗi £123m

    Liverpool ta kammala ɗaukar ɗan wasan gaba na Faransa, Bradley Barcola, daga ƙungiyar Paris St-Germain kan kuɗin da ka iya kaiwa fam miliyan 123.

    Da farko, PSG ta sanya wa dan wasan mai shekaru 23 farashin fam miliyan 145, amma Liverpool za ta biya fam miliyan 106 a matsayin na farko, tare da karin fam miliyan 17 da za a iya biya dangane da wasu sharudda na gaba.

    Barcola ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar, inda ya zama sabon dan wasa na biyar da ya koma Anfield a wannan bazara, bayan daukar dan wasan gefe Victor Munoz da masu tsaron baya Jeremy Jacquet, Ronald Araujo da Ifeanyi Ndukwe.

    "An ɗauki lokaci mai tsawo, amma ina matuƙar farin ciki a yau da na samu damar buga wa Liverpool wasa; abin da kawai nake so shi ne in kasance a filin wasa kuma in samu damar taka leda," in ji Barcola.

    "Ina fatan cimma manyan nasarori. Abu na farko shi ne lashe gasar Premier League - wannan yana ɗaya daga cikin manyan burina a rayuwa."

    Barcola ya koma PSG daga Lyon a shekarar 2023 kan kuɗin da aka bayyana cewa ya kai fam miliyan 38.5, inda ya lashe kofunan Ligue 1 guda uku da Champions League guda biyu da French Cup sau biyu, da UEFA Super Cup da kuma FIFA Intercontinental Cup.

  5. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin labaran wasannin kai-tsaye na BBC Hausa.

    Shafin da babu kamar shi wajen kawo muku muhimman abubuwa da ke faruwa a duniyar wasanni.

    Za ku iya tafka muhawara kan labaran da muke kawo muku a shafukanmu na sada zumunta: Facebook, Instagram da X.

    Haka nan za ku samu labarai da ɗumi-ɗuminsu a zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp idan kuka latsa nan.

    Ku je shafinmu na YouTube domin kallon ƙayatattun bidiyoyi na bayanai kan labaran da suka shafe ku.