Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya isa birnin New York da ke Amurka don wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da jagorantar tawagar Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
Wannan ne karo na uku da Shettima yake wakiltar Tinubu a babban taron na UNGA.
Mai bai wa mataimakin shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, a sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, ya ce abubuwan da Najeriya za ta mayar da hankali a kai yayin taron za su kasance bisa muradun ƙasar, goyon bayanta ga haɗin gwiwar ƙasashe da kiraye-kirayen da Shugaba Tinubu ke yi na sake fasalin cibiyoyin duniya don su yi daidai da yanayin tattalin arziki da yawan al'umma na wannan zamani.
"Saƙonmu a New York a bayyane yake. Najeriya ta yadda da haɗin gwiwa da ƙasashe amma dole ne masu gwamnati su zama wakilan kowa kuma masu adalci," in ji Shettima.
Maitaimakin shugaban Najeriyar ya isa New York ne tare da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara da ƙaramar ministar kasafi, Dr Doris Uzoka-Anite da sauran manyan jami'an gwamnati.
A birnin na New York kuma, Shettima ya samu tarba daga gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da ministar harkokin mata, Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim da sauran manyan jami'an gwamnati da na diflomasiyya.
A babban taron na UNGA, Shettima zai gabatar da jawabi inda zai bayyana matsayar Najeriya kan muhimman batutuwan da suka shafi duniya musamman kan zaman lafiya da kuma tsaro, ci gaba da bunƙasar tattalin arziki da kuma haɗin gwiwar ƙasashen duniya.